'Na zama tamkar mala'ikan mutuwa': jami'in da ya sanar da iyalai mutuwar ƴan uwansu

Rafael speaks into a microphone

Asalin hoton, Handout

Bayanan hoto, Rafael na zaune a Isra'ila tsawon shekara 20, yana kuma aiki da rundunar sojin ƙasar tun 2009.
    • Marubuci, Julia Braun
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, São Paulo

Dangin duka mutanen Isra'ila da suka mutu yayin farmakin soji ko hare-haren da gwamnatin ƙasar ta alaƙanta da ta'addanci, sun samu kulawa ta musamman, ciki har da ziyarar jami'an soji domin sanar da su mutuwa a hukumance.

Tun bayan harin da Hamas ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,400 a ƙasar, aka yi ta kiran jami'an tsaro daga rundunar sojin Isra'ila domin sanar da dangin mamatan a wani ɓangare na girmamawa ga mamatan.

Rafael - wanda asalinsa ɗan Brazil ne - wani babban jami'in soji ne, kuma yana ɗaya daga cikin sojojin da aka kira domin wannan aiki.

Tun a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba, yakan ziyarci a ƙalla gidaje uku domin sanar da su mutuwar 'yan uwansu.

"A lokacin da na ƙwanƙwasa ƙofar gidan dangin mamatan, nakan ji ni tamkar wani mala'ikan mutuwa," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"To amma na sani wani aiki ne mai muhimmanci, domin aiki ne na sanar da dangin haƙiƙanin abin da ya faru da 'yan uwansu, domin ba su damar shirya musu jana'iza."

Wannan ne karon farko da Rafael ke irin wanan aiki. Kasancewarsa ma'aikaci a rundunar sojin Isra'ila na kusan shekara 14, a baya jami'in na aiki ne a sashen shari'a na rundunar sojin Isra'ila.

"Akwai sojoji a rundunar da suka saba gudanar da irin wannan aiki, to amma kasancewar adadin mamatan na da yawa, ta sa dole wasu jami'an suka shigo cikin aikin, saboda sojojin da aka horas kan wannan aiki ba za su iya gudanar da aikin su kaɗai ba," in ji shi.

Jami'in ya ce an ba shi horon sa'a huɗu kafin ya fara wannan aiki.

"A horon da aka ba mu, an ce za mu shiga firgici musamman a kwanakin farko-farkon aikin namu, sakamakon gajiya da rashin bacci, kuma hakan ya faru, domin kuwa da kyar muke samun bacci da cin abinci," in ji shi.

"To amma na yi ta tilasta wa kaina cin abinci da ƙoƙarin yin bacci, saboda na san cewa idan ban yi aikin ba, to wasu iyalan ba za su samu labarin mutuwar 'yan uwansu ba."

Burned out cars line the road at a music festival which was attacked by Hamas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Motocin da suka ƙone tare da lalacewa sakamakon harin da Hamas ta kai Isra'ila a lokacin da matasa ke halartar bikin kiɗe-kiɗe
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rafael ya ce gidajen da kai musu labarin mutuwar danginsu ya razana shi, su ne gidajen da ke da ƙananan yara da matasa suka mutu a dangin.

Daya daga cikin gidajen, shi ne gidan da ya kai labarin mutuwar wata matashiya mai shekara 17.

Tana wata ziyara a gaɓar teku da ke kusa da Gaza domin kwana tare da saurayinta a lokacin da Hamas ta ƙaddamar musu da harin.

"A lokacin da na sanar da mahaifinta labarin mutuwarta, sai ya ce ai kuwa jiya ya ga hotonta a talbijin cikin mutanen da ake zargi Hamas ta yi garkuwa da su,", in ji Rafael.

"Sai ya ce min yana fatan 'yar tasa na cikin mutanen da aka yi garkuwa da su, don haka fatansa shi ne tana raye."

A wani gidan kuma, ya ziyarci iyayen wata mata mai shekara 30 da aka kashe a gidanta, tare da ɓacewar mijinta.

"Sun bar tagwayen jarirai 'yan wata 10, waɗanda iyayen suka sanya cikin ginin ƙarƙashin ƙasa da ke ɗakinsu kafin zuwan maharan," in ji shi.

"Aiki ne mai matuƙar wahala, ba zan iya daina tunanin halin da dangi suka shiga ba. Iyaye ne da ba za su sake ganin 'ya'yansu ba, 'ya'ya ne da za su tashi su rayu ba tare da iyayensu ba."

Major Rafael in uniform

Asalin hoton, Handout

Bayanan hoto, Rafael ya ce "Bacci na min wahala,"

Rafael ya ce da yawa daga cikin dangin wadanda suka mutu a harin 7 ga watan Octoba za su ɗauki kwanaki kafin su samu labari kan 'yan uwansu.

"Gano gawarwakin na da wahala, saboda wasunsu ba za a iya ganesu ba. saboda haka, akan ɗauki lokaci kafin a tabbatar da waɗanda suka mutu,' in ji shi.

"Akwai fiye da mutum 600 da ba a gani ba, kuma da yawa daga cikinsu sun mutu, to amma gano gawarwakin ba abu ne mai sauki ba."

Ana kallon harin na ranar 7 ga watan Oktoban, a matsayin mummunan harin kan iyaka da isra'ila ta taɓa fuskanta a shekarun nan.

Mambobin ƙungiyar Hamas sun ɓalle shingen da ya raba Gaza da Isra'ila a wurare masu yawa, tare da kai samame ƙauyuka da kashe aƙalla mutum 1,400. An kuma kiyasta cewa kimanin mutum 200 aka yi garkuwa da su.

Mayaƙan sun kuma jefa dubban rokoki daga Zirin Gaza, inda wasu daga ciki suka faɗa a biranen Tel Aviv da Birnin Kudus.

A burned-out house

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani gida da ya ƙone a unguwar Kibbutz Be'eri, kusa da Zirin Gaza, bayan harin Hamas

A martanin da ta mayar, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama kan Zirin Gaza kwanaki bayan harin. Mutanen da suka mutu a Gaza sakamakon hare-haren na Isra'ila ya kai mutum 1700 a ranar litinin (16, ga watan Oktoba).

Haka kuma, hukumomin Falasɗinawa sun ce kusan mutum 1,000 ɓaraguzan gine-gine suka danne su sakamkon hare-haren na Isra'ila.

A ƙarshen makon da ya gabata, rundunar sojin ƙasar ta bayyana cewa tana shirya sabbin hare-hare ta ruwa da ta ƙasa da kuma ta sama kafin shiga Gaza.

Isra'ila ta faɗa wa Falasɗinawa miliyan 1.1 da ke zaune a arewacin Gaza da su koma kudancin birnin domin kauce wa illar hare-haren nata.

Matsalolin jin-ƙai na ci gaba da ƙaruwa a yankin na Falasɗinawa, kuma akwai fargabar yaɗuwar rikicin zuwa wasu ƙasashen yankin, kamar Lebanon da Iran.

*BBC ta ɓoye sunan mahaifin sojan domin dalilai na tsaro.