Zargin cin naman mutane da bautar shaiɗan a zaɓen Brazil

Asalin hoton, Getty Images
Ikirari game da rashawa, annobar korona, lalata dazuka, cin naman mutane, da ma bautar shaiɗan sun ja hankula yayin da ake tsaka da kamfe a shirin zaɓen shugaban ƙasa na ƙasar Brazil a ranar Lahadi mai zuwa.
Shugaba Jair Bolsonaro na fuskantar ƙalubale daga tsohon Shugaban Ƙasa Luiz Inácio Lula a zagaye na biyu na zaɓen.
Mun duba ɓangarorin da 'yan takarar suka fi sukar juna a kai.
Zargin shaiɗanci da da cin naman ɗan Adam
Bolsonaro da Lula, waɗanda dukkansu mabiya ɗarikar Katolika ne, sun yi ta neman goyon bayan sauran Kiristoci waɗanda su ne kusan kashi ɗaya cikin uku na al'ummar ƙasar.
Sai dai kuma kamfe ɗin nasu cike yake da labaran ƙarya game da addini. Ɗaya daga ciikin misalai shi ne wani bidiyo da 'ya'yan Bolsanaro biyu suka wallafa a shafukan zumunta, inda wani mai tasiri da ya kira kansa Satanist (mai bin addinin shaiɗan) yana goyon bayan Lula.

Asalin hoton, Getty Images
Bidiyon ya karaɗe gari tare da saƙonnin da ke cewa Brazil za ta afka cikin "haɗarin addini" idan Lula ya yi nasara - duk da cewa mutumin ba shi da wata alaƙa da tsohon shugaban ko kuma manufofinsa.
Jama'ar Lula sun fitar da sanarwa suna musanta alaƙa da bautar shaiɗan sannan kotun zaɓe ta haramta yaɗa bidiyon.
Sai dai kuma kamfe ɗin nasu cike yake da labaran ƙarya game da addini. Ɗaya daga ciikin misalai shi ne wani bidiyo da 'ya'yan Bolsanaro biyu suka wallafa a shafukan zumunta, inda wani mai tasiri da ya kira kansa Satanist (mai bin addinin shaiɗan) yana goyon bayan Lula.
Bidiyon ya karaɗe gari tare da saƙonnin da ke cewa Brazil za ta afka cikin "haɗarin addini" idan Lula ya yi nasara - duk da cewa mutumin ba shi da wata alaƙa da tsohon shugaban ko kuma manufofinsa.
Jama'ar Lula sun fitar da sanarwa suna musanta alaƙa da bautar shaiɗan sannan kotun zaɓe ta haramta yaɗa bidiyon.

Asalin hoton, Ricardo Stuckert
A gefe guda kuma, kamfe ɗin Lula sun fito da wani bidiyo na Bolsonaro da ya yi hira da jaridar New Yrok Tmes, inda a ciki yake cewa ya kai ziyara wajen mazauna ƙasar da ake zargi suna dafa naman mutane kuma ma wai ya nemi ya gani.
A cewarsa a cikin hirar, idan yana so gani sai dai a ci naman da shi. "Zan ci," in ji shi. "Ba ni da wata idan na ci naman 'yan gargajiya." Amma ya ce muƙarrabansa ba sa son zuwa saboda haka shi ma bai je ba.
Kare dajin Amazon
Dajin na Amazon na taka muhimmiyar rawa wajen zuƙe iska mai guba wadda ka iya ratsawa cikin al'umma kuma kusan 60 cikin 100 na dajin yana cikin Brazil.
Dukkan 'yan takarar na ikirarin suna da tahiri mai kyau na ba shi kariya.
Yayin muhawara kai-tsaye a watan Oktoba, Lula ya ce: "A gwamnatinmu, [muna da] mafi ƙarancin lalacewar dajin Amazon, amma a taku gwamnatin kuna da mafi yawa."

Asalin hoton, Getty Images
Lalacewar dajin Amazon ta ƙaru a 'yan shekarun nan
Bolsanaro ya mayar da martani da: "Ku duba shafin Google na lalacewar dajin daga 2003 zuwa 2006 na shekara huɗu ta mulkin Lula. Sai kuma ku duba lalacewar dajin daga 2019 zuwa 2022'.
"Lokacin gwamnatinka, an lalata dajin ninki biyu na abin da aka lalata a mulkina," a cewarsa.
Gaskiya ne dajin da aka lalata a shekara ukun farko na mulkin Bolsanaro bai kai na irin waɗannan shekarun ba na mulkin Lula - kusan girman murabba'in kilomita 34,000 kenan idan aka kwatanta da kilomita 71,000, a cewar hukumar National Institute for Space Research (Inpe).
Sai dai lamarin ya ragu sosai bayan Lula ya shekara biyu a kan mulki, kuma ya zuwa lokacin da ya bar mulki a 2011 lalacewar ta ragu zuwa adadin da ba ta kaiwa ba.
Zargin rashawa da cin hanci
Bolsonaro ya bayyana zargin rashawa babba da aka gano a lokacin mulkin Lula na biliyoyin dala da aka sace da kuma ƙara farashi kan kwangilar man fetur da aka bayar ta hannun kamfanin mai na ƙasar Petrobras.
Shi kansa Lula an same shi da laifin hannu a cikin lamarin kuma aka ɗaure shi a gidan yari a 2017. An janye ɗaurin da aka yi masa a shekarar da ta gabata, abin da ya sa ya samu damar tsayawa a takarar.
A ɓangarensa, Lula ya sha zargin Bolsanaro da ingiza cin hanci da kuma zargin sa da kasa tafiyar da harkokin kuɗin ƙasar.
Game da haka, yana magan ne kan wani "kasafi kudi a asirce" da aka saka wa hannu a 2019, wanda hakan ya bai wa 'yan majalisa damar kashe kuɗi ba tare da an saka musu ido sosai ba.
Daƙile korona
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana zargin Bolsonaro da yaɗa labaran ƙarya kan rigakafin korona, kuma ya ƙi yarda a yi masa rigakafin shi kansa.
Lula ya sha zargin Bolsonaro da gazawa wajen daƙile cutar.
Ya bayyana adadin mutanen da suka mutu yana cewa: "Brazil na da yawan kashi 3 cikin 100 na yawan al'ummar duniya amma kuma tana da kashi 11 cikin 100 na yawan waɗanda annobar ta kashe."
Gaskiya ne Brazil ce ke da kusan 11 na waɗanda suka mutu da mutane sama da 687,000, a cewar Jami'ar Johns Hopkins.
Wannan ne adadi a hukumance na mutuwa na biyu mafi girma a duniya bayan Amurka.
Sai dai ba lallai ne alƙaluman hukuma su ba da ainahin adadin mtattun ba a dukkan ƙasashe saboda ba kodayaushe ake iya samun gwaji ba. Lula ya kuma soki tsawon lokacin da aka ɗauka kafin a fara yi wa mutane rigakafin cutar.
Da yake kare gwamnatinsa, Shugaba Bolsonaro ya ce: "Mun sayi fiye da miliyan 500 na rigakafin korona...kuma Brazil na cikin ƙasashen da aka fi yi wa rigakafi a duniya kuma cikin sauri."

Asalin hoton, Getty Images
Zuwa yanzu, gwamnatin Bolsonaro ta sayi allurai kusan miliyan 750, amma odar da ta yi ba ta ƙarasa ƙasar da wuri ba kamar sauran ƙasashe.
Brazil ta yi allurar sau 220 cikin duk mutum 100, amma duk da haka adadin bai kai na na wasu ƙasashe ba a yankin na Latin Amurka - kamar Argentina da Chile da Peru.











