Ko sayar wa 'yan canji dala zai iya farfaɗo da darajar naira?

Daga Aisha Bappa, BBC Hausa

A makon nan ne Babban Bankin Najeriya CBN ya sanar da cigaba da sayar wa 'yan kasuwar canji dalar Amurka a yunƙurinsa na daƙile faɗuwar darajar naira.

Matakin sauyi ne gagarumi da CBN ya ɗauka bayan ya daina sayar musu da dalar a baya, yana mai zargin su da tsawwala farashi a kasuwar bayan fage da kuma taimaka wa masu halasta kuɗin haram.

Faɗuwar da darajar nairar ta dinga yi a makonnin da suka wuce ta jawo ɗaukar matakai daban-daban, ciki har da kama 'yan kasuwar canjin da jami'an tsaro suka yi a manyan birane kamar Kano, da Abuja, da Legas.

'Yan kasuwar sun faɗa wa BBC cewa hakan ta sa suka rufe shagunansu a ƙarshen watan Janairu.

'Matakin zai taimaka wa naira'

A jiya Litinin ne CBN ya fitar da wata sanarwa, inda ya ce ya sayar wa kowanne kamfanin canji dala 10,000 kan farashin N1,251 bisa sharaɗin cewa ba za su ci ribar da ta wuce kashi 1.5 ba idan za su siyar.

Sai dai babban bankin ya yi barazanar ɗaukar mataki kan duk ɗan canjin da ya saɓa ƙa'idar, ciki har da dakatar da sayar masa da dalar.

Kazalika, ya umarci 'yan kasuwar da ke da lasisi su sanya nairar a wasu asusun bankin da ya ware kafin yammacin ranar Alhamis 28 ga watan Maris na 2024, sannan kuma su miƙa takardar shaidar biyan kuɗin da sauran takardun da suka dace kafin su samu dalar.

Masana da kuma masu hada-hadar kuɗaden waje a Najeriya na ganin matakin na CBN zai taimaka wajen farfado da darajar naira.

Bashir Abdullahi Achida, masanin tattalin arziki ne, ya shaida wa BBC cewa matakin na CBN zai taimaka matuka gaya wajen farfaɗo da darajar naira da kuma rage hauhawar farashin kayayyakin da ake fama da shi a ƙasar.

"Ɗaya daga cikin abubuwan da ke janyo hauhawar farashin kaya a Najeriya shi ne tashin farashin dala, saboda mafi yawan abubuwan da ake amfani da su a ƙasar shigowa da su ake yi," in ji shi.

Bayan shigowa da kaya da 'yan kasuwa ke yi cikin Najeriyar, kuɗin fiton da ake biya na kayan ma yawanci da dala ake biya, abin da wani lokacin ke sa 'yan kasuwa kara farashin kaya ke nan, a cewarsa.

Bugu da ƙari, wasu 'yan kasuwar canji da abin ya shafa sun shaida wa BBC cewa matakin zai taimaka wajen farfaɗo da darajar naira.

"A yanzu muna ta ƙoƙari wajen ganin mun cika sharuɗɗan karɓar dalar daga CBN, idan muka kammala muka karɓa, za mu sayar da ita kamar yadda bankin ya ce, ma'ana mu ƙara kashi 1.5 kan abin da muka siya," a cewar Aminu Gwadabe shugaban 'yan canji na Najeriya.

Ya ƙara da cewa sun i daɗin matakan kuma "ina ganin hakan zai taimaka a samu sauƙin abubuwa da dama a Najeriya ciki har da farfaɗowar darajar naira".

"Ribar da za mu samu naira 18 ne kawai, domin mun saye ta kan N1,251 za mu sayar kan N1,268.76."

Ƙa'idojin da ɗan canji zai cika kafin ya karɓi dala

Babban Bankin Najeriya CBN ya shimfida ƙa'idoji da ya kamata duk ɗan canji ya cika kafin a bashi dala. Ƙa'idoji sun hadar da:

  • Dole sai canjin yana da cikakkun takardu na lasisi
  • Dole sai mai sayen dala ya bayar da wasu bayanansa ga ɗan canjin da zai sayi dalar a hannunsa; kamar lambar BVN, da fasfo, don ɗan canjin ya shigar da bayanan nasa ga CBN
  • 3.Dala dubu hudu ce ƙa'idar kuɗin da ɗan canji zai siyar wa mutum guda, ma'ana kada a zarta ƙa'idar dala hudu ga duk wani mai siyan dala
  • Dole mai sayan dala ya tura wani ɓangare na kuɗin da zai sayi dala ta asusun ɗan canji
  • Tura rahoton kullum a kan dalar da ɗan canji ya sayar, da kuma wadanda ya sayar wa ga CBN

Aminu Gwadabe, ya ce su yanzu babban fatansu komai ya daidaita a bangaren kasuwar hada-hadar kudaden waje.

Dangane da batun ƙara farashin kuɗi a kan dalar da suka samu ba ta wajen CBN ba, ya ce shi a ganinsa bai kamata a ƙara kuɗi ba.

"Idan muna so komai ya daidaita a ƙasarmu kamar farfaɗo da darajar kuɗinmu da daƙile hauhawar farashin kayayyaki, dole sai mun yi abin da ya dace, mu dinga sayar da dala kan farashin gwamnati ko da kuwa farashin da aka siye ta ya fi na gwamnati."

Shugaban 'yan kasuwar canjin ya ce a shirye suke su ba wa gwamnati "duk wani goyon baya domin farfaɗo da darajar naira".

A watannin baya bayannan dai darajar naira na kara faɗuwa, abin da ƙwararru ke dangantawa da buƙatun kuɗaɗen ƙasashen waje musamman dalar Amurka, wadda ta yi ƙaranci a cibiyoyin da ke hada-hadar kuɗin a farashin hukuma da kuma masu shaci-fadin farashi.

Najeriya a halin yanzu na fuskantar taɓarɓarewar tattalin arziƙi mafi muni, wanda ke haifar da wahalhalu tare da fusata al'ummar ƙasar.