Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
NLC na shan suka saboda ɗage zanga-zangar tsadar rayuwa
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, NLC ta sanar da ɗage zanga-zangar matsin rayuwa a ranar Laraba, rana ta biyu ta gangamin da ta shirya a faɗin ƙasar domin nuna takaici da rashin jin daɗi kan halin matsi da al'umma suka shiga tun bayan da gwamnati ta janye tallafin man fetur.
A ranar Talata - ranar farko ta zanga-zangar, ɗaruruwan masu zanga-zanga sun fantsama kan titunan biranen ƙasar domin amsa kiran NLC.
NLC dai ta kare matakinta na ɗage zanga-zangar a rana ta biyun inda ta ce ta yi haka ne domin bai wa gwamnati nan da 13 ga watan Maris ta yi wani abu na sauƙaƙa wa al'umma.
Ɗage zanga-zangar dai ya janyo cece-kuce a tsakanin al'ummar ƙasar da wasu ke ganin za a rina saboda zargin da suke cewa ƙungiyar ba da gaske take ba a iƙirarinta na yi wa talaka fafutuka.
Dama a baya wasu al'ummar Najeriya sun zargi NLC da fakewa da yi wa al'ummar ƙasa hidima domin biyan buƙatunta na ƙashin kai.
Mun leƙa shafukan sada zumunta domin zaƙulo wasu ra'ayoyin al'ummar Najeriya game da matakin NLC na janye zanga-zangar.
Wani mai amfani da shafin X, Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya rubuta a shafinnasa cewa "akwai haɗari nuna yarda ga NLC."
Kwamared Deji Adeyanju, shugaban ƙungiyar Concerned Nigerians ya wallafa ra'ayinsa a shafinsa na X game da ɗage zanga-zangar inda ya ce babu abin da aka cimma a zanga-zangar da aka yi a ranar farko, ga shi kuma NLC ta janye zanga-zangar.
A saƙon nasa ya sanar da NLC cewa yana fatan tana ganin abin da ya sa mutane ba sa ganin ƙimarta a Najeriya.
FS Yusuf kuwa cewa ya yi lokaci na zuwa da mutane ba za su jira NLC ba inda ya ce abu ne na sannu a hankali.
Shi kuwa Adebayo Raphael cewa ya yi, "abin takaici ne cewa NLC wani ɓangare ne na lalacewar Najeriya saboda shugabancinta cike yake da masu neman dama ta amfana daga rashin kyautatuwar yanayin aikin ma'aikata a Najeriya."
Chlorpheniramine, wani ma'abocin shafin X ne inda shi ma game da matakin na NLC ya ce "kada a yaudari ƴan Najeriya. Duk wata zanga-zanga da NLC ta shirya, gwamnati ce ta ɗauki nauyinta. Dama mutane sun san haka za ta faru, kwanaki kafin zanga-zangar, suka soke ta. Shirin shi ne lokaci ya yi ta tafiya sannan a rikita tunanin masu zanga-zangar da gaske. Irin haka ta faru a Ibadan."
Abin da ya sa muka janye zanga-zangar - NLC
Mataimakin shugaban ƙungiyar ta NLC na Najeriya, Kwamared Audu Titus Amba ya ce sun ɗage zanga-zangar ne ganin yadda hukumomi suka ji kokensu a faɗin ƙasar.
Ya ce dalilin zanga-zangar shi ne isar wa gwamnati damuwar al'umma kuma "mun ba da wasiƙunmu, an amshe mu hannu bibiyu kuma an tabbatar mana duk koke-kokenmu da muka nuna musu, za su tabbatar cewa za su kai ga shugaban ƙasa kuma za a ɗauki mataki."
A cewarsa, suna son su bai wa gwamnati dama don ta yi wani a tsukin wa'adin da suka ɗibar mata.
Kwamared Titus ya ce ƙungiyar ƙwadago tana aiki ne ga al'ummar Najeriya ba wai kawai ma'aikata ba.
Ya ce idan har bayan wa'adin na ranar 13 ga watan Maris gwamnati ba ta yi wani abu ba, a ƙungiyance za su sake zama.
Ya bayyana cewa babu dalilin fita yin zanga-zanga sau biyu "bayan abin da muke so mu yi ɗin mun yi shi [ranar Talata]."
Game da zargin cewa ba don jama'a suke ba, Kwamared Titus ya ce dama ba jama'a ne suka ce su fita ba, sun zauna a ƙungiyance ne inda suka yanke shawarar yin zanga-zangar.
"Mu muka ce kwana biyu ne, yanzu kuma mun ce wanda muka yi ya isa." in ji shi.