An kai ƙarar Instagram da YouTube kan 'mallake tunanin yara'

Four parents holding up framed photos of their children, whom they say died due to social media–related harms standing alongside one another outside a courthouse in Los Angeles.

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Lily Jamali
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North America Technology correspondent
    • Aiko rahoto daga, Los Angeles
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kamfanonin sada zumunta biyu mafi girma a duniya na fuskantar tuhuma kan samar da shafukan da suka zamo "alaƙaƙai" yayin da aka fara sauraron ƙarar da aka shigar a Amurka kan yadda shafukan Instagram da YouTube ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwar al'umma.

A lokacin da suka karanto ƙorafin a karon farko a wata kotu da ke birnin Los Angeles, mai shari'a Carolyn B. Kuhl da mai taimaka wa alƙali Mark Lanier, sun ce mai ƙarar ta samu matsalolin ƙwaƙwalwa sanadiyyar ɗauke hankali irin na shafukan sada zumunta.

"Waɗannan kamfanoni sun samar da shafukan da aka tsara su ta yadda za su zama alaƙaƙai a ƙwaƙwalwar yara, kuma an yi hakan ne da gangan," in ji Lanier.

Lauyoyin da ke kare kamfanonin Meta da YouTube sun shaida wa kotu cewa wasu abubuwa daban ne suka yi illa ga lafiyar mai ƙarar, ba sakacin su ba.

Mai shigar da ƙaran Kaley G.M, wadda ta fi son a kira ta da K.G.M ta ce ta cutu ne daga shafukan sada zumunta a lokacin da take yarinya.

Mai taimaka wa alƙali, Lanier, ya kuma yi zargin cewa Meta da YouTube sun ƙi su gargaɗi mutane game da haɗarin da shafukansu ke da shi ga yara.

"Wannan shari'a ta shafi kamfanoni biyu ne mafiya duniya a tarihi, wadanda suka kitsa mallake tunanin yara," in ji Lanier.

''Zan nuna muku shafukan mallake mutane da suka ƙirƙira, da saƙonni da kuma takardu na cikin gida wadanda ba kowa ne yake da ikon gani ba, da kuma saƙonnin email da (shugaban Meta) Mark Zuckerberg da shugabannin YouTube suka aika."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wani ɓangare na wani saƙon email daga shekarar 2015 da Lanier ya nuna wa kotu, Zuckerberg ya buƙaci a samu ƙarin kashi 12% na yawan lokacin da mutane ke kwashewa a shafuka mallakin Meta, domin cimma manufa ta kasuwanci.

A game da YouTube kuwa, Lanier ya ce shafin, wanda mallakin kamfanin Google ne ya riƙa ƙoƙarin jan hankalin yara ta yadda zai riƙa ''ƙara kuɗin tallace-tallace''.

Daga nan sai Lanier ya zargi YouTube da yin amfani da kasancewar iyaye na da harkoki da yawa, saboda haka nan suna neman wani abu da zai riƙa dauke hankalin ƴaƴansu ta intanet.

A lokacin da aka bai wa kamfanin Meta damar kare kansa, lauyan da ke kare kamfanin Paul Schmidt ya jawo hankalin mai kare K.G.M. game da zargin cewa Instagram ya yi illa ga tunanin mai ƙara.

Ya bayyana K.G.M. a matsayin wadda ke fama da wasu matsaloli na iyali, cewar iyalinta sun yi watsi da ita, sannan ta fuskanci tsangwama da duka daga iyayenta.

Schmidt ya shaida wa kotu cewa yana jinjina wa K.G.M kan "ƙoƙarin da ta yi sosai wajen shawo kan matsalolin" da ta fuskanta.

Ya kafa hujja da wasu takardu da suka nuna cewa iyalin su K.G.M na da tarihi na rikicin cikin gida kuma sun fara zuwa wajen ƙwararru domin samun shawarwari tun tana yar shekara uku.

Schmidt ya nuna wasu lokuta a baya da K.G.M ta yi bayani kan rayuwar iyalinta, ciki har da cewa mahaifiyarta ta yi mata tsawa, ta kuma kira ta maras hankali, lamarin da ya kai ga cewa ta fara tunanin kashe kanta.

"Na san cewa waɗannan kalamai ne masu wahala," kamar yadda Schimidt ya faɗa wa masu taimaka wa alƙali. "Idan ana magana kan batun abubuwan da kan yi illa ga tunanin mutum, wadannan na daga cikin abubuwan da ake lura da su," in ji shi.

Zaman kotun na ranar Litinin shi ne na farko a shari'ar da ake sa ran za a kwashe mako shida ana yi, wanda zai iya zama zakaran gwajin dafi ga ƙararraki makamantar wannan da ake da su a fadin Amurka, wadanda za su iya tasowa a wannan shekara.

Shari'ar, wadda ake yi a birnin Los Angeles za ta iya zama wata madogara ga ƙararrakin da iayalai da dama suka shigar kan zargin cewa shafukan sada zumunta sun jefa ƴaƴansu cikin halin ƙunci, yayin da su kuma kamfanonin ke barranta kansu daga abin da zai iya biyo baya bayan mutane sun yi amfani da shafukansu.

A cikin makonni masu zuwa za a saurari bayanai daga masana, da iyalan da ƴaƴansu suka mutu, sai kuma daga bakin Mark Zuckerberg da shugaban Instagram Adam Mosseri, sai kuma shugaban YouTube, Neal Mohan.

Haka nan an sa ran ji daga bakin wasu tsofaffin ma'aikatan kamfanin Meta waɗanda suka zamo masu kwarmata bayanai game da yadda shafukan sada zumunta kan zame wa ƙananan yara alaƙaƙai.

Hukuncin kotun zai iya samar da wata madogara ta biyan diyyar kuɗi da zai shafi dubban shari'o'i da iyaye da masu wakiltar jihohi da kuma makarantu suka shigar a fadin Amurka.

A ɗaya daga cikin irin waɗannan ƙararraki da manyan alƙalan jihohi 29 suka shigar, masu shigar da ƙara sun nace kan cewa kotu a jihar California ta tursasa wa kamfanin Meta, mamallakin dacebook da instagram ya dakatar da wani ɓangare na ayyukansa.

Dukkanin jihohin na son a yi wani hukunci wanda zai buƙaci Meta ya goge duk wani shafin da aka bude mallakin yara ƴan ƙasa da shekara 13, ya goge duk wasu bayanai da ya tattara na masu amfani da shafin facebook da Instagram ƴan ƙasa da shekara 13, sannan ya goge bayanan da ya tattara waɗanda ƙirƙirarriyar basira ke amfani da su wajen tsara abin da masu amfani da shafukan ke gani.

Haka nan kuma wasu manyan alƙalan jihohi 18 na neman kotu ta turasasa wa kamfanin aiwatar da wani tsari na kare masu amfani da shi ta hanyar taƙaita lokacin da yara ke amfani da shafin, ta yadda ba za su iya amfani da shafukan ba a lokacin makaranta da kuma tsakar dare.

Haka nan suna buƙatar shafin ya soke wasu salailai da shafin ke amfani da su, kamar kallon abubuwa ba tare da iyakancewa ba, da bidiyon da ke kunna kunna kansa, haka nan shafin ya haramta amfani da salon ƙara wa hoto kyau, wato filta.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, kamfanin Meta ya fitar da wasu sabbin ƙa'idoji kamar "shafin yara ƴan shekara 12 zuwa 19" a instagram, da kuma tace abin da yara ƴan shekara 16 zuwa ƙasa za su iya gani.

Masu shigar da ƙarar sun bayyana matakin na Meta a matsayin abin da bai taka kara ya karya ba, kuma ya yi ne kawai domin nuna cewa ya yi wani abu.

Kimanin mutane 100 ne suka kalli zaman kotun na ranar Litinin, cikin su har da iyayen da suke zargin cewa yaransu sun mutu ne sanadiyyar yadda shafukan sada zumunta suka tsara shafukan nasu.

Sai dai kamfanonin sada zumunta sun bayyana cewa ba su da alhakin abubuwan da wasu mutane na daban suka wallafa a shafukansu, ƙarƙashin dokar tarayya ta Amurka.

Shafukan Snapchat da TikTok sun warware tasu matsalar da mai shigar da ƙara K.G.M a watan da ya gabata, saboda haka ba su a cikin wadanda ake tuhuma a ƙarar ta ranar Litinin.