Abu biyar da muka sani game da sabon shugaban mulkin sojan Nijar

Abu biyar da muka sani game da sabon shugaban mulkin sojan Nijar

Janar Abdourahmane Tchiani ya shelanta kansa a matsayin sabon shugaban ƙasa a Nijar bayan wani juyin mulki bagatatan.

Mutumin wanda kuma ake kira da Omar Tchiani, shi ne ya shirya ƙwace mulkin da aka fara ranar Laraba, lokacin da dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa da yake jagoranta suka kama shugaban Nijar.

Hamɓararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum shi ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar na farko da ya gani wani zaɓaɓɓen shugaba tun bayan samun 'yancin kai a 1960.

Niger Coup

Asalin hoton, AFP