Yadda biranen ƙasar Iran ke nutsewa ƙasa saboda tonon ruwa

Ɓaraguzan birnin masarautar Persepolis "ɗaya ne daga cikin wuraren tarihi mafiya ƙayatarwa" in ji hukumar Unesco ta Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da tarihi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɓaraguzan birnin masarautar Persepolis "ɗaya ne daga cikin wuraren tarihi mafiya ƙayatarwa" in ji hukumar Unesco ta Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da tarihi
    • Marubuci, Armen Nersessian
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 8

Matattakalar da aka sassaƙa a jikin dutse da ke kai mutum ginin faɗa a birnin Persepolis, wanda shi ne babban birnin Daular Fasha, ta shekara kusan 2,500 - amma yanzu wurin da kewayensa na nutsewa ƙasa.

An gina ta ne a kan dutse. An ɗan samu sauyi a matsayar ginin amma da ƴan taki kaɗan. Yanzu wurin da ruwa ke gangarowa na ƙara nutsewa a cikin ƙasa duk shekara.

Dandaryar ƙasar da ke kewayen Marvdasht - mai nisan rabin kilomita daga ginin - ta fara rarrabewa da juna, kuma abin na ƙaruwa.

"Akwai tsagewa a kusa da Persepolis da kuma Naqsh-e Rastam wadda muke alaƙantawa da hanzarin da ƙasar ke yi wajen nutsewa," inji Dr Mahmud Haghshenas, na cibiyar binciken albarkatun ƙasa da ke jami'ar Leibniz da ke ƙasar Jamus.

"Ga al'ummar Persepolis, na ga rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke cewa an samun tsagewar ƙasa da ɓarna a wasu wuraren da hakan ke nuna tabbas matsala ce mai alaƙa da tsagewar, sannan hanyar hawa tsaunin na tsagewa."

Sassaken masu gadin fadar Fasha da aka yi ado da su a masarautar sarki Darius a HHPersepolis

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A shekarar 518BC ne Darius I ya samar da Persepolis wanda nan ne babban birnin masarautar Fasha, inda sarkin sarakuna ya gina katafariyar fada

Gawurtaccen wurin tarihi

Hukumar ilimi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta keɓe wurin a matsayin na tarihi a shekarar 1979.

UNESCO ta ce katafaren wurin da aka lalata na dada cikin wuraren masu daraja da aka gano a ban ƙasa.

"Wurin da Fashawa suka sabunta shi, an yi shi ne da kyakkyawan tsari kimiyya, da zane-zane masu ban sha'awa, a iya cewa babu wani wuri da aka baza fasaha da mikiyya wajen yin sa kamar masarautar birnin Persepolis, wadda ta fuskanci sauye-sauye a zamani daban-daban."

Wannan sauyi na zamani haka ya yi ta faruwa har zuwa lokacin da aka samar da daular Fasha, wadda ake gani a matsayin mai karfin iko a fduniya, inda ta mamaye wurare da dama da faɗaɗa daga yammacin Libya zuwa gabashin ƙasar Indiya.

Kyakkyawan sassaken tarihi da aka yi a jikin wani katon dutse. An yi sassaken da ke kama da kofo ko tagogi. Masu yawon bude ido na wucewa ta wurin yayin da ruwan bular sararin samaniya ya kara kayata wurin.

Asalin hoton, Ullstein Bild via Getty Images

Bayanan hoto, Gaban wurin tarihi na Naqsh-e Rostam da aka sassaka daga jikin dutse da har yanzu ya ke tsaye da kafafun shi, amma akwai fargabar nan ba da jimawa ba zai fuskanci barazanar nutsewa

Yawancin wuraren tarihi 28 da UNESCO ta keɓe a Iran na kusa da yankin da ƙasar ke nutsewa, ciki har da ainayin babban birnin Pasargadae da masarautar Fasha ta ke, da birnin Yazid mai cike da tarihi.

Hukumomi sun kuma bayyana hadarin da ake ciki a Isfahan wurin tarihi mai dauke da gadoji da masallatai da suke gab da yankin da ke nutsewar.

A shekarar 2021 UNESCO ta ayyana wani wuri mai nisan kilomita 1,394 daga tashar jirgin ƙasa ta ƙasa da ƙasa ta Iran, a matsayin wurin tarihi to amma shi ma na fuskantar barazana.

Matattakalar da za ta sada ka da kofar shiga wurin ta tsattsage, haka ma ta wajen tagogin da ke jikinsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wurin tarihi da ke Naqsh-e Rostam mai suna Kaba ye Zartoshit da harshen Fasha, mai tsahon mita 14m shi ma jikinsa ya tsattsage

Lokaci na ƙurewa

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dandaɓaryar ƙasar wurin ba ta da tudu, dan haka zai yi matukar wuya a yi saurin gane abin da ke faruwa da harsashin ginin.

Masu bincike na amfani da na'urori da tsaffin hotuna domin gano yanayin da ake ciki.

"Fasahar na bada damar gano dandabaryar kasar da 'yan mitoci idan ana son gane ko yana fuskantar nutsewa," inji Farfesa Mahdi Motagh, na jami'ar Leibniz.

Tawagar masu binciken da ya ke jagoranta na nuna damuwa kan matsalolin da ake cin karo da su da ke nuna girman matsalar yadda kasa ke nutsewa a kasa da biranen Persepolis da Naqsh-e Rostam.

Duk da cewa birnin Naqsh-e Rostam na tsaye da kafafun shi a halin yanzu amma babu tabbacin tsahon lokacin da hakan zai dore, saboda nutsewar da wani wuri da ke kusa da nan ke yi.

"A iyakar da ke tsakanin wurin tarihin mai cike da duwatsu da sarar mu na ganin wuraren da akai watsi da su da kuma kasar wurin ke tsagewa," inji Farfesa Motagh.

"Wurare da dama sun lallace, mun ga yadda wasu suka tsattsage da suka dangana har zuwa Kaba ye Zartosht, da ke Naqsh-e Rostam."

Farfesa Motagh ya ce abu guda da zai yi cikakken bayani da gano girman matsalar shi ne cikakken bincike, in ba haka ba wata rana tabbas wurin nan zai nutse.''

Fitilu da ketowar alfijir sun haskaka gadar Isfahan da aka samar da ita tun karni na 17, mai kofofi 33 a karkashin gadar kuma godin Zayandeh da ya bushe

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images

Bayanan hoto, Iran ta ci gaba da amfani da ruwa duk da barnar da hakan ne yi wa rafukan ta da kuma hadarin da gadar Isfahan mai cike da tarihi ke fuskanta.

Ruwan da ke wurin ya ƙafe

Farfesa Motagh ya ƙara bayani da cewa: ''babban abin da ke kawo bushewar ƙasa a Iran shi ne rashin ɗorewar ruwan karkashin kasa fiye da kima wanda ke haifar da karancin kasa da kwararowar hamada.''

Idan aka tilasta fitar da ruwa daga karkashin kasa, kasar da abubuwan da ke rike ta sannu a hankali kasar na nutsewa. Mummunan fari da tsananin zafin da ake fama da shi na kara munanan lamarin ta yadda ruwanb ke kara kafewa. Kuma Iran na cikin kasashen da suke rasa ruywa cikin sauri a fadin duniya.

Sama da gwamman shekaru, Iran ta yi amfani da ruwa fiye da wanda ake da shi, inda ta kje kanface ruwan tafkuna da koguna, da ma'adinar ruwa.

Tun a shekarar 1970, aka kwashe albarkatun ruwan Iran. Sama da kashi 70 cikin 100 na ruwan da ake adanawa sun kafe, kamar yadda wani bincike ya bayyana.

"Yawancin bincike da nazari da aka gudanar sun bayyana Iran a matsayin sahun gaba a inda ake samun kafewar ruwa," inji Andrew Pearson, na cibiyar binciken albarkatun ruwa ta International Groundwater Resources Assessment Centre (IGRAC).

"Kusan kashi 90 cikin 100 na ruwan da akai amfani da shi a Iranm a fannin noma ne, yawan amfanin da shi da kuma matsalar fari da ake fama da shi ya kara janyo matsalkar kafewar koguna."

Ta yaya yawan hakar ruwan karkashin kasa ke shafar nutsewar kasa? 1. Ana fitar da ruwan karkashin kasa 2. An danne kasa kuma ta nutse

Sai dai illar ta wuce yadda ake tsdammani a wuraren tarihi.

Wani bincike na kasa da aka gudanar a baya-bayan nan ya gano kusan murabba'in kilomita 56,000 na Iran, wato kashi 3.5 na kasar ana shuka nau'in cimaka.

A wasu yankunan birnin Tehran kuwa sun nutse da kusan santi mita 25 a kowace shekara a cikin 'yan shekarun nan. A Rafsanjan, yanki mai cike da manyan gonakin gyada nau'in pistachio, an kiyasta an rasa kimanin mita 300 na ruwa na karkashin kasa saboda yawan hakowa.

Kuma yayin da kasa ke nutsewa, tituna, da magudanar ruwa, da bututun mai suna karkacewa, suna haifar da matsalolin da ke shafar ayyukan ababen more rayuwa da aka kashe makudan kudade wajen yin su.

Tsararren daben da aka kawata masallacin da launukan sararin samaniya da ruwan dorawa da fararen furanni sun nuna alamu tsattsagewa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masallatan wuraren tarihi na duniya na Isfahan sun nuna alamun bazuwar ƙasa

Matsalar a Iran kaɗai take?

Halin da ake ciki a Iran ya musanana amma ba wai ita ce kadai ba. Shi ma birnin Mexico, da Jakarta na Induniysa, tsakiyar California ana samun nutsewar kasa da akalla mita 100 a kowacce shekara.

Abin da ya sa Iran ta zama sahun gaba shi ne, kasancewar mashahuran wuraren tarihi na Unesco da ke cikin hadari.

Farfesa Pietro Teatini na Jami'ar Padova ya ce "Saboda yanayin kasa, sau da yawa sauyin kasa a Iran na faruwa ne saboda tsagewar zurfin mita daya yawa tare da mummunar barna kan ababen more rayuwa."

Akwai kasashen yankin gabas ta tsakiya da ke fama da kafewar ruwa kamar Saudiyya da Isra'ila da yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Sai kuma yankunan arewacin Afurka musamman kasar Masar na cikin wuraren da ke fama da matsala a duniya.

Unesco ta shirya tarurruka da ta gayyato kwararru a fannin kimiyya da fasaha, da wakilan gwamnati a kasashe irin su Indunisiyya da Vietnam kuma tana shirin yin hakan a kasar Philippines, amma yanayin siyasar kasar Iran na neman katange Unesco daga yin irin wannan taron.

Alkinta hanyoyin samar da ruwa

Mai magana da yawun Unesco ya shaidawa BBC cewa an koyi darasi daga abin da ya faru a kasashen Sifaniya da Mexico da China da Indunisiya, kan da zarar an fara fuskantar matsala irin wannan, da matakan da za a dauka dan magance hakan musamman a kasa kamar Iran.

Kwararru sun amince ana bukatar daukar matakin alkinta ruwan karkashin kasa. Amma sun yi gargadin rikita-rikitar siyasa da matsalolin cikiun gida da yadda kasar ta dogara kacokam ga fannin noma.

"Abin da ya kamata ayi anan shi ne haɗa ilimin kimiyyar ƙasa da alkinta kayan tarihi ya kamata a yi," in ji Farfesa Motagh, "amma ba kai tsaye ba, dole sai an yi aikin kuma haɗin gwiwa tare da cibiyoyin Iran da ake fuskantar manyan ƙalubalai."

Kayatacciyar matattakalar hawa ginin masarautar Persepolis, da akai wa sassaken masu gadin fada.

Asalin hoton, LightRocket via Getty Images

Bayanan hoto, Kwararru na fatan Iran za ta samar da wata hanya da za ta alkinta ruwa da wuraren tarihin da ta ke da su

Iran ta sha alkwashin rage yawan ruwan da ake amfani da shi a kasar da cubic biliyan 45 cikin shekaru bakwai, ta sake amfani da shi domin inganta noman rani.

Sai dai hakan ya fuskanci tangarda, sakamakon takunkuman da kasashen yamma suka kakabawa kasar.

A watan Agustan bana, BBC ta tambayi ma'aikatar harkokin wajen Iran, da ofishin jakadancin Iran a Landan, da karamin ofishin diflmasiyyarta domin martani kan shirin kasar na alkinta hanyoyin samun ruwa, amma ba su maido sakon Imel ko takartdsar da muka aike ofishin diflomasiyyar.

Matakan da ake dauka a sassan duniya na alkinta ruwa, ka iya haskawa Iran fitilar yadda za ta adana ruwan da kuma ababen tarihinta.

A shekarun 1980, wasu yankunan birnin Bangkok na kasar Thailand sun nutse da mita 120 a kowacce shekara. Amma bayan gwamnati ta gabatar da tsarin takaita yawan ruwan da za a hako, da sanya kudi da kuma sanya ido, da alkinta ruwan da suke da shi na karkashin kasa. Hukumar da ta ke sa ido kan yadda aikin ke gudana, inda ruwan ya karu daga a yankuna da dama cikin shekarar.

"Abin fa ba wai rufa ido ba ne, abin da ake bukata kawai shi ne samar da manufofin da za a yi aiki da su," inji Mr Pearson.