Tsohon kwamandan dakarun wanzar da zaman lafiya da ya kifar da gwamnati

Tchiani

Asalin hoton, ORTN

Bayanan hoto, Janar Tchiani ya yi wa ƴan ƙasar jawabi a gidan talbijin a ranar 28 ga watan Yuli

Janar Abdourahmane Tchiani wanda ya taɓa shiga aikin wanzar da zaman lafiya a ƙasashe da yaƙi ya ɗaiɗaita, a yanzu ya haddasa wata gagarumar rikici a Yammacin Afrika ta hanyar kifar da gwamnati a Nijar.

Janar ɗin wanda ba sananne bane a wajen mahaifarsa, ya kasance kwamandan dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa kafin ya taso ya hamɓarar da mutumin da aka ɗora masa alhakin tsarewa, Shugaba Mohamed Bazoum.

Janar Tchiani ya ayyana kansa Shugaban Kungiyar Ceton Ƙasar, wanda suka kasance shugabanni da aka kafa bayan kwace iko a ranar 26 ga watan Yuli.

A ɗaya gefen kuwa, tsohon maigidansa na can yana tsare a gida. Mista Bazoum ya kasance yana tattaunawa da shugabannin kasashen waje tun bayan faruwar lamarin, sai dai yana cikin kaɗaici.

Zuwa yanzu, janar Tchiani ya yi watsi da dukkan buƙata ta mayar da mulki ga Bazoum. Ya ki ganawa da yawancin jakadu daga ƙasashen duniya, amma ya gana da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma tsohon Sarkin Kano na 14 Muhammad Sanusi a ranar Laraba.

Mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amuka Victoria Nuland da ta kai ziyara Nijar a ranar Litinin, ta ƙasa ganin janar din mai shekara 62.

Haka ma, wata tawaga daga kungiyar Ecowas ta ƙasa ganin shugaban mulkin sojin ƙasar, inda suka tsaya a filin jirgin sama an Yamai.

An ɗage wani shirin ganawa da kungiyar Ecowas da kungiyar Haɗin Kan Afrika da kuma jkadun Majalisar Dinkin Duniya suka shirya yi a ranar Laraba, bayan da sojojin suka ce yanzu ba lokaci ba ne na ganawa da su.

Janar Tchiani na ci gaba da nuna kansa a matsayin mai taurin kai da kuma ba shi da fara'a ga mutane.

Ba ya cikin wani gangami da sojojin suka shirya a Yamai, babban birnin ƙasar a ranar Lahadi. Ya bayyana a gaban talabijin ɗin ƙasar har sau uku tun bayan kifar da gwamnati, kuma ya yi magana sau biyu - na farko lokacin da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban ƙasar da kuma jawabin da ya yi a ranar bikin samun ƴancin ƙasar.

Ya yi jawabin ne duk da cewa a ɗaya ɓangare ba shi da matsaniyar inda rikicin zai karkata nan gaba.

Shin Ecowas za ta kaddamar da farmakin soja ne a kan Nijar, kamar yadda tayi barazanar yi, ganin cewa ɗaya daga cikin ginshikan kungiyar shi ne tabbatar da kyakkyawar shugabanci da kuma dimokuraɗiyya?

Ko kuma kungiyarza ta jira ta ga yadda takunkumai da ta kakabawa Nijar ɗin za su shafeta ta hanyar matsa lamba ga sojojin, musamman ma ganin cewa mutane da dama a Najeriya da wasu ƙasashen Ecowas sun nuna adawa da batun ɗaukar matakin soja.

.

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban kungiyar, wanda kuma shi ne Shugaba Bola Tinubu na Najeriya, ya ƙara nanata buƙatarsa ta son ganin an bi hanyar diflomasiyya da kuma shawarar da shi da takwarorinsa za su yanke bayan taron da ake gudanarwa a Abuja ranar Alhamis.

Duba da rashin tabbas da ake ciki, da kuma bayan samun ƙwarin gwiwar makwaɓtansa na Mali da Burkina Faso da kuma Guinea waɗanda suka hamɓarar da gwamnatocinsu, alamu na nuna cewa Janar Tchiani ya shirya yin wasan jan kafa.

Gwamnatinsa ta sanar da naɗa tsohon ministan kuɗi kuma jami'in Bankin Ci Gaban Afrika Ali Mahaman Lamine Zeini - a matsayin firaminista - abin da ke alamta cewa sojojin sun shirya daɗewa kafin miƙa mulki.

Wasu masana na nuna shakkun cewa ko hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum wanda ya fito daga kabilar Larabawa da ba ta rinjaye, zai iya tayar da rikicin kabilanci a ƙasar.

Sai dai, wata alaƙa ta musayar al'adu mai ƙarfi da jin kasancewar mutum ɗan ƙasa a ko yaushe sun zama wani ginshiƙi da ya tallafi Nijar ɗin zamani

Wani tsohon jagoran 'yan tawaye kuma ɗan siyasa a Nijar ya ce ya kafa wata ƙungiya a ƙoƙarin mayar da hamɓararren Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki.

Rhissa Ag Boula ya ce ƙungiyar tasa mai suna Majalisar Nuna Bijirewa don Tabbatar da Jamhuriya (Conseil de la Résistance Pour la République) za ta tallafa wa ƙoƙarin dawo da gwamnati mai aiki da tsarin mulki a Nijar.

Sai dai Janar Tchiani ya ɗauki babbar kasada. Ana ganin matakin da ya ɗauka na na tsare Mista Bazoum da kuma kifar da gwamnati shi kaɗai kasada ce mai hatsari. Da a ce bai samu nasara ba, to da a yanzu yana can a gidan yari a tsare.

Har ila yau, matakin da ya ɗauka na yanke daɗaɗɗiyar alaƙa ta ɓangaren tsaro da Faransa wadda ta yi wa Nijar ɗin mulkin mallaka abu ne da ba a san mai zai haifar ba.

Komawa neman taimako daga sojojin hayan Rasha na Wagner da Nijar ɗin ke yi a yanzu na ƙara nuna bijirewa umarnin Ecowas da kuma na gwamnatocin yamma, ko da in tafiya ta ɗaure da cincirindon masu adawa da Bazoum ta ɗore a Yamai.

A tsawon shekaru 40 da ya ɗauka yana aikin soji, Janar Tchiani ya samu horo a ƙasashen Senegal, Faransa, Moroko, Mali da kuma Amurka.

Ya kuma yi aiki a:

  • Ya yi aiki a matsayin jami'in wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Ivory Coast da yankin Darfur na Sudan da kuma Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
  • Ya shiga cikin tawagar Ecowas da aka tura Ivory Coast
  • Ya kuma yi aiki cikin dakarun haɗin gwiwa na ƙasashen waje, inda dakaru daga Nijar, Chadi, Najeriya da kuma Kamaru suka haɗa kai wajen yaki da ƴan kungiyar Boko Haram.

A yanzu dai alamu na nuna cewa yana barazanar yin fito-na-fito ta fuskar soji da Ecowas ta hanyar kin martaba wa'adin da ta bayar na mayar da mulkin ga hannun Bazoum.

Janar Tchiani ya kum jagoranci rundunoni daban-daban a Nijar, duk da cewa ba wanda ke yaki da masu iƙirarin jihadi ba. Amma yanzu yana ƙoƙarin sanya Nijar da makwaɓtanta Mali da Burkina Faso da kuma Benin da ke tsakiyar Sahel cikin gagarumar rikici.

Sai dai abubuwa biyu ne aka fi tuna wa da su game da shi a tsawon rayuwarsa ta aikin soji.

Kafin kara masa matsayi zuwa mai jagorantar dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa a 2011, bai taɓa riƙe wani babban muƙami ba a ciki da wajen ƙasar wanda ke buƙatar aiki da shugabannin gwamnati da masu haɗin gwiwa na ƙasashen waje.

Janar Tchiani mai shekra 62 ya kasance babban jami'in soja da ake ɗora wa alhakin gudanar da wasu ayyuka na musamman maimakon jagorantar ɓangaren tsaro.

Ko da bayan naɗa shi shugaban dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa da tsohon shugaban ƙasar Nijar Mahamadou Issoufou ya yi, bai cika fitowa ya yi magana ba kan abubuwan da ke faruwa.

Ba ya cikin tattaunawar jin ra'ayin jama'a da aka yi na hanyar da za a bi wajen daƙile ayyukan masu iƙirarin jihadi da kuma rikice-rikice tsakanin al'umma da ke yi wa mutane barazana a tsawon shekaru.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawancin magoya bayan sojojin sun nuna goyon baya ga Rasha da kuma adawa da Faransa

Kasancewarsa wanda aka aminta da shi amma ba a saba ji daga garesa ba, an bayyana cewa yana abubuwansa cikin sirri, inda wasu lokuta ko shugabannin da yake bai wa tsaro, su ma ba su san abubuwa game da shi ba.

Dangantakarsa da shugaba Bazoum, wanda yake da daɗaɗɗiyar alaƙa Mista Issoufou, ta fara tsami kafin jijita ta fito cewa shugaban yana ƙoƙarin ƙorarsa.

Yi masa ritaya daga kan muƙaminsa, ko da yake shekarunsa sun kai, da ya kasance zai iya zama abu mafi ciwo garesa, kasancewarsa mutumin da a tsawon shekarunsa kusan 40 na aikin soja ya taka matakin girma daban-daban.

Janar Tchiani ya fito ne daga kabilar Hausawa da ke da rinjaye, daga yankin Tillabéri, wanda ya kasance wurin da ake ɗaukar sojoji.

Mista Bazoum ya fito ne daga gidan talakawa, inda ya fara yin karatunsa sannu a hankali daga matakin sakandari har zuwa jami'a. Ya taɓa zama malamin makaranta da kuma shiga harkar kasuwanci, kafin ya zarce zuwa siyasa a farkon shekarun 1990.

Sai dai Janar Tchiani bai taɓa yin kyakkyawar mu'amala da Shugaba Bazoum ba - inda ya fi aiki kut-da-kut da tsohon shugaban ƙasar Issoufou.

Bayan shafe tsawon shakaru ba tare da idon jama'a ya kai kansa ba, yanzu Janar Tchiani ya samu kansa a cikin rikicin siyasa da kuma hulɗar diflomsiyya.

Zuwa yanzu dai ya ci gaba da dogara da abin da ya fi amincewa da shi a tsawon shekaru na aikinsa na soja, wanda ya kunshi: turjiya, furta abin da yake cikin ransa a gaban mutane, da kuma kin miƙa wuyaa.

Sai dai Janar Tchiani da gwamnatin mulkin sojan sun yi wayo sun tayar da batun ƙin jinin Faransa a tsakanin ƴan Nijar da dama kuma za su yi ƙoƙarin mayar da wannan ya zama babban tushe na goyon baya da kuma abu da zai yi fito-na-fito da Ecowas.