Yara miliyan 4.4 na fama da yunwa a Arewacin Najeriya

Ummi marainiya ce Katsina
Bayanan hoto, Ƙanwar mahaifin marainiya Ummi da ke riƙonta na shan wahala wajen shayar da ita
    • Marubuci, Madina Maishanu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Katsina
  • Lokacin karatu: Minti 8

"A ranakun da nake samu na ƙoshi, yarana suna ƙoshi, amma a ranakun da ban samu abinci ba, za su yi ta tsotso, sai su fara kuka saboda yunwa," a cewar Murja, ‘yar jihar Katsina wadda ke da yara biyu da take ƙoƙarin shayarwa.

Murja na rayuwa ne a wani ƙauye da ke kusa da birnin Katsina a Arewacin Najeriya. A kwanakin baya ne ta fara riƙon Ummi 'yar wata bakwai, Ummi ‘yar yayanta ce wadda mahaifiyarta ta rasu. Tun lokacin da ta fara riƙon Ummi, Murja da yaranta biyu ke fama da wahala. Murja ta ce a da babbar ‘yarta na koyon tafiya amma saboda yunwa yanzu ta ma daina gwadawa.

Babu wutar lantarki a ƙauyen da Murja ke rayuwa, inda gidansu, wanda aka gina da ƙasa ke a tsakiyar daji. Babu isassun hanyoyin da iska za ta ratsa, lamarin da ke janyo zafi sosai a gidan. Murja na cin abinci sau ɗaya a rana, abin da ya sa ba ta iya samar da isasshen ruwan nono.

“Ina jin ciwo idan na ga kowane yaro na yin kumari, ya yi jiki, amma ita sai tsumburewa take yi, dalilin da ya sa na kawo ta nan ke nan,” a cewar Murja.

Ummi and her aunt Murja and cousin Ummi da mai riƙonta Murja da 'yar Murja
Bayanan hoto, Akan yi fama da ƙarancin abin ci a lokacin da ake hada-hadar noma, kuma a wannan shekarar lokacin ya zagayo da wuri

Matsanancin ƙarancin abinci mai gina jiki

Mummunar matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ta yi ƙamari a jihohi shida na Arewacin Najeriya, wani lamari mai matuƙar tayar da hankali, inda matsalar ta shafi yara ‘yan ƙasa da shekara biyar miliyan 4.4 da mata masu juna biyu kusan 600,000, a cewar Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP).

Matsalar na ci gaba da yaɗuwa cikin sauri: Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce adadin yaran da ke fama da matsalar ya ninka fiye da sau biyu idan aka kwatanta da bara.

Locator map six N Nigeria
Bayanan hoto, Yara miliyan 4.4 ne ke fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a jihohi shida na arewacin Najeriya

Daraktar kula da harkokin lafiya a Ƙungiyar Likitoci masu Bayar da Agaji ta MSF, Catherine Van Overloop ta ce a wasu wuraren a arewacin Najeriya, adadin ya ninka kusan sau biyu.

“Akwai yiwuwar yaran za su fuskanci matsalolin da suka shafi girmansu da fahimtarsu yayin da suke tasowa,” in ji ta, a lokacin da take faɗin irin illolin da za su iya shafar yaran.

“Za su iya fuskantar cikas wajen girma, akwai kuma yiwuwar cewa ƙwaƙwalwarsu ba za ta ginu yadda ya kamata ba; hakan zai haifar masu da matsaloli wajen neman ilimi. Kuma wadannan yara su ne makomar Najeriya.”

Murja and her two daughters Murja da yaranta biyu
Bayanan hoto, Shekaru da dama na rashin tsaro a Arewa na daga cikin manyan dalilan wannan matsalar

Me ya janyo matsalar?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Najeriya na fuskantar matsalar ƙarancin abinci a duk faɗin ƙasar. A tsakanin watan Oktoba zuwa Disamban 2023 an tabbatar cewa mutum miliyan 25 ba sa samun isashen abinci. Wannan adadin ya haura zuwa miliyan 32 a tsakanin watannin Yuni zuwa Agustan 2024, kamar yadda alƙaluman WFP suka nuna.

Amma matsalar ta fi ƙamari a Arewacin Najeriya. Matsalar tsaro da tashe-tashen hankula na daga cikin manyan abubuwan da suka fi ta’azzara matsalar yunwa a yankin.

Yankin arewa maso gabashin ƙasar ya kasance cibiyar rikice-rikicen ƙungiyar Boko Haram tsawon sama da shekara 10, waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyar ISIS. Boko Haram ta yi sanadin kashewa da kuma sace dubban mutane, ta kuma tilasta wa miliyoyi barin gidajensu domin neman mafaka a wasu yankunan Najeriya, da kuma makwaftanta, Nijar, Chadi da Kamaru.

Yayin da jami’an tsaron Najeriya suka mayar da hankali kan Boko Haram, rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya da aka shafe shekaru ana fama da su, sun ƙara janyo rashin zaman lafiya a yankin.

A cikin shekaru takwas da suka wuce, ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da aka fi kira da ’yan fashin daji na satar mutane don neman ƙudin fansa, tare da kashewa da kuma yi wa wasu fyade. Wannan ta’addancin ya tilasta wa dubban mutane – musamman namoma da makiyaya barin gonakinsu.

Sauyin yanayi ya ƙara ta’azzara matsalar ƙarancin abinci yayin da yanayin zafi ke lalata amfanin gona.

A wannan shekarar, lokacin da ake fama da ƙarancin abinci ya zo da wuri kuma manoma sun ce yanayin bana shi ne mafi muni da suka gani a cikin shekara bakwai.

Najeriya na kuma fuskantar hauhawar farashi, wanda ke ƙara janyo tsadar farashin kayan masarufi kamar abinci da man fetur, lamarin da ke janyo tsadar rayuwa mai tsanani.

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

Matsalar za ta yi illa ga Yammacin Afrika?

Matsalar tsaro da ƙarancin isashen abincin da ake fuskanta a Arewacin Najeriya za ta iya yin illa ga ƙasashen da ke makwaftaka da ita a Yammacin Afrika, a cewar masana.

“Matsalar za ta iya janyo a fuskanci ƙarancin abinci a sauran ƙasashen da ke Yammacin Afrika, wanda hakan zai janyo ƙarin mutanen da za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki, da ƙaruwar ‘yan gudun hijira da kuma yiwuwar ƙara tabarbarewar matsalar tsaron da ake fuskanta a yankin, a cewar babban mai yin sharhi a bangaren da ke lura da tsattsauran ra’ayi na Cibiyar Tony Blair, Bulama Bukarti.

“Hakan zai tilasta wa ƙungiyoyin bayar da agaji karkata ‘yan ƙudaden da suke kashewa zuwa kan matsalar, lamarin da zai iya yin illa ga agajin da suke bayarwa kan wasu matsalolin, kamar rikice-rikice da ɓangaren lafiya, wanda hakan zai shafi zaman lafiya na yankin,“ in ji shi.

Ƙungiyoyin bayar da agaji kamar Médecins Sans Frontières (MSF) sun yi gargaɗin cewa babu kuɗaɗen da ake buƙata domin magance wannan gagarumar matsalar.

“Mun sha nanata wa Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran masu tallafawa kan yadda matsalar harkar jin ƙai ke ƙara tabarbarewa a arewa maso yammacin ƙasar,” a cewar Ahmed Bilal, shugaban shirin na MSF a yankin.

A bisa tilas, Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, Unicef ya rage yawan tallafin da yake bayarwa daga ƙananan hukumomi 23 zuwa ƙananan hukumomi 14 a jihar Katsina, duk da dai asusun na ci gaba da ƙoƙarin ganin ya samo wasu ƙarin kuɗaɗen.

Jamila

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto, Jamila ta kai ɗanta mai shekara biyu cibiyar MSF don ya samu lafiya

‘Yan bindiga sun ƙwace mana komai’

BBC ta sha bayar da rahotanni na irin ɓarnar da matsalolin tsaro ke yi a arewacin Najeriya.

“’Yan bindiga sun shiga gidana kuma sun ƙwace gonarmu,” a cewar Jamila, wata manomiya a wata cibiyar kula da yara masu fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki na MSF.

Kwanaki kaɗan da suka gabata, Jamila ta kai ɗanta Aliyu asibitin kula da yara masu fama da matsanancin ƙarancin abinci.

Ta ce jikinsa ya kumbura kuma asibitin gwamnatin da ta kai shi sun kasa yi masa magani.

“Ba mu da bambanci da mabarata a yanzu, ‘yan bindiga sun ƙwace komai. Rayuwata ta da ta fiye min ta yanzu, muna sayar da amfanin gonarmu kuma mu ci abinci daga abin da muka noma,” in ji ta.

A mafi yawan lokuta, Jamila mai ‘ya’ya uku kan dogara ne kan garin kwaki a matsayin abincinta na yau da kullum.

Kamar Jamila, yawancin mutanen da muka haɗu da su a Katsina manoma ne waɗanda ‘yan bindiga suka tilasta wa barin gonakinsu.

Mr Abubakar and his family
Bayanan hoto, Alhaji Abubakr ya kasance babban manomi a shekarun baya kafin matsalar tsaro ya tursasa masa tserewa daga kauyensu

“A da ina da abubuwa da yawa, ina noma masara da auduga kuma ina da dabbobi,” a cewar Alhaji Abubakar wanda ke zama tare da yaransa 23 da matansa uku a wata unguwar da ake amfani da ita a matsayin sansanin ‘yan gudun hijira amma ba a hukumance ba, bayan ‘yan bindiga sun kore shi daga inda yake noma.

Shi da iyalinsa na zama ne a wani ƙaramin gida da ke da ɗakin bahaya guda ɗaya, wanda bai da sirri sosai. Sau ɗaya kawai suke samun cin abinci a rana.

“Wanda ke bayar da abinci kyauta, yau ya zo ana ba shi, dole zuciyata ta buga,” in ji Alhaji Abubakar.

Wannan sansanin da yake zama mafaka ce ga ɗaruruwan ‘yan gudun hijirar da suka zo daga ƙauyuka daban da ke ciki da wajen Katsina. Yanayin rayuwa maras kyau a irin sansanonin nan sun janyo yaɗuwar cututtuka kamar Maleriya da Kwalara da Ƙyanda, a cewar Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Smiling Heart Initiative International.

“Ina ma a ce gwamnati za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaron da muke fuskanta saboda mu samu koma gonakinmu. Zan ji daɗi sosai idan hakan ta faru,” a cewar Alhaji Abubakar.

Mr Abubakar has 23 kids and three wives to support
Bayanan hoto, Alhaji Abubakar wanda ke da wadata sosai a baya, yanzu yana shan wahala wajen ciyar da yaransa 23 da mata uku

Kauce wa bala'i

Catherine Van Overloop ta kungiyar Médecins Sans Frontières ta ce: Domin kauce wa yaɗuwar wannan matsalar, dole gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa mutane sun samu abinci da wuraren rigakafi da kuma cibiyoyin kula da yara masu fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.

“Muna son a ƙara mayar da hankali kan wayar wa mutane kai kan muhimmancin rigakafi,” in ji ta. Ta ƙara da cewa samun tsaftattacen ruwa shi ma babban abu ne da ya kamata a duba don hana yaduwar cututtuka kamar gudawa da kyanda a tsakanin ƙananan yara.

Ta ce MSF ta fara tattaunawa da ma’aikatar lafiya ta Najeriya kuma an haɗa wata tawagar da za ta duba yadda za a magance waɗannan matsaloli.

Amma Mataimakin Gwamnan jihar Katsina, Faruk Lawal Jobe ya musanta cewa adadin masu fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki na ƙaruwa tsakanin yara ‘yan kasa da shekara biyar a jiharsa.

Ya ce alƙaluman da ƙungiyoyin bayar da agaji suka fitar ba sahihai ba ne kuma ya jaddada cewa gwamnatinsu na bakin ƙoƙarinta domin magance rashin isasshen abinci da kuma ta matsalar tsaro a Katsina.

“Mun fara sayo hatsi, wanda za mu sayar cikin farashi mai rahusa, wasu kuma za mu raba kyauta. A karon farko, cikin kwanakin baya mun kai samame tare da haɗin gwiwar dukannin rundunonin tsaro na Najeriya. A samamen mun samu nasarar tarwatsa maɓoyar ‘yan bindigar domin bai wa mutane damar komawa gonakinsu,” in ji shi.

Rundunar sojin Najeriya kuma ta ce ta ƙara azama wajen yaƙi da ƙungiyoyin ‘yan bindiga.

“Mun sauya salon yaƙin da muke yi da ‘yan bindigar nan, domin manomanmu su samu komawa gonakinsu kuma a magance matsalar rashin isashen abinci,” a cewar wani mai magana da yawun rundunar, Group Captain Ibrahim Ali Bukar.

“Ba za mu iya bayyana matakan da za mu ɗauka ba saboda dalilai na tsaro amma nan ba da daɗewa ba za a ga sauyi”.

Amma ga yara da ke fuskantar yunwa, kamar Ummi, wannan sauyin zai iya zuwa a ƙurarren lokaci, Murja ta ce tana jin kamar ba ta da kowa da zai taimaka mata a yanzu.

“Babban burina a rayuwa shi ne yarana mata biyu su girma cikin ƙoshin lafiya kuma su zama masu sa’a a rayuwa.”