Me ya sa gwamnatin Najeriya ta ce za ta sayar da shinkafa mai rahusa?

Asalin hoton, @PBATMediaCentre
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta karya farashin shinkafa wadda ta tanada da za a sayar a sassan kasar da nufin samar da sauƙi ga ƴan kasa.
A kasuwa dai ana sayar da buhun shinkafar ne kusan naira 80,000, ɗaya daga cikin dalilan da suka sa wasu ƴan Najeriya ke shirin gudanar da zanga-zanga domin nuna fushinsu da tsadar rayuwa.
Amma Gwamnatin tarayya ta ce za ta karya farashin shinkafar zuwa naira 40,000 kan duk buhu ɗaya mai nauyin kilogiram 50, kamar yadda ministan yada labarai na kasar Muhammad Idris ya shaida wa BBC.
Ya ce tuni aka ware wuraren da za a sayar da shinkafar a sassan jihohin Najeriya. Sai dai gwamnatin ba ta bayyana lokacin da za ta fara sayar da shinkafar mai sauƙin kuɗi ba.
Amma a cewar ministan, karya farashin na zuwa bayan gwamnatin tarayya ta bayar da tirelar shinkafa 20 ga duk jihohin ƙasar domin raba wa ƴan Najeriya.
"Da farko an bai wa gwamnoni shinkafa su raba wa masu ƙaramin ƙarfi kyauta kuma yanzu gwamnati ta tanadi shinkafa da za ta sayar da rahusa domin samar da sauƙi ga ƴan Najeriya," in ji ministan.
Ya ce shinkafar da za a sayar a farashi mai rahusa ba wadda gwamnatin tarayya ta raba wa gwamnonin jihohi ba ce.
Shinkafa na ɗaya daga cikin abincin da ake ci a Najeriya, kuma farashinta a kasuwa kusan ya gagari aljihun wasu ƴan ƙasar.
Ministan ya ce gwamnati ta lura da tsadar shinkafar a kasuwa, shi ne ya sa ta ɗauki matakin samar da ita a farashi mai rahusa domin ƴan ƙasa su amfana
Kuma a cewarsa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.
"Idan aka ci gaba da kawo matakai irin waɗannan, sannu a hankali abubuwa za su yi sauƙi."
Yadda rabon kayan abinci ke haifar da yamutsi a Najeriya
Sai dai sau da yawa rabon kayan abinci a Najeriya bai cika yin nasara ba, sannan kuma ana yawan samun hargitsin da a wasu lokutan kan haifar da rasa rayuka.
A watan Fabararun da ya gabata, an samu rasa rayuka a Legas, lokacin da aka samu turmutsutsun mutane a wurin sayar da shinkafar da hukumar hana fasa-ƙwauri ta ƙasar ta ƙwace.
Mutanen da suka yi tururuwa domin sayen shinkafar da ake sayarwa kan naira 10,000 kan rabin buhu sun ja dogon layi a cibiyar da aka tanada, sai dai jim kaɗan bayan haka aka samu turmutsutsun da ya haifar da asarar rayuka.
A cikin watan Maris na shekarar ta 2024 ma an samu wani turmutsutsun mutane a jihar Bauchi da ke arwacin ƙasar ta Najeriya, lokacin da wani ɗan kasuwa ke raba kayan abinci a matsayin zakka.
Ƴansanda sun bayyana cewa mutum bakwai ne suka mutu a sanadiyyar turmutsutsun.
Ina za a sayi shinkafar
Gwamnatin tarayya ta ce ta kafa kwamitoci a jihohin ƙasar da za su kula da tsarin sayar da shinkafar.
Ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce an tanadi cibiyoyi a jihohin ƙasar da za a sayar da shinkafar.
"An tanadi jami'an tsaro da za su sanya ido domin tabbatar da cewa ba a sayar da shinkafar fiye da farashin da gwamnati ta ƙayyade ba."
"Kuma ana son waɗanda suka fi kowa buƙatar shinkafar ne za a sayar mawa idan har suna da halin da za su saya - kuma an dauki mataki na tabbatar da ba ta shiga hannun ɓata-gari ba," in ji shi.
Sai dai duk da wannan albishir na gwamnatin tarayya, har yanzu wasu ƴan ƙasar na cewa gwamnonin jihohi ba su fara rabon shinkafar da gwamnatin ta yi ikirarin ta ba su ba.
Lallashin masu zanga-zanga?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan da matasan ƙasar ta Najeriya suka ƙuduri aniyar yin zanga-zanga domin nuna fushi kan matsin rayuwa gwamnatin ta Najeriya ke ɗaukan wasu matakai da ake ganin tamkar na lallashin matasan ne.
Wannan ma wani abu ne da ya yi kama da hakan.
A duk ganawar da shugaban ƙasar ya yi da manyan masu faɗa a ji na ƙasar, babban saƙon da yake aikawa ga matasan shi ne 'a yi haƙuri, gwamnati za ta ɗauki matakin sauƙaƙa wa al'umma tsadar rayuwa."
Yanzu haka dai tashin farashin kayan masarufi ya sanya da dama daga cikin al'ummar ƙasar na cikin halin matsi.
Da dama daga cikin mutane, musamman a yankunan karkara na cewa ba su iya samun cin abinci sau uku a rana.
Rahoton hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ya ce hauhawar farashi a ƙasar ta ƙaru zuwa kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin 2024.
Kuma tsawon wata 18 ke nan a jere ana samun hauhawar farashi a Najeriyar, duk da matakan da hukumomin ƙasar ke ɗauka.
Hauhawar ta fi shafar kayan abinci inda sabbin alƙalumman na hukuma suka ce ya kai kashi 40.87 a watan Yunin 2024 idan aka kwatanta da Yunin 2023 inda aka samu ƙaruwar kaso 15.6.










