Yin hira da baƙin fuska na taimaka wa walwalar ɗan'adam

    • Marubuci, Merve Kara Kaska da Anya Dorodeyko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hatta 'yar gaisuwa da za ku yi wa juna kamar "barka" ko "sannu" a kan titi ko a shagon sayen kayayyaki za ta iya ƙara farin ciki a zukata.

Sakamakon wani bincike da aka gudanar a Turkiyya a kwanan nan ya ƙara bayani kan sauran bincike a duniya game da yadda hulɗa tsakanin mutane za ta iya haɓaka walwalarsu.

"Mun gano cewa hira da mutanen da mutum bai sani ba na da tasiri a kyautatuwar rayuwar mutum," in ji Esra Ascigil, shugabar marubuta binciken na Tsangayar Zamantakewa a Jami'ar Sabanci.

Ire-iren hirar sun ƙunshi gode wa direban da ya tuƙa mutum idan zai fita daga motar, ko kuma gaishe da mutanen da mutum ya sani, a cewarta.

Sai dai kuma wasu binciken sun nuna da yawna manyan mutane ba su son yi wa baƙin fuska magana.

Ta yaya 'yar hira ke ke bayar da gudummawa ga walwalar mutane, kuma ta yaya mutum zai ƙirƙiri hira ba tare da matsala ba?

Amfanin yin hira da baƙin fuska

Duk lokacin da mutum ya yi magana da baƙuwar fuska walwalarsa kan ƙaru kuma zai ji 'yar shaƙuwa da wurin da suka yi magana, a cewar Dr Gillian Sandstrom, wani mai nazarin tunanin ɗan'adam a Jami'ar Sussex da ke Birtaniya.

Tana cikin shugabannin da suka gudanar da bincike kan alfanun yin hira da baƙi, kuma ɗaya cikin marubutan wannan binciken na Turkiyya.

"Yin hira da baƙin fuska na taimakawa wajen jin cewa kana da amfani kuma mutane sun san kana nan, wanda babbar buƙata ce ta ɗan'adam. Yakan shafi ba wai abin da muke ji a jikinmu ba kawai, har a fili ma," a cewarta.

Tun bayan da Dr Sandstrom ta ji sha'awar bincike a kan hakan shekara 10 da suka wuce, ta yi hira da ɗaruruwan mutane duk da cewa tana ganin kanta a matsayin mai kunya, kuma maras son magana.

Ta ce hakan ya sauya yadda take kallon mutane da kuma ƙarin yarda da mutanen.

'Yar hira ƙarama na taka rawa kaitsaye wajen ƙarfafa alaƙar mutane, in ji Itaru Ishiguro, wani mai bincike a Jami'ar Rikkyo da ke Japan.

"Iriin wannan yanayin na jin an karɓe ka a cikin al'umma na shafar walwalar mutum ta hanya mai kyau," a cewarsa.

Me ya sa hira da baƙin fuska ke yi wa wasu mutanen wuya?

A cewar Dr Sandstrom, mutane kan manta cewa akwai alfanu a yin hira, suna ganin ba ta da amfani. Amma abin da ya fi damun mutane shi ne fargaba.

"Bayanai sun nuna cewa abin da mutane suka fi jin tsoro - har ma ya wuce fargabar kada a jizga su - shi ne yin hirar da mutum zai ji kunya," in ji ta.

Itaru Ishiguro ya ƙara da cewa wasu kuma na ganin yin hira haka kawai ba ta dace da al'ada ba, kuma hakan na iya sauyawa hatta a cikin wata ƙasa guda ɗaya.

Hirar tsira da lafiya

Akwai ƙungiyoyin da kan yi gwagwarmayar bayar da shawarar yadda yara za su tsira da lafiyarsu duk lokacin da suka haɗu da wani baƙon fuska. A ƙsashen da ke magana da harshen Ingilishi, akan kira hakan da "Stranger Danger".

"Yanzu shawarwarin na sauyawa. Tabbas wasu baƙin na da matsala, amma kuma mukan nemi taimakon wasunsu a wani lokacin," kamar yadda Dr Gillian Sandstrom ta yi bayani.

"Misali, a Birtaniya akan koya wa yara yadda za su gane baƙi "marasa matsala" da za su iya amincewa da su, kamar iyayen wasu yaran, ko jami'an tsaro kamar 'yansanda da ma'iakatan kantinan sayayya.

Dr Sandstorm na ganin akwai hanyoyin da manya za su bi masu yawa wajen yin hira da baƙin fuska.

"Ba wai ina bayar da shawarar a kama hira da mutane a cikin duhu ba. Amma idan a fili ne, inda mutane suke, me ya sa za mu koma gefe alhalin za mu iya amfani da damar haɗuwa da jama'a?"

Hanyoyi biyar da za ku iya fara hira

Dr Sandstrom ta bayar da waɗannan shawarwarin da mutum zai iya ƙirƙirar hira da baƙin fuska:

  • Lura da abin da kuke da shi iri ɗaya. "Shi ya sa mutane kan yi magana kan yanayin zafi ko sanyi. Ko kuma idan kuna cikin lambu ne sai ka ga furanni na tasowa, kana iya yin magana a kansu."
  • Yi tambayoyi. "Akasari nakan tambayi mutane abin da suke yi. Nakan tambayi wani a jikin jirgi cewa ina za ka je? Magana ce ta lura da abin da sauran mutane ke yi. Indai za ka tambaya cikin sanyin rai ba wai kamar kana tuhumar su ba, mutane za su kula ka."
  • A wani wurin kallace-kallace ko sayayya. "Kana iya tambayar ma'aikacin wurin mafi darajar kayansu da ke wurin. Za su iya nuna maka abubuwan da ma ba ka gani ba, har ma su ba ka labari mai daɗin ji."
  • "Mutane za su iya ba ka shawara ko taimaka maka ma idan ka tambaya. A gefe guda kuma, za ka iya yin tayi. Idan ka ga wani yana neman wani abu, kana iya cewa: 'Yaya, kana buƙatar wani taimako ne?'
  • Ka yaba wa mutane. "Ba zan bayar da shawarar mutum ya yaba wa wani ba game da tufafin jikinsu saboda zai ji kamar an saka masa ido, amma idan ka yi magana kan wani abu da suka zaɓa, ko suka aikata - kamar sarƙar wuyansu, ko kalar gashinsu - zai ji daɗi saboda wani wanda bai zama dole ya yabe su ba ya yi hakan."