Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yanbindiga sun sace mata da yara 'sama da 50' a jihar Zamfara
Da yawan mazauna ƙauyen Gidan Maidanko a yankin ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun tsere daga gidajensu bayan wasu mahara sun auka tare da sace sama da mutum 50 a garin.
Bayanai sun nuna cewa maharan ɗauke da muggan makamai sun shiga garin ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:00 na dare.
Wasu mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa maharan sun sace aƙalla mutum 50 zuwa 55, waɗanda mafi yawansu mata ne da ƙananan yara.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton masu garkuwar ba su tuntuɓe su ba, a cewarsu. Sai dai ba su bayyana ko an samu asarar rayuka ba a ɓangaren maharan ko kuma jama'ar garin.
Zuwa yanzu hukumomi ba su ce komai ba game da lamarin. Kakakin rundunar 'yansanda a Zamfara, Yazid Abubakar, ya ce yana kan wani aiki, yayin da Kwamashinan 'Yansanda Muhammed Shehu Dalijan bai dawo da kiran waya da aka yi masa ba.
Garin na Gidan Maidanko na da nisan kilomita kusan 92 daga Gusau babban birnin jihar ta Zamfara da ke arewa maso yammcin Najeriya.
'Fafatawar awa biyu babu jami'n tsaro'
Ƙauyuka da dama a faɗin jihar ta Zamfara sun daɗe suna fama da hare-haren 'yanbindiga da ke sace mutane ko hana su noma domin neman kuɗin fansa, a wasu lokutan ba tare da wani ƙalubale ba daga jami'an tsaro.
A wannan karon, mazauna yankin sun shafe kusan awa biyu suna gwabzawa da mazauna yankin kafin su ci ƙarfinsu, kamar yadda wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC.
"An shafe awa biyu ana ɗauki ba daɗi da mutanen nan amma babu wasu jami'an tsaro da suka kawo mana tallafi," in ji shi. "Mutanen gari ne kawai suka tashi tsaye domin su kare kan su."
Ya ƙara da cewa yanzu haka mutanen garin nasu na cikin fargaba da zulumi.
"Muna cikin halin tsoro da fargaba. Wasu ma suna ta guduwa garuruwan da ke kusa, amma matsalar ita ce wurin da suke guduwar ma babu wani tsaro, kawai dai saboda mutanen garin sun fi namu yawa shi ya sa ake taruwa a jajanta wa juna."
Shi ma wani mazaunin yankin ya ce maharan sun yi ta kai wa mutane hari har zuwa 12:00 na dare, yana mai cewa akwai gidan da aka ɗauki kusan mata 20.
"Har zuwa 12:00 na dare ana faɗa da su amma wabu wani tallafi daga jami'an tsaro, kuma mun yi duk abin da za mu iya yi domin samun hakan," kamar yadda ya bayyana.
"Akwai magidancin da aka sace wa mata kusan 20, mazan gidan ne kaɗai suka tsira. To yanzu irin wannan gidan ba ka san ma ta yaya za ka yi musu jaje ba."
A cewarsa, mako biyu da suka wuce ma 'yanbindigar sun shiga garuruwan Gidan Goga, da Tungar Gada, da Gidan Madu, inda suka sace mata kusan 100, kuma a cewarsa har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton suna hannun masu garkuwar.
"Mu ma a yankinmu na Malikawa da Kakindawa da sauran yankunan da ke kusa, duka zaman ɗar-ɗar da fargaba ake yi," in ji shi.
A baya-bayan nan, hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe wasu manyan jagororin 'yanfashin daji, amma duk da haka matsalar ba ta kau ba.