Wane ne cikakken ɗan gudun hijira Kuma wane irin tallafi zai iya samu?

Lokacin karatu: Minti 6

A makon da ya gabata, ƴan Afirka ta kudu fararen fata su 59 suka sauka a tashar jirgin sama ta Dulles da ke kusa da Washington DC bayan an amince da su a matsayin ƴan gudun hijira.

Shugaba Trump ya ce fararen fata ƴan Afirka ta Kudu, wata ƙungiyar marasa rinjaye da suka fito daga tsatson turawan mulkin mallaka, na fuskantar ''wariyar launin fata' da kuma '' kisan ƙare dangi''

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce zarge-zargen ba gaskiya bane, kuma babu hujjar da za ta goyi bayansu.

A sanye da ƙananan kaya tare da ɗaga tutar Amurka, mazan da matan da yaran sun sami tarba ta musamman daga hukumomin Amurka, wani abu da masu sharhi ke cewa ya sha bamban da matsayar gwamnatin Trump a yanzu kan ƴan gudun hijira.

A watan Janairu, Shugaba Trump ya sanya hannu kan wata dokar shugaban ƙasa na dakatar da shirin tsugunar da ƴan gudun hijira.

Wannan mataki ya dakatar da ƙarbar ƴan gudun hijira, wanda ya bar fiye da ƴan gudun hijira 100,000 babu matsuguni.

Sai dai dokar ta amince za a iya tsame wasu ta hanyar la'akari da wasu abubuwa.

Wata ɗaya bayan nan, Shugaba Trump ya sanya hannu kan wata dokar da ta amince da fararen fata ƴan Afirka ta kudu a matsayin ƴan gudun hijira.

Matakin ya janyo suka da fushi a faɗin Afirka ta Kudu inda fararen fatan, wanɗanda su ne kashi 7 na yawan alummar ƙasar suka mallake rabin filayen noma na ƙasar.

Shugaba Ramaphosa ya bayyana masu yin hijirar zuwa Amurka a matsayin ''matsorata''.

''Idan kuka kalli dukka rukunin mutanen da ke ƙasar, ko baƙaƙe ko farare, sun tsaya a ƙasar saboda ƙasar mu ce kuma ba za mu tsere daga matsalolinmu ba. Dole mu tsaya a nan mu magance matsalolinmu,'' in ji shi.

Wannan mataki ya kuma fuskanci suka daga ƙungiyoyin kare haƙƙin biladama, da masu sharhi, har ma da Cocin Episcopal, wanda ya ce ba zai taimaka wajen sake tsugunar da su ba saboda saudaukarwarsa ga tabbatar da adalci da sasanci tsakanin ƙabilu, wanda hakan ya kawo ƙarshen alaƙarsu ta kusan shekara 40 da gwamnatin Amurka.

BBC ta tambayi mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka John Landau kan me ya sa aka amince da fararen fata ƴan Afirka da Kudu a matsayin ƴan gudun hijira maimakon mutanen da ke tserewa azabtarwa kamar ƴan Afghanistan.

Ya ce an yi la'akari da sauƙin ƴan gudun hijira su saje cikin alumma, wanda ya tayar da muhawara kan rawar da siyasa da buƙatun ƙasa ke takawa wajen zaɓen wanda za a amince da shi a matsayin ɗan gudun hijira.

Wane ne ɗan gudun hijira?

Taron duniya kan ƴan gudun hijira na 1951 ya bayyana ɗan gudun hijira da cewa shi ne ''mutumin da ke cikin tsoron muzguna masa saboda launin fatarsa ko addininsa ko ƙasarsa ko kasancewarsa memba na wata ƙungiya ko ra'ayin siyasa, wanda kuma ya fice daga ƙasarsa, ya koma wata ƙasar domin samun kariya, ko kuma mutum da yake wajen ƙasarsa kuma yake fargabar komawa saboda tsoron muzgunawa a ƙasarsa.

Ma'anarsa ta farko na da nasaba da ƴan gudun hijira daga Turai bayan yaƙin duniya na biyu, sai dai taron ya yi masa gyaran fuska a 1967 domin cire batun yanki.

Baya ga samar da ma'anar ɗan gudun hijira, taron ya kuma fitar da haƙƙoƙin ƴan gudun hijira.

Alƙaluman ƴan gudun hijira

A cewar Hukumar kula da ƴan gudun Hijira ta Majalisar dinkin duniya UNHCR, zuwa watan Yunin 2024, akwai ƴan gudun hijira miliyan 43.7 a faɗin duniya. Kuma kashi 65 cikin 100 na zuwa ne daga ƙasashen huɗu: Syria da Venezuela da Ukraine da kuma Afghanistan.

Kashi 71 na ƴan gudun hijira na zama ne a ƙasashe masu tasowa da masu matsakaitan tattalin arziƙi. Iran da Turkiyya da Colombia da Uganda su ne ƙasashen da suka fi tsugunar da ƴan gudun hijira.

Kusan kashi 70 na ƴan gudun hijira na samun matsuguni ne a ƙasashen da ke maƙwaftaka da su.

Ƙarƙashin shugaba Joe Biden, adadin ƴan gudun hijira da aka tsugunar a Amurka ya kai 125,000 a shekara.

A shekararsa ta ƙarshe kan mulki, fiye da mutane 100,000 aka amince da su a matsayin ƴan gudun hijira.

Mene ne bambanci tsakanin ɗan gudun hijira da mai neman mafaka da ɗan ci-rani

Ɗan gudun hijira shi ne wanda ya gudu daga ƙasarsa saboda yaƙi ko rikice-rikice ko muzgunawa. Mutumin na da ƴanci a doka na samun kariya idan an amince da shi a matsayin ɗan gudun hijira.

Mai neman mafaka kuma shi ne wanda shi ma ya gudu daga ƙasarsa saboda yaƙi ko rikice-rikice, amma doka ba ta amince da shi a matsayin ɗan gudun hijira ba.

A cewar hukumar kula da ƴan gudun hijira ta duniya IOM, babu ma'anar ƴan ci-rani da aka amince da shi baki ɗaya, amma ma'anarsa da aka fi amfani da shi ita ce mutumin da ya bar inda ya ke , a cikin ƙasar da yake ko zuwa ƙasar waje, na zaman wucin gadi ko na din-din-din, saboda dalilai da dama.''

Waɗanne abubuwa ne ke tasiri kan wanda za a amince da shi a matsayin ɗan gudun hijira?

Ana amincewa da mutum a matsayin ɗan gudun hijira bisa ga ma'anarsa da dokar ƙasa da ƙasa ta amince, sai da kowacce ƙasa na da matakan ta domin tantance wanda ya cancanta.

Tendei Achiume, wata farfesa a fannin shari'a a jami'ar Stanford, ta ce ana samun son zuciya a lokacin da ake tantance wane ne za a amince da shi a matsayin ɗan gudun hijira.

Ta ce wasu ƙasashen kan fi son su taimakawa mutanen da suke da wata alaƙa, inda kuma ake bai wa fararen fata ƴan gudun hijira wata ''gata da ƙariya ta musamman'' wadda ba a bai wa waɗanda ba fararen fata ba.

'' Ukraine ta kasance abar misali a irin hakan,'' in ji ta.

'' An yi ta cece-kuce a faɗin duniya a lokacin da aka ga hotunan mutanen da ke tserewa daga ƙasar, inda aka ƙi bai wa waɗanda ba fararen fata dake tserewa ba muhimmanci.

Achiume ta kuma ce buƙatun ƙasa na tasiri game da yadda ƙasar za ta zaɓi ƴan gudun hijira. A misali, wata ƙasa za ta iya nuna sha'awar amincewa da ƴan gudun hijira idan tana da hannu cikin ɗaiɗaicewarsu.

'' Wasu lokutan ƙasashe za su iya zaɓin ƴan gudun hijirar da suka fi rauni, kamar mata da yara da tsofaffi,'' a cewar Achiume.

''Sai dai dokar ƙasa da ƙasa ta haramta nuna wariya kamar ta ƙabila ko addini ko asali.''

Yaya ƴan gudun hijira a Amurka suka ji da abubuwan da ke faruwa a yanzu?

Ƴan gudun hijira a faɗin Amurka na nuna fargaba game da sauyin tsari da aka samu farat ɗaya, in ji Nils Kinuani, shugaban wata ƙungiyar da ke goyon bayan ƴan gudun hijira daga Afirka da ke Amurka.

'' Mutane basu san abin da zai iya faruwa ba ko kuma yadda za su tsara rayuwarsu, in ji shi.

Ya ce matakin bai wa fararen fata ƴan Afirka ta kudu matsayi na zama ƴan gudun hijira cikin ɗan ƙanƙanin lokaci , yayin da wasu dubbai ke shafe shekaru suna nema na aika saƙonnin damuwa.

''An gina Amurka a kan tubalin cewa ita ƙasa ce da ke maraba da mutane wadda kuma ke samar da kariya ga mutanen da ke cikin haɗari. A yanzu kuma muna ganin wannan alfarma, sai waɗanda ke da gata wannan gwamnati za ta bai wa.'' in ji shi.

Kunani ya ce wannan mataki na gwamnatin Trump na da nasaba da ''wariyar launin fata.''

A lokacin da aka tambaye shi ko meyasa akayi gaggawan amincewa da buƙatar fararen fata ƴan Afirka ta kudu akan wasu ƙungiyoyin, shugaban ƙasar ya ce ba saboda ƙabila bane.

'' Ana kashe manoma, waɗanda kuma suka kasance fararen fata ne, amma kuma ko farare ne ko baƙaƙe ne ba shi da wani bambanci a gareni''.

Kuani ya kuma ce matakin Trump ya dace da tsare-tsaren cikin gida na yanzu wanda ake amfani da shi wajen ƙoƙarin gyara matsalolin da ke da alaƙa da wariyar launin fata a Amurka kamar tsarin rage wariya wajen ɗaukar aiki.

Tendai Achiume ta amince da hakan.