Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba za mu yarda a danne wa al’ummar Kamaru hakkinsu ba - Bakary
- Marubuci, Paul Njie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Garoua
- Marubuci, Wedaeli Chibelushi
- Lokacin karatu: Minti 5
Jagoran adawa na Kamaru Issa Tchiroma Bakary, wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe kansa a matsayin wanda ya lashe zaben 12 ga watan Oktoba, ya shaida wa BBC cewa ba zai amince da magudi ba a sakamakon zaben da ake shirin sanarwa ranar Litinin.
Ya ce tawagarsa ta tattara bayananta ne daga alkaluman da ta hada daga rumfunan zabe, saboda haka babu tantama game da su.
Tchiroma Bakary, mai shekara 76, tsohon minista ne wanda ya raba gari da shugaba Paul Biya, mai shekara 92 a duniya, wanda ya shafe shekara 43 a kan mulki.
Jam’iyya mai mulki ta yi watsi da ikirarin samun nasarar da Tchiroma Bakary ya yi kuma jami’an gwamnati da dama sun bayyana matakin nasa a matsayin abin da ya saba wa doka domin Majalisar Kundin Tsarin mulki ce kawai za ta iya bayyana sakamako a hukumance.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidansa a birnin Garoua, Tchiroma Bakary ya ce ya bukaci magoya bayansa su kare kuri’unsu.
“Ba za mu amince wani ya saci kuri’unsu ba,” in ji shi, yana sanye da farar babbar riga.
Tsohon ministan ya ce bai damu ba koda za a kama shi ko kuma za a daure shi, “amma na riga na sani cewa na yi nasara a zaben shugaban kasa”.
”Babu ko shakka, kuma babu tantama ko kadan. Babu wanda zai iya musanta nasarar da na samu,” in ji shi.
Tchiroma Bakary ya ce jam’iyyar CPDM mai mulki “ta ki ta amince da gaskiyar abin da ke faruwa game da zaben,” sannan ya kalubalance gwamnatin ta bayar da hujjar da za ta nuna cewa abin da yake fadawa ba gaskiya ba ne.
Ya kare matakin da ya dauka na ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya dage cewa doka “ba ta haramta mana yin hakan ba”.
A baya Tchiroma Bakary ya bayyana cewa ya lashe zaben da kashi 55% na kuri’un da aka kada, bayan ya tattara alkaluma na kashi 88% na kuri’un da aka kada.
Lokacin da aka tambaye shi ko zai amince da shan kaye idan aka ayyana cewa wani dan takara na daban ne ya yi masar ba shi ba, ya ce zai amince “matukar Majalisar Kumdin tsarin mulki ta sanar da ainahin sakamakon zabe da ala samu a rumfunan zabe ba na aringizo ba”.
Zaman dardar na ci gaba da karuwa sanadiyyar jinkirta sanar da sakamakon zaben, lamarin da ke ruruta fargabar rikicin bayan zabe a kasar wadda ke fama da rikicin ‘yan aware na yankin masu amfani da turancin Ingilishi da kuma rikicin Boko Haram a Arewa mai nisa ta kasar.
A birnin Garuoa, zaman dardar na karuwa bayan zanga-zangar da aka rika gudanarwa a makin nan. Jami’an tsari na sintiri a kan tituna cikin dare, duk da cewa sun rage zirha-zirga da rana.
Cocin Katolika ta kasar wadda ake matukar girmama ta yi kira da a kwantar da hankula bayan fargabar da ake yi kan cewa za a iya samun rikici bayan bayyana sakamakon zaben.
Bishop-Bishop na cocin na Katolika sun ce suna fatan sakamakon zaben zai yi daidai da zabi al’umma, tare da fatan cewa “babu wata hukuma da abin ya shafa da za ta sauya wani abu a yayin tattara sakamakon”.
Tchiroma Bakary wanda aka haifa a birnin Garoua, ya samu kwarewa a fannin gyare-gyaren na’ura a Faransa kafin komawa Kamaru inda ya yi aiki a kamfanin sufurin jiragen kasa.
A shekara ta 1984 aka tura su gidan yari bayan zargin shi da hannu a kitsa kifar da gwamnatin Paul Biya. Duk da cewa ya musanta zargin kuma ba a taba kama shi da laifin a kotu ba, Tchiroma Bakary ya shafe shekara shida a gidan yari.
Ya rika yin noma kamar sauran fursunoni sannan kuma ya koyi magana da harshen turancin Ingilishi.
Bayan sakin sa daga gidan yari sai Tchiroma Bakary ya shiga siyasa. A shekara ta 1992 ya zama dan majalisar dokoki a karkashin jam’iyyae adawa ta UNDP, amma sai ya shiga wani tsari na hadaka, inda ya zama ministan sufuri na tsawon shekara hudu.
Haka nan kuma ya zama ministan sadarwa daga shekara ta 2009 zuwa 2019.
A matsayinsa na ministan sadarwa kuma mai magana da yawun Shugaba Biya, Tchiroma ya kare manufofin shugaban kasar a lokacin da ake fama da matsalar Boko Haram, lokacin da aka zargi sojoji da kashe fararen hula.
To sai dai a watan Yuni,wata hudu kacal gabanin babban zaben kasar, sai Tchiroma Bakary ya sauya ra’ayi dare daya, ya ajiye mukin gwamnati tare da ayyana yin takara domin fafatawa da Paul Biya.
Ya zargi shugaban da kasancewa wanda bai san halin da ake ciki ba, inda ya ce “ba zai yiwu ba a ce kasar tana hannun mutum daya ba”.
Duk da rawar da ya taka a matsayin mai magana da yawun gwamnati, dandazon mutane sun rinka taruwa a lokuta yakin neman zabensa, lamarin da ya karfafa gwiwar masu neman kawo sauyi.
Bayan shekara sama da 40 na mulkin Biya, tattalin arzikin Kamaru ya tsaya cik, yayin da matsalolin hauhwar farashi da rashin aikin yi da rashin tsaro ke kara kamari.
Bugu da kari, mutane masu magana da turancin Ingilishi a yammacin kasar sun dade suna kokawa cewa ana danne su, haka ne ya sanya da dama daga cikin su suka goya wa Tchiroma Bakary baya a kan Biya, wanda ake yi wa kallon mai goyon bayan maus magana da turanci Faranshi, wadanda su ne ke da rinjaye.
A wani yakin neman zabe a Doula, ciniyar kasuwancin Kamaru, dubban mutane ne suka jure wa dukan ruwan sama domin sauraron jawabin Tchiroma Bakary. Yana da izza - akasin Biya, wanda ya kwashe akasarin lokacin yakin neman zaben a Turai, sai lokaci daya da ya fito
Sai dai ba kowa ne yake mararun takarar tsohon mai magana da yawun gwamnatin kasar ba. A Garuoa, birnin da ala haife shi, wasu mutanen sun shaida wa BBC cewa Bakary ba shi ne irin mutumin da suke son ganin ya yi takara ba, amma duk da haka ya zamo wani zabi na daban daga dogon lokacin da Biya ya kwashe yana mulki.
“Ba za mu iya ci gaba da jure wa wannan irin rashin ci gaba da ke kara durkusar da Kamaru ba’” in ji wani manomi Benjamin Temunga.
Tchiroma Bakary ya kuma yi ta kokarin nesanta kansa da gwamnati, inda ya nemi afuwa kan aikin da ya yi mata a matsayin mai magana da yawunta.
Misali, ya kare sojoji duk kuwa da cewa yana sane da cewa suna tafka ta’asa a rikicin yankin masu magana da harshen Ingilishi - inda yan tawaye ke yakar gwamnati na tsawon shekara shida.
”Na amince dari bisa dari cewa sojoji sun tafka laifuka,” in ji shi. “To amma a matsayin ministan yada labarai, aikina shi ne na kare mutuncin dakarun tsari. Yau kuwa ina magana ne a matsayin mutum mai yanci.”
Yana magana cikin natsuwa kuma kai-tsaye, da alama Tchiroma Bakary na kan bakarsa cewa al’umma sun amince da shi. Shi ne halastaccen shugaba, kamarbyadda ya shaida wa BBC.
“Kasar nan ta sani, kuma duniya ta sani.”