‘Yadda yajin aiki ya sa ni koyarwa kyauta a makarantar sakandaren garinmu’

.

Asalin hoton, Muhammad Bala Garba

Yajin aikin ƙungiyar malaman jami'o'i ta ASUU a Najeriya ya tilasta wa wani ɗailibin jami'a mai suna Muhammad Bala Garba koyarwa kyauta a ƙananan makarantun sakandiren unguwarsu har guda biyu.

Dalibin ya bayyana haka ne a yayin wata hira da BBC a shirin da muke yi na musamman game da abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a gabanin zaben Najeriya na 2023.

Muhammad, wanda ke ajin ƙarshe a Jami’ar Maiduguri inda yake karanta fannin nazarin kiwon lafiya (Health Education), ya ce ya rungumi koyarwa ne domin dama tuni ya saba da ita tun lokacin da yake koyon sanin makamar aiki a shekarar 2018, kuma tun a wancan lokacin ne ya saba da ɗaliban.

Kasancewar ƙungiyar ASUU tana yajin aiki sai ya ga ya kamata ya koma makaranta ya riƙa koya wa ɗalibai karatu kyauta.

Muhammad Bala Garba, wanda ke zaune a unguwar Hausari/Zango a birnin Maiduguri, ya ce yana koyarwa a makarantu guda biyu da suka haɗa da Mala Kachalla Model Junior Secondary School, da Mafoni Junior Day Secondary School, ko da yake daga baya ya ce ya daina koyarwa a makarantar Mafoni sakamakon wasu dalilai.

.

Asalin hoton, Muhammad Bala Garba

Bayanan hoto, Wasu daga cikin ɗaliban Muhammad Bala Garba

Ya kara da cewa a lokacin da aka tsunduma yajin aikin ASUU, akwai wasu makarantu masu zaman kansu guda uku da suka nemi da ya je ya riƙa koyarwa a can domin su riƙa biyansa, amma kuma sai ya ƙi saboda a cewarsa ya riga ya saba da waɗancan makarantu don haka ba zai iya tafiya wasu makarantun ya bar waɗancan ba.

Dalibin ya ce akwai wani abokinsa da ya taɓa ce masa me ya sa ba zai tafi makaratun da suke nemansa domin su biya shi kuɗi ba?

Sai shi kuma ya ce masa haƙiƙa ba zai iya tafiya domin kuwa su waɗancan makarantu ko ''ban je ba za su iya ɗaukar wani malamin ya je ya koyar domin su biya shi''.

Amma a ganinsa a waɗanan makarantun da ya saba idan ya daina zuwa wa zai zo ya koya wa ɗimbin ɗaliban da suka saba da shi.

'Ina jin daɗi yadda ɗalibaina suka rungumi karatu'

.

Asalin hoton, Muhammad Bala Garba

Bayanan hoto, Malam Muhammad Bala Garba da wasu daga cikin ɗaliban ajinsa

Ya ce yana jin daɗi da farin cikin abin da yake yi saboda yadda ɗalibansa suka rungumi ɗabi'ar karatu sosai.

“Na taɓa haɗuwa da wata ɗalibata a kasuwa tana karanta abin da nake koya musu a aji, kuma haƙiƙa na ji daɗin wannan abu,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

Ya ce ɗaya daga cikin makarantun da yake zuwan shugabar makarantar ce ta roƙe shi da ya je ya riƙa koyar da ɗaliban, ɗaya makarantar kuma ɗaliban makarantar ne da kansu suke roƙonsa da ya je ya koya musu karatu sakamakon sabawa da suka yi da shi

'Har muƙamin fom masta na samu saboda jajircewa'

.

Asalin hoton, Muhammad Bala Garba

Bayanan hoto, Muhammad Bala Garba a lokacin da yake duba aikin ɗalibansa a ofishinsa

Muhammad Bala Garba ya ce a yanzu haka yana duba jarrabawar da shi kansa ya shirya wa ɗaliban.

Ɗalibin ya ce ya fa'idantu da abubuwa da dama daga koyarwa da yake yi a makarantun guda biyu da suka haɗar da samun horon sanin makamar aiki.

Ya shaida wa BBC cewa ''yanzu maganar da nake da kai a yanzu na samu muƙamin fom masta a makarantar saboda jajircewarta''

'Malam ba ya gajiya da koyarwa'

.

Asalin hoton, Muhammad Bala Garba

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasu daga cikin ɗaliban da malamin ke koyarwa sun shaida wa BBC cewa Malamin ya daɗe yana koya musu karatu tun suna ajin farko na ƙaramar sakandire har a yanzu da suke aji na biyu ko na ƙarshe.

Ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Aisha Abdullahi wadda a yanzu ke ajin ƙarshe na ƙaramar sakandiren 'Mala Kachall Model Junior Secondary School' ta ce ''daga cikin abubuwan da malam ke koya mana akwai alamomin rubutu, da insha'i da sana'o'in Hausawa da sauransu''.

Shi ma wani ɗalibin mai suna Muhammad Mustapha Sheriff wanda ke aji biyu a makarantar ya ce malamin nasu baya gajiya domin in ya koya maka abu ba ka gane ba zai sake koya maka shi har sai ka fahimce shi.

Ya ci gaba da cewa malamin nasu kan yi amfani da harsunan Turanci da Hausa da Kanuri domin ya tabbatar da cewa dalibai sun fahimci karatun da yake koya musu.

Muhammad Mustapha Sheriff ya ce a ''kullum malamin namu na gaya mana cewa ''Kar mu yi wasa da karatu kuma kullum mu riƙa zuwa makaranta''.

Har yanzu ina zuwa koyarwa

.

Asalin hoton, Muhammad Bala Garba

Malam Muhammad Bala Garba ya ce har a yanzu da aka janye yajin aikin ASUU ya ci gaba da zuwa makarantar da yake koyarwa domin aikinsa, kasancewar ya saba da aikin.

Ya kuma tabbatar wa BBC cewa ko bayan kammala karatunsa na jami'a zai ci gaba da zuwa koyarwar har zuwa lokacin da Allah zai ɓullo masa da aikin yi.