Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona na zawarcin Harry Kane, Madrid za ta dauki Gravenberch
Barcelona na zawarcin kyaftin din Ingila Harry Kane, mai shekara 32, wanda ya zura kwallaye 95 a wasanni 102 da ya buga wa Bayern Munich a gasar lig da kofin duniya. Ana kallon Kane a matsayin wanda ya dace ya maye gurbin dan wasan gaban Barca dan kasar Poland Robert Lewandowski mai shekaru 37. (El Nacional)
Za a bai wa kocin Manchester United Ruben Amorim kudi don neman dan wasan Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, mai shekara 22, a watan Janairu. (Teamtalk),
Chelsea, Manchester United da Newcastle United duk suna zawarcin dan wasan tsakiya na Real Madrid da Faransa Eduardo Camavinga, mai shekara 22, wanda farashinsa ya kai Yuro miliyan 80 (£69.7m). (CaughtOffside)
Real Marid na zawarcin dan wasan Liverpool da Netherlands Ryan Gravenberch, mai shekara 23, wanda aka kiyasta darajarsa kan Yuro miliyan 75 (£65.3m). (Fichajes)
Arsenal na da kwarin gwiwar cewa dan wasan bayan Faransa William Saliba, mai shekara 24, zai rattaba hannu kan wani sabon kwantiragi na dogon lokaci duk da nemansa da Real Madrid ke yi. (Football Insider)
Jami'an West Ham sun alamta cewa kocin nan dan kasar Portugal Nuno Espirito Santo, mai shekaru 51, wanda Nottingham Forest ta kora a farkon wannan watan, a matsayin wanda zai maye gurbin Graham Potter sakamakon fara kakar wasa ta bana. (Talksport)
Hammers din ba za ta tuntubi tsohon dan wasanta Frank Lampard, mai shekara 47, wanda yanzu yake kocin Coventry City game da aikin ba. (Football Insider)
Manchester United na fatan dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, ya ci gaba da haskakawa a Barcelona, wacce ke da zabin siyan dan wasan da yake aro a kan fan miliyan 26. (Teamtalk)
Tsohon kocin Liverpool Rafael Benitez, mai shekara 65, ya ce yana son ya sake yin koci a Ingila. (Telegraph)