Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce gaskiyar soke masarautar Sarkin Hausawan Sasa ta Ibadan?
Sarkin Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya soke matsayin sarautar sabon sarkin Sasa a karamar hukumar Akinyele, bayan gano cewa sarautar ba ta cikin kundin tsarin mulkin Ibadan.
Sarkin ya sanar da haka ne a yayin taron hukumar gudanarwar birnin da aka yi a fadar sarkin da ke Oke Aremo a Ibadan.
Rahotanni sun ambato cewa Sarkin Sasa shi ne shugaban al'umma Arewa a jihohi 17 da ke kudancin Najeriya kafin rasuwarsa.
A abin da muka ji shi ne mutuwar sarkin na da alaka ne da sanarwar da muka ji cewa dansa Ahmed Haruna, da aka fi sani da Ciroma shi ne sarkin Sasa ba tare da amincewar sarkin Ibadan ba.
Daga baya ne, mai magana da yawun sarkin Ibadan, Gbenga Ayoade, cikin wata sanarwa ya ce sarkin Ibadan ya ce bai san wani sarki ba sai Chif Akinade Ajani Amusa, a matsayin Baale Sasa a Akinyele.
Ya ce, abin da muke so jama'a su sani shi ne dukkan wadanda ke zaune a Sasa na karkashin kariyar Baale Sasa.
"A don haka yana da muhimmanci sosai a rinka girmama shi da kuma bin duk wasu umarni da ya bayar."
Ya ce," Ba za mu bari wani ya rinka kin bin umarni da girmama Baale Sasa ba, kuma duk wanda ya yi hakan to martaba da kimarsa za ta zube a idon sarkin Ibadan."
Sun zabi sabon Sarkin Sasa ba tare da tuntubar Sarkin Ibadan ba
Lokacin da BBC ta tuntubi Sarkin Ibadan a kan ya yi mata karin haske a kan wannan batu, daya daga cikin dattijan Ibadan wanda baya so a ambaci sunansa ya ce Sarkin Ibadan ko shakka babu ya bayar da umarnin haka.
Ya ce, "Abin da mai magana da yawun Sarkin Ibadan ya fadi gaskiya ne."
"Daga abin da na ji, sun ce suna so hakan ne tsawon kwanaki takwas, to amma kuma daga bisani sai suka fahimci cewa ana bashi girma da karramawa kamar irin wadda ake ba wa Sarkin Sasa."
Dattijon ya shaida mana cewa duk da ya ke Sarkin Ibadan ba shi ne zai nada Sarki Sasa ba, dole ne a tuntube shi kafin sanar da duk wanda za a bawa sarautar saboda ya bayar da umarnin hakan.
Rikicin cikin gida
Da dama daga cikin al'ummar Hausawa a birnin Ibadan na alaƙanta halin da masarautar ta shiga ga rashin haɗin kai da kuma ƙoƙarin yi wa juna zagon ƙasa.
A tattaunawarsu da BBC, wasu daga daga cikin iyalan tsohon sarkin Sasa sun bayyana cewa ba su amince da naɗin da aka yi wa ɗan marigayin ba a matsayin sabon sarki.
Alhaji Auwal Haruna Mai Yasin, wanda ɗa ne ga marigayi tsohon sarkin Sasa ya ce tun asali ba a riga an tabbatar da sarautar ga ɗan'uwansu Ahmad Haruna Mai Yasin Ɗaya ba.
Ya ce: "Shi ɗan'uwanmu an ƙaddamar kan cewa an ba shi (sarauta), kafin naɗi, to amma sai ya riƙa yawo da jiniya da yin abubuwa na riga-malam-masallaci, wannan abin da ya tunzura masarautar Olubadan, har aka kai ga rubuta takarda a kan cewa ba a naɗa shi ba kuma an dakatar da naɗa shi."
Ya ƙara da cewa yanzu ya kamata Hausawan da ke yankin su ajiye duk wani batu na cewa akwai wani da aka bai wa sarautar.
"Yanzu za mu yi taro a tsakaninmu cikin iyali da kuma sarakuna, kuma za mu sanar wa duniya idan aka samu matsaya kan wanda ya cancanta a ba shi," in ji Auwal Haruna Mai Yasin.
Martanin masarautar
A ɓangare ɗaye kuma mutumin da tun farko aka zaɓa a matsayin wanda za a naɗa domin ya gaji sarautar, wato Ahmad Haruna Mai Yasin ya mayar da martani ta bakin magatakar masarautar, Haruna Yaro.
A tattaunawarsa da BBC ya yi zargin cewa siyasa ce aka saka a cikin batun sarautar.
Ya ce: "Ba mu da masaniya kan wata sanarwa da aka bayar daga fadar Olubadan domin babban wakilin Olubadan shi ne Baale ɗin Sasa, saboda haka ba da yawun Olubadan ake magana ba.
"Wannan ba wani abu ba ne, in sha Allahu za a sansanta rikicin," in ji Haruna Yaro.