Ambaliyar ruwa a Turai alama ce ta ɓarnar da sauyin yanayi zai haifar nan gaba

    • Marubuci, Mark Poynting and Greg Brosnan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen Yanayi da Kimiyya na BBC
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ambaliyar ruwa mai muni da tsakiyar nahiyar Turai ke fama da ita ta ta'zzara sakamakon sauyin yanayi kuma tana yin nuni da irin matsalar da duniya za ta shiga a shekaru masu zuwa, in ji masana kimiyya.

Guguwar da ake yi wa laƙabi da Boris ta auka wa ƙasashen da suka haɗa da Poland, da Czech Republic, da Romania, da Austria, da Italiya, abin da ya jawo mutuwar mutum 24 da asarar biliyoyin kuɗaɗe.

Cibiyar World Weather Attribution (WWA) wasu ruwa da aka jera kwana huɗu ana yi shi ne mafi yawa da aka taɓa gani a tsakiyar Turai - yanayin da ya ninka abin da aka yi hasashe saboda sauyin yanayi.

Wani abu mai ɗan daɗin ji shi ne, an yi hasashen guguwar tun kafin ta auku, abin da ke nufin wasu yankunan sun shirya tsaf da zimmar kauce wa mace-mace.

Masana kimiyya a WWA sun yi hasashen tasirin da sauyin yanayi zai yi idan aka samu aukuwar bala'i idan aka kwatanta da wani tsari da ke kintata yadda duniya za ta ksance idan da a ce ba a amfani da makamashi masu gurɓata muhalli tsawon shekara 200.

Nau'in ruwan saman da Guguwar Boris ta haifar ya fara janyewa - amma kuma ana sa ran zai ci gaba da faruwa sau ɗaya duk shekara 100 zuwa 300 bisa la'akari da yanayin da duniya ke ciki a yanzu, wadda ta ɗumama da 1.3C saboda makamashi mai gurɓata muhalli.

Amma idan zafin ya kai ma'aunin 2C, girman matsalar zai ƙaru da kashi 5% sannan yawan faruwarta ta ƙaru da kashi 50% cikin 100, a cewar gargaɗin WWA.

Idan ba a ɗauki matakai masu ƙarfi ba, ɗumamar duniya za ta kai kusan 3C nan da ƙarshen ƙarni.

"Tabbas wannan ne irin abin da za mu ci gaba da gani nan gaba," a cewar Friederike Otto, babban malamin sauyin yanayi a kwalejin Imperial College London kuma ɗaya cikin marubuta binciken WWA.

"Babbar alama ce ta sauyin yanayi [...] da ta zarce dukkan abin da muka sani a baya sosai."

Turai ta fi sauran nahiyoyin duniya ɗumama cikin sauri. Shekara biyar da suka wuce ta ɗumama da kashi 2.3C fiye da yadda ta ɗumama a tsawon rabin ƙarni na 19, in ji cibiyar Copernicus.

Wannan ba wai zafi mai tsanani kawai zai dinga haifarwa ba, akwia kuma mamakon ruwan sama musamman a arewaci da tsakiyar Turai. Lamarin ya fi ƙazancewa a kudancin Turai saboda yawan sauyin da yanayi ke yi.

Babban dalilin da ke haifar yawan ruwan sama shi ne idan sama ta ɗumama da yawa ta fi tara laima - kamar kashi 7% a kan duk 1C. Wannan ƙarin laima ne kan jawo mamakon ruwan sama.

Yanayi mai jan ƙafa

Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa Guguwar Boris ta jawo ruwa mai yawa shi ne, yanayin ya tsaya 'cak', abin da ya sa ta jibge ruwa mai yawa a yankunan na tsawon kwanaki.

Ana ganin akwai hujja cewa tasirin sauyin yanayi zai iya sakawa wannan jan ƙafar ya dinga faruwa akai-akai. Amma ana ci gaba da muhawara kan hakan.

Ko da ba mu fuskanci jan ƙafa ba a harkokin yanayi nan gaba, sauyin yanayin na nufin duk lokacin da sama ta tara laima da yawa zai iya zama abu mai haɗari.

"Irin wannan yanayi na faruwa ne saboda tiriri mai gurɓata muhalli, saboda haka yawa da kuma ƙarfin ruwan ya zarce abin da ya kamata a gani," kamar yadda Richard Allan, farfesa kan sauyin yanayi a Jami'ar Reading.

Ana ci gaba da samun hasashen yanayi mai ɗan kyau, kuma a wannan lokacin ana iya hasashen yawan ruwan da za a samu tun kafin a yi shi.

Hakan na nufin za a shirya da wuri game da aukuwar ambaliya.

Wannan na cikin dalilan da suka sa ba a samu mace-mace masu yawa ba kamar a baya - lokacin ambaliyar a 1997 da 2002 - duk da cewa ruwan na yanzu ya fi yawa kuma ambaliyar ta fi shafar wurare da yawa.

"An kashe kuɗaɗe masu yawa bayan ambaliyar da aka yi a baya [na kafawa da kuma sabunta] ganuwar ambaliyar," a cewar Mirek Trnka na cibiyar Global Change Research Institute.