Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2023: Golan da koci Jose Peseiro ke karewa daga masu suka
Kocin Super Eagles, Jose Peseiro ya bayyana goyon bayansa ga Francis Uzoho, golan da ke shan suka daga magoya baya, inda ya ce "kowanne ɗan wasa ma yana kuskure".
Kwazon Uzoho, ya kasance babban abin tattaunawa bayan wasan sada zumunta da 'yan Najeriya suka yi a baya-bayan nan da ƙasashen Saudiyya da kuma Mozambique.
Mai tsaron ragar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Omonia Nicosia ɗan shekara 24, ya yi ta tafka kura-kurai. Kuskurensa da ya fi fitowa fili shi ne na karawa da Saudiyya, inda ya yi bahagon lissafi ya yi tsalle, ya tunkuɗa ƙwallo a ragarsa.
"A Najeriya, ko yaushe suna sukar masu tsaron raga ne," Peseiro ya faɗa wa BBC Sport Africa.
"Me ya sa ba za su soki 'yan wasan gaba da suka riƙa ɓaras da ƙwallaye ba? Ai duk abu ɗaya ne."
Golan na Omonia Nicosia kuma mai goyon bayan ƙungiyar Man United, tun daga yarinta, tauraronsa ya haska lokacin da ya kama ƙwallo a Old Trafford
Uzoho har yanzu bai buga wasa ko sau ɗaya ga ƙungiyarsa ta ƙasar Cyprus a wannan kaka ba. Yayin da ƙwazonsa ya ƙasa kuma ƙwarin gwiwarsa ya yi matuƙar raguwa, wani gagarumin sashe na magoya baya na alla-alla a cire shi daga jerin 'yan wasan da ke fara bugawa.
Sai dai, Peseiro yana kare mai tsaron ragar, wanda ya yi bayyanarsa ta farko a wasan ƙasashe, yana ɗan shekara 19.
"Idan na ce zan canza ɗan wasa ko yaushe, ko kuma hukunta shi, idan ya yi kuskure, wata rana ba zan samu ɗan wasa ko ɗaya ba, saboda ɗan ƙwallo yana yin kuskure, " in ji shi.
"Mun fahimta, kuma mun amince cewa magoya baya na da 'yancin su yi ihu ko kuma su yi magana. Wannan an saba da shi.
"Ni da Uzoho da sauran 'yan wasan duk mun yarda da haka. Wajibi ne, kuma nauyi ne da ya rataya a wuyana, na samu ƙwarin gwiwa kuma na goyi bayan 'yan wasanmu."
Wanda ya fara kama ƙwallo a Gasar Kofin Duniya ta 2018 a Rasha, Uzoho ya kasance golan yau da gobe tun da Peseiro ya karɓi ragamar kocin Najeriya a watan Mayun 2022.
Dan ƙasar Portugal ɗin ya ƙara adadin masu tsaron raga uku a cikin rukunin 'yan wasansa a baya-bayan nan, sai dai ya bijire wa matsin lamba a kan ya ajiye Uzoho bayan canjaras 2-2 da Saudiyya, inda ya ƙara sanya shi cikakken wasa tsawon minti 90 a karawa da Mozambique.
"Matsalata kawai guda ɗaya ce kuma ita ce idan Uzoho ya kasa jurewa (sukar da ake yi masa)," ya ƙara da cewa.
"Suka abu ne mai kyau har a wajenmu - wasu lokutan takan bude idanuwanmu. Sai dai na sani cewa, a Najeriya, mutane sun fi son su soki mai tsaron raga.
"A wajena, Uzoho har yanzu kuskure ɗaya kawai ya yi."
Burin zuwa Gasar cin Kofin Duniya
Wasaninin sada zumuntar na watan Oktoba, wani shiri ne na tunkarar karawar samun cancantar zuwa Gasar Kofin Duniya a 2026, da za a fara a watan Nuwamba.
Najeriya za ta fara wasanninta da karawa tsakanin Lesotho a gida, sannan ta je ta haɗu da Zimbabwe.
Peseiro, wanda a tsawon shekarunsa na koci ya horas da ƙasashen Saudiyya da Venezuela, yana fatan jagorantar Super Eagles zuwa Gasar cin Kofin Duniya a Amurka ta Arewa.
Kuma ya yi shelar cewa yana alfahari da ci gaban da suka samu zuwa yanzu.
"Muna da buri guda biyu a wannan mataki," ya bayyana. "Abu na farko shi ne mu samar da wani ƙwaƙƙwaran yanayi. Na biyu kuma shi ne mu shirya tunkarar Lesotho da Zimbabwe.
"Mun yi nagartaccen wasa da Saudiyya, inda muka nuna kyawun inganci.
"Wasanmu da Mozambique, na so takun da muka yi a rabin lokaci. Bayan dawowa rabin lokacin ƙarshe ne abubuwa suka fita daga raina. 'Yan wasan sun yi sakaci, ba su ƙara gudunsu ba, kuma sun riƙa bai wa abokan hamayya damar mayar da kora.
"Zan so mu ƙara shiryawa, na buga wasa ɗaya ko biyu a cikin makon gobe, sai dai ba abu ne mai yiwuwa ba.
"Lokacin na sa hannu kan kwanturagi, burina shi ne na kai Najeriya Gasar cin Kofin Duniya, sannan na mayar da su zakarun Afirka.
"Jazaman ne sai kun ci Lesotho da Zimbabwe, amma ba abu ne da za ku ɗauka mai sauƙi ba.
"A baya, abu ne mai yiwuwa ka gane babban bambanci tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa, amma yanzu abin ba haka yake ba. Kulob-kulob suna matuƙar kai ruwa da rana da juna. "
Duk da haka, Najeriya tana sa ran samun maki mafi yawa daga wasannin guda biyu, ko ma wane ne ya fara cin kwallo.
Dan wasa Adebayo Adeleye, mai buga ƙwallo a Isra'ila ya taka leda a nasarar muka samu ta ci 3-2 a kan Saliyo ta samun cancantar Gasar cin Kofin Afirka a watan Yuni.
Yana cikin rukunin 'yan wasan da suka buga a karawarmu da Saudiyya da Mozambique, amma bai samu damar fito da kansa sosai ba.
Maduka Okoye, sahun farko a Gasar Kofin Afirka ta 2021 a Kamaru, ya fuskanci kakkausan sakamako bayan gasar, kuma tun daga nan bai sake yin kataɓus ba sama da wata 18 kenan.
Wasu na yi wa golan Chippa United Stanley Nwabali laƙabi da sabon zaɓi da ake da shi.
Sai dai, Peseiro na iya shiga ƙarin damuwa game da ƙoshin lafiyar Victor Osimhen da Samuel Chukwueze.
Duka 'yan wasan gaban sun ji ciwo a gwiwa yayin karawa da Saudiyya, abin da mai yiwuwa zai sa ba za su buga wasannin samun cancantar zuwa Gasar cin Kofin Duniyar na watan gobe ba.
"Muna son duk zaƙaƙuran 'yan wasanmu su kasance cikin ƙoshin lafiya kuma su samu damar buga wasa," in ji Peseiro.
"Ina kuma jin kulob ɗin namu ya ƙara samun inganci. Na san 'yan wasana sosai kuma muna da mutum biyu ko uku da ke buga matsayi ɗaya da nagarta kusan iri ɗaya."
Abokan karawa 'masu hatsari' a Afcon
Damar Peseiro ta jagorantar Najeriya zuwa Gasar cin Kofin Duniya, ga alama za ta dogara ne a kan ƙwazonsa a Gasar cin Kofin Afirka (Afcon) na shekara mai zuwa a Ivory Coast.
Kwanturagin kocin ɗan shekara 63 zai ƙare ne bayan gasar ta Afirka.
Mutane da yawa sun yi imani cewa ciyo wa Najeriya kofin nahiyar na huɗu ne kawai zai sanya shi, ci gaba da aiki har bayan watan Fabrairu, lamarin da ya sa ci gaba da goyon bayan fafutukar Uzoho ke ƙara zama mai wuyar fahimta.
Peseiro ya amince da rage albashin da ake biyansa don ci gaba da aiki da Najeriya.
Rabon rukunonin gasar ta cin kofin Afirka ta haɗa ƙungiyar Super Eagles a rukuni na 1 da mai masaukin baƙi da kuma Equatorial Guinea da Guinea-Bissau, wadda ta ɗimauta yaran Peseiro a wasan samun cancanta da ci 1-0 a Abuja.
"Idan kana so ya lashe gasar Afcon akwai buƙatar ka yarda da rabon rukunin," cewar Peseiro. "Abokan karawarmu su ma suna kyau da kuma hatsari.
"Mun fi Guinea-Bissau ƙwazo, amma ka tuna cewa sun cinye mu har gida, don haka sai mun shirya tunkarar kowacce ƙungiya da tunani da hali iri ɗaya."