Yadda sabbin ƙa’idojin CBN za su shafi kasuwar canjin kuɗi

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

A yunƙurinsa na daidaita darajar kuɗin Najeriya - naira, babban bankin ƙasar CBN, a 'ƴan kwanakin da suka gabata, ya gabatar da wasu sabbin ƙa'idoji ga ƴan canji domin tsaftace harkar.

Sabbin sharuɗan sun shafi abubuwan da ake buƙata kafin samun lasisi da yadda kamfanonin ƴan canji za su gudanar da harkokinsu da hana almundahana da yaƙi da ba da kuɗin tallafin ta'addanci ga masu canji.

Ƙarƙashin sabbin ƙa'idojin, CBN ta kasa rukunan masu canji gida biyu - a matakin farko, ana buƙatar sai masu canji suna da naira biliyan biyu, waɗanda ke mataki na biyu kuma za su tanadi naira miliyan ɗari biyar kafin tafiyar da harkokinsu.

A ƙarƙashin mataki na farko, masu canji za su iya buɗe rassansa a ko ina a Najeriya bisa samun amincewar CBN.

A mataki na biyu kuma, masu canji kawai za su iya buɗe ofishi ne kawai a jiha ɗaya ko kuma babban birnin tarayya Abuja.

Wannan dai cikin matakan da gwamnatin Najeriya ta ɓullo da su ne domin inganta harkokin ƴan canji a ci gaba da yunƙurin da take na kawo sauye-sauye a kasuwar musayar kuɗaɗe ta ƙasar.

A ranar Litinin ne kuma, babban bankin na CBN zai fara bai wa ƴan canjin dala kowane mako.

Sabbin ƙa'idojin na CBN sun janyo cece-kuce tsakanin al'ummar Najeriya musamman masu canji, lamarin da ake ganin yana iya janyo durƙushewar wasu.

Martanin ƴan canji kan sabbin sharuɗan

Shugaban ƙungiyar ƴan canji a Najeriya, Aminu Gwadabe ya ce sabbin sharuɗan da babban bankin ya gindaya musu abu ne da ya zo musu bagatatan sai dai a cewarsa CBN ya ce ƙa'idojin an samar da su ne domin jin ra'ayoyin masu canji kafin a zartar da shi.

A cewarsa, CBN ya buƙaci su gabatar da nasu shawarwarin wanda zai yi nazari a kansu domin a cimma abin da zai yi wa duka ɓangarorin daɗi.

Game da yunƙurin CBN na soma ba su dala a kowane mako kuwa, Gwadabe ya ce abubuwan da aka cimma a baya, ba su haifar da wani ci gaba ba inda kuma ya ce yana fatan matakin zai sauko da farashin dala da ke hauhawa.

"Abubuwa da yawa da ke kawo shi, na ɗaya tsoratarwa, dawo da shi zai yi maganin wannan kuma za a samu nasara." in ji Gwadabe.

Ya bayyana cewa ba wannan ne karon farko ba da ake haka idan an samu irin waɗannan matsaloli, "an yi a 2006 kuma mun taka rawar gani, an yi a 2009 mun taka rawar gani, an yi a 2016 har zuwa 2020, duk mun taka rawar gani."

Gwadabe ya ƙara da cewa labarin soma yunƙurin ya karyar da farashin dala da sama da naira ɗari biyu da hamsin.

Shi ma shugaban ƙungiyar ƴan canji na Zone 4 a Abuja, Abdullahi Abubakar Dauran ya ce sabbin ƙa'idojin matakai ne na gyara.

"Gyaran ƙasa ne kuma duk abin da aka ce gyaran ƙasa ne kai ɗan ƙasa ba ka da wani abu sai dai ka yi biyayya." kamar yadda ya shaida wa BBC.

Ya ce a baya, tsarin shi ne ka tanadi naira miliyan talatin da biyar a CBN "idan ya ɗauki wani lokaci toh za su dawo maka da kuɗinka tun da ka riga ka wuce ƙa'ida, daman sun ba ka lasisi."

"Matsalar da ke faruwa a baya, CBN su suke ba mu dala, sai ka sayar a kasuwa, cewa ka sayar wa matafiya da ƴan makaranta da masu tafiya saboda ganin likita." in ji shi.

Ya ce daga baya an samu ƙalubale inda CBN ya soke tsarin.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar ƴan canji ta ƙasa ya bayyana cewa daina ba su dala bai yi wani tasiri ba saboda daga 2021 da aka daina ba su, wanda a lokacin farashin dala naira 450 zuwa 500 ne, hakan bai hana dalar tashi ba har zuwa naira 1,900 a kwanakin baya.

A cewarsa, cikin sharuɗan da aka gindaya musu shi ne "duk wanda aka samu da karya doka, za a soke lasisinsa."

"Idan ka siya ba ka sayar ba, to kar ka sake saye sannan sun kawo manhaja da ke bibiyar bayanan wanda za ka sayarwa kaya." in ji shi.

Ya ce "an sa tsare-tsare da za a tabbatar da cewa abubuwan da ke kawo mishkila, an rage su ko an kawar da su gaba ɗaya."

Gwadabe ya ce za su sa ido domin tabbatar da cewa an ɗauki mataki kan duk wani ɗan canji da ke son kawo cikas domin cimma buƙatun gwamnati.

Yadda tsarin kasuwar canji take a wasu ƙasashen

A cewar Aminu Gwadabe, binciken da suka yi ya nuna cewa tsarin da CBN ta bijiro da shi ya sha banban da wasu ƙasashen duniya.

Ya ba da misali da ƙasar Indiya inda ake neman masu canji su tanadi jarin dala dubu sittin da bakwai sai Kenya da yake dala dubu hamsin yayin da a Tanzaniya ake neman jarin dala dubu ɗari biyu.

"Idan ka haɗa su duka, babu wanda ya kai miliyan ɗari da hamsin, idan aka ce mana biliyan biyu, kamar ana so a kore mu ne, ko abin da ake gudu, ya faru a gaba." kamar yadda ya ce.

Ƙarin bayani kan sabbin ƙa'idojin

Baya ga tanadar jarin soma hada-hadar canjin kuɗaɗen waje, takardar da ke ƙunshe da sabbin sharudɗan da CBN ya bijiro da su ta nuna cewa

  • CBN ya umarci masu canji su biya kashi 25 cikin 100 na kuɗaɗen canjin da aka saya domin tafiye-tafiyen kasuwanci ko tafiya ta ƙashin kai a tasabar kuɗi inda za a tura ragowar kashi 75 cikin 100 zuwa asusun kwastoma na ajiyar kuɗaɗen waje.
  • CBN ya ce kwastamomi masu karɓar dala ɗari biyar ko ƙasa da haka, za a biya su lakadan.
  • Masu canji a ƙarƙashin rukuni na farko za su tafiyar da harkokinsu a matakin ƙasa - za su iya buɗe rassa su kuma samu masu hannun jari bisa amincewar CBN.
  • Ƴan canji da ke rukuni na biyu kuma suna da damar bude ofishi ne kawai a jiha ɗaya ko Abuja. Yana iya zama wurare uku - babban ofishi da rassa biyu, shi ma bisa sahhalewar CBN.