Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko gyaran matatun man Najeriya zai magance matsalar fetur a ƙasar?
Najeriya ta samu nasarar kammala gyaran matatar man fetur ta gwamnati da ke garin Fatakwal, kamar yadda kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya sanar.
Wannan nasara ta samu ne bayan kwashe shekaru matatar ba ta aiki.
Kamfanin na NNPCL ya ce matatar za ta iya tace gangar mai 60,000 a kowace rana.
Najeriya na da matatun mai guda huɗu, akwai guda biyu a Fatakwal sai ɗaya a Kaduna da kuma ɗaya a Warri, waɗanda suka daina aiki a shekarun da suka gabata, lamarin da ya tilasta wa gwamnatin ƙasar fitar da ɗanyen man ƙasar zuwa ƙetare domin tacewa.
Wannan al'amari ya yi matuƙar tasiri wajen haifar da matsalar ƙarancin man fetur da tsadarsa a ƙasar, wanda kuma ya shafi tattalin arzikin ƙasar.
Najeriya wadda ta fi kowace ƙasa arzikin albarkatun man fetur a nahiyar Afirka ta shafe shekaru tana ƙoƙarin gyara waɗannan matatu nata domin sauƙaƙa wa 'yan ƙasar da bunƙasa tattalin arzikinta.
Komawa aikin matatar ta Fatakwal na zuwa ne bayan fara aikin matatar man fetur ta Dangote mai ƙarfin tace gangar ɗanyen man fetur 650,000 a kowace rana.
A baya-bayan nan dai an riƙa samun taƙaddama tsakanin kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL da matatar ta Dangote.
To amma wane tasiri gyaran matatun man fetur ɗin zai yi ga harkar a Najeriya?
Hakan zai kawo wadatar mai a Najeriya?
Masana a fannin man fetur a Najeriya na ganin cewa har yanzu tsugune ba ta ƙare ba, domin adadin man da matatar za ta tace a kullum bai kai rabin adadin man da ake buƙata a ƙasar ba.
Farfesa Ahmad Adamu na Jami'ar Nile da ke Abuja ya ce fara aikin matatar a yanzu ba zai sa man fetur ya wadata a Najeriya ba.
''Idan ka duba matatar man ta Fatakwal, tun da ƙarama ce ta fara aiki, wadda gangan 60,000 ne kawai za ta iya tacewa a kullum, kuma ka san yanzu ba za ta iya aiki ɗari bisa ɗari ba, kenan ka ga a yanzu ba za ta samar da wannan adadi ba kenan''.
''Alal misali a yanzu a ce tana iya aiki kashi 90 cikin 100 na ƙarfinta, kenan za ta iya tace ganga 54,000 a kowace rana'', in ji shi ne.
''Idan ka duba man fetur da ake amfani da shi a Najeriya a kowace rana yana kai wa miliyan 50 zuwa 60 , to ka ga idan ka duba kwatanta da lita miliyan biyu zuwa uku da wannan matata za ta samar, sai ka ga ba zai yi wani tasiri na yawan man fetur da ake buƙata a Najeriya ba'', in ji masanin albarkatun man fetur ɗin.
Hakan zai kawo saukar farashin man?
Farfesa ahmad Adamu ya ce a yanzu a duniya ana sayar da gangar fetur kan dala 75 a kasuwar duniya, sannan kuma a yanzu da ake canja kowace dala kan naira 1,700...
''Kowace gangar mai na ɗauke da lita 159 a cikinta, kenan idan ka lissafa da wancan kuɗi kowace ganga ana sayar da ita kan naira 127,000'', in ji shi.
Masanin ya ƙara da cewa idan aka lissafa bisa wannan adadi za a tarar da cewa kowace lita guda ta ɗanyen mai ana sayar da ita kan naira 800.
''To idan ka ƙara kuɗin tacewa da kuɗin ajiya da na sufuri da ribar mai matata da ribar mai sarowa a kan ainihin kuɗin litar na naira 800, sai ka ga zuwan matatar ba zai yi wani tasiri ba wajen sauko da farashin a dai yanzu'', in ji masanin.
Ya ci gaba da cewa ita kanta matatar mai ta Fatakwal idan za ta sayi ɗanyen man da za ta tace, za ta saya ne kan farashin yadda yake a kasuwa.
''Don haka maganar zuwan matatar zai sauya farashin man fetur a Najeriya, wannan ba daidai ba ne'', in ji shi.
Masanin ya kuma ce har yanzu Najeriya za ta ci gaba da sayo mai daga ƙetare, saboda 'yan kasuwa na da tasiri, kuma za su iya zuwa duk inda suka ga dama su saro mai idan hakan zai sa su same shi da sauki fiye da na cikin gida.
Fatanmu matatar Fatakwal ta kawo sauƙi - IPMAN
Bashir Ahmad Danmallam, Shugaban dillalan man fetur da iskar gas a Najeriya ya ce zuwan matatar abin a yaba ne da suka jima suna fatan tabbatar faruwar aikin.
Ya ce akwai abubuwa da dama da zuwan matatar zai sauƙaƙa, kama da sauƙin samun man a cikin gida da kuma da samun sa da sauƙi.
Danmallam ya ce ƙungiyarsu na fatan hakan zai zama wani mataki na gyara duka matatun man fetur na ƙasar ta yadda za a samu sauƙin man a cikin ƙasar.
Shugaban na IPMAN ya ce tsadar man fetur ko sauƙinsa ya dogara ne da farashin dala, ya ce kasancewar da dala ake cinikayya to dole a ga tasiri a farashin mai idan dalar ta tashi.
Sai dai ya yi kira ga gwamnatin ƙasar da ta kawo tallafi a harkar tunda man nata ne kuma masu sayensa ('yan Najeriya) su ma 'ya'yanta ne.
Dangane da shigowa da mai kuwa ya ce babban abin da su dillalai ke la'akari da shi, shi ne ina za su samu fetur mai sauƙi, ko da kuwa a ina yake cikin duniya.
''Duk inda za a samu mai ko a Amurka ne ko Nijar ko Ingila ko Najeriya, mu dai fatanmu sauki, ina mai mai sauki yake''?
Me zai kawo sauƙin farashin mai a Najeriya?
Farfesa Adamu ya ce za a samu sauƙin farashin man fetur a Najeriya ne idan har duka matatun mai na ƙasar suka fara aiki tare da ta Dangote, da ita ma ta fara aikin tace man a wannan shekara.
''Idan har Dangote ya ƙara haɓaka aikin tace mai, sannan gwamnati ta gyra duka matatunta suka fara aiki, to hakan zai sa a samu sauƙin farashin man da kuma wadatarsa a cikin ƙasar,'' in ji shi.
Ya kuma ce idan duka matatun mai na gwamnati huɗu suka koma aiki, hakan na nufin dukkansu za su iya tace aƙalla ganga miliyan 22, shi kuwa Dangote zai iya samar da ganga miliyam 80, to ka ga idan aka haɗa za a iya samun ganga miliyan 100 ko fiye, wanda kuma hakan zai haura buƙatar Najeriya game da man fetur.
Masanin tattalin arzkin ya ce a lokacin ne Najeriya za ta iya fitar da mai zuwa ƙasashen ƙetare ta yadda za ta samu ƙarin kuɗin shiga, sannan GDP ya haɓaka.
''To a lokacin ne farashin man fetur zai ragu a Najeriya a sosai domin akwai gasa, kuma kowace matata za ta riƙa duba farashin da takwararta ta saka domin ita ma ta rage don ta samu masu saya, saboda a lokacin matatar da ta fi sayarwa da araha, ita za a fi zuwa domin saro man da take tacewa,'' in ji masanin.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ƙasar, tare da alƙawarta tabbatar da gyara matatun man fetur na ƙasar.
Lamarin da ya haifar da matsaloli masu tarin yawa da suka shafi tattalin arziki.
Inda kuɗin sufuri ya ƙaru, sannan aka samu tashin farashin kayan masarufi yayin da darajar kuɗin ƙasar ta zube, kodayake gwamnatin na iƙirarin samun farfaɗowar tattalin arzikin ƙasar a watannin baya-bayan nan.