Seaman Abbas: Shin saki ko kora daga aiki sojoji suka yi masa?

..

Asalin hoton, Brekete Family

Lokacin karatu: Minti 3

Da safiyar ranar Juma'a ne labarin sojan ruwan nan mai suna Seaman Abbas Haruna da mai ɗakinsa ta fallasa irin uƙubar da yake ciki tsawon shekaru shida, ya sauya bayan sojan da mai ɗakinsa sun bayyana a tashar Brekete Family.

Mai ɗakin nasa dai Hussaina cikin rawar murya da kuka ta shaida wa tashar cewa "sun kore shi. Sun fito da shi daga gate. Ko sun ɗauka ba na son mijina, Allah ya sa haka ne ya fi alkairi. Koma dai me suka yi masa ni ina son mijina."

A nan ne Seaman Abbas Haruna ya tashi ya kama mai ɗakin nasa yana rarrashinta inda ya karɓi abin magana yana mai cewa "ni kam ba na ce ki yi haƙuri ba? Kullum kina kuka ina ba ki haƙuri kuma na ce ki yi haƙuri." In ji Seaman Abbas.

Kafin nan sai da Hussaina ta yi wa al'ummar Najeriya godiya kan yadda suka tallafa mata har aka kai ga sakin mijin nata.

Sai dai yanzu abin da ƴan Najeriya ke son sani shi ne ko an saki sojan ne kuma zai ci gaba da aikinsa ko kuma an sake shi tare da sallamar sa daga aiki.

Korar Seaman Abbas sojoji suka yi ko saki?

BBC ta tambayi mai magana da yawun rundunar tsaron Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau dangane da ko a wane hali aka sallami sojan.

"Jiya aka sake shi sannan kuma an kore shi daga aiki". In ji Birgediya Janar Tukur Gusau.

Bisa al'adar aikin soji da ma sauran ayyukan gwamnati a Najeriya, idan aka kori mutum daga aiki to ba za a ba shi haƙƙoƙinsa ba.

Kotun soji ce dai kawai take da hakkin korar mutum daga aikin soji a Najeriya.

Yanzu abin jira a gani shi ne sakamakon binciken da rundunar tsaron ƙasar ta ce za ta yi dangane da batun.

Da ma dai babban hafsan tsaron Najeriyar, Janaral Christopher Musa ya sha alwashin yin bincike kan wannan batu.

Seaman Abbas Haruna dai ya kwashe shekaru 12 yana aikin soji kamar yadda mai ɗakin nasa Hussaina ta bayyana cewa "yana cikin sojojin ruwa na 21AK" abin da ke nufin ya fara aikin ne a shekarar 2012.

Asalin abin da ya faru da Seaman Abbas Haruna

..

Asalin hoton, Brekete family

Makonni biyu da suka gabata ne dai a cikin wani faifan bidiyo Hussaina matar sojan ruwan mai suna Abbas Haruna ta bayyana cewa an gana masa uƙubar da ta wuce misali.

Hussaina ta bayyana ne a wani shiri na gidan talabijin na 'Brekete Family', inda a ciki ta bayyana wasu zarge-zargen cewa ba a yi wa mijinta da ma su iyalansa ɗin adalci ba.

Matar sojan wadda ake kira Maman Shahid, ta bayyana cewa mijin nata ya samu saɓani ne da wani babban hafsan soja, inda tun a lokacin aka kama shi, aka tsare, kuma a cewarta kusan shekara shida ke nan yana tsare.

Bidiyon na Hussaina ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka riƙa yaɗa shi, wasu na zagi, wasu na Allah wadai, wasu kuma suna cewa a dai yi bincike.

Babban abin da ya ja hankalin mutane shi ne yadda Hussaina ta bayyana yadda ta sha faɗi-tashi da tafiye-tafiye tsakanin Kaduna da Taraba da Abuja da Gombe duk a kan mijin.