'Mata da 'yan mata na bukatar kariya lokacin zabe'

A duk lokacin da ka ce zabe ya gabato a Najeriya, mata da 'yan mata (wadanda shekarunsu sun kai 18) da tsofaffi kan zaku domin ganin lokacin ya yi da za su fita runfunann zabe domin kada kuri'arsu.

Ko a runfunan zabe, akasari mata sun fi maza yawa, sai dai ana nuna damuwa kan yadda matan ba za samun kariyar da ta dace domin zabar shugaban da ya kwanta musu a rai da sukai amanna zai cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

Kan haka, kungiyar Plan International mai rajin kare hakkin yara da 'yan mata da kuma mata, ta koka kan yadda aka rika kai hari kan masu kada kuri'a a lokacin zaben shugaban kasa da wasu 'yan majalisu a ranar 25 ga watan Junairun 2023.

Plan International, wadda ta sa ido kan yadda aka gudanar da zaben, ta ce idan ba a dauki mataki ba, nan gaba mata da 'yan mata ba za su fito kada kuri'a ba.

Daya daga cikin jami'an kungiyar mai suna Lisa Nanbam Daspan,ta shaidawa BBC cewa ya na da matukar muhimmanci a dauki matakin bai wa mata kariyar da ta dace domin su samu zarafin kada kuri'a kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba su iko.

Ta ce sun lura kashi 40 cikin 100 na mutanen Najeriya da suka kada kuri'a mata da 'yan mata ne, sannan mata kashi 47 ne sukai rijista a zaben da aka yi.

''Abin damuwar shi ne a zaben shugaban kasa da aka yi a makon da ya wuce, an kai wa mata hari ciki har da wadda aka sokawa wuka a ciki amma duk da haka ba ta hakura ba sai da ta sake dawowa rumfar zabe ta kada kuri'a bayan ta je asibiti an bata taimakon gaggawa,'' in ji Lisa.

Ta kara da cewa akwai wata mace a jihar Edo da aka harba kuma ta mutu a lokacin zaben, dan haka dole lamarin ya dagawa kungiyar Plan International,

Dan haka suke bukatar gwamnati da hukumar zabe INEC su dauki matakin bai wa mata da 'uyan mata kariyar da ta dace a lokacin zabuka, musamman sauran zaben da ya rage ba a yi ba na gwamnoni da 'yan majalisar wakilai na jihohi.

Lisa ta kara da cewa ''Mu na kira da babbar murya, gwamnati da masu ruwa da tsaki su tabbatar da bai wa mata kariya. Matar da aka ji wa cio gwamnati ta tallafa mata, da wadda aka kashe a jihar Edo, ana bukatar bai wa 'yan uwanta diyya da tabbatar da hakan ba ta sake faruwa ba.''

Batun kai wa mutane hari a lokacin zabe na daga cikin batutuwan da masu sharhi kan lamarin siyasa ke ganin ya na sanyayawa mutane gwiwa musamman mata wajen fita domin kada kuri'a a wani banare na 'yancinsu da kundin tsarin mulki ya ba su a matsayin 'yan Najeriya.