Chelsea na sha'awar sake ɗaukar Marc Guehi daga Palace

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea na sha'awar sake ɗaukar ɗan wasan tawagar Ingila mai taka leda a Crystal Palace, Marc Guehi.
Ƙungiyar Stamford Bridge ta sayar da Guehi, mai shekara 24 ga Palace kan £18m a 2021 - daga nan Todd Boehly da Clearlake Capital suka mallaki Chelsea.
Har yanzu Chelsea ba ta tuntuɓi Palace ba kan batun Guehi, amma wakilan ɗan wasan sun kwan da sanin batun.
Saura yarjejeniyar wata 18 ta ragewa Guehi a Palace, wanda ya kulla kwantiragin kaka biyar a lokacin da ya koma Selhurst Park da taka leda.
Chelsea na fama da karancin masu tsare baya, shi ya sa take son sake ɗaukar Guehi a Janairu, bayan da Wesley Fofana ke jinya.
Haka kuma Benoit Badiashile na jinya, wanda ake sa ran sai cikin watan Fabrairu zai koma taka leda.
Wasa biyu Guehi ya buga a Chelsea, sune a Carabao Cup a 2019 daga nan ta bayar da aronsa Swansea mai buga Championship, sai ta sayar da shi ga Palace.
Kawo yanzu ya yi wa tawagar Ingila karawa 22.
Palace ba ta sallama tayin da Newcastle ta yi wa Guehi ba kan fara kakar nan kan ƙudi da ya kai £65m.
Wasu rahotannin na cewar Chelsea za ta dawo da Trevoh Chalobah daga Palace da yake yi wa wasannin aro.
Tuni kuma ta kira ɗan wasan tawagar Argentina, Aaron Anselmino daga Boca Juniors, domin buga mata wasannin a Stamford Bridge.










