Rabiot da Juventus sun yi hannun riga

Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus ta tabbatar da cewa ɗan wasan tsakiyar ƙasar Faransa Adrien Rabiot ya bar ƙungiyar a kakar wasa ta bana bayan kwantiraginsa ya ƙare.

Tsohon ɗan wasan Paris St-German mai shekaru 29, ya shafe kaka biyar a kulob ɗin na Turin, inda ya lashe Kofin Italiya biyu da kuma Super Cup na Italiya ɗaya.

"Adrien Rabiot da Juventus sun rabu," in ji ƙungiyar a cikin wata sanarwa a shafinta na Intanet.

Sanarwar ta ci gaba da cewa "Za a tuna da shi a matsayin ɗan wasan da ya ke bayar da duk abin da ya dace don kare mutuncin wannan ƙungiyar, kuma wanda ya gudanar da al'amuransa cikin aminci da kwarjinin da ba za a iya musantawa ba."

Rabiot dai ya buga wa ƙungiyar wasanni 212, daidai da takwaransa na Faransa Zinedine Zidane. Michel Platini (224) da David Trezeguet (320) ne kawai ƴan wasan Faransa da suka fi shi yawan buga wasanni a Juventus.

Yanzu ya zama ɗan wasa mai zaman kansa, inda ya ke da ƴancin rattaba hannu kan yarjejeniya da kowace ƙungiya ya ke buƙata