Me ya sa manyan jam'iyyun siyasa ke rububin Wike?

Atiku, Wike, Kwankwaso, Tinubu da Obi

Asalin hoton, Others

Wata ɗasawa da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike na jam'iyyar PDP ya fara yi da wasu jam'iyyun siyasa a Najeriya na neman jefa jam'iyyarsa ta PDP cikin fargaba.

A ƴan kwanakin nan an ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi ya kai wa Mista Wike ziyara. 

An ga kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci gwamnan na Rivers.

Haka kuma wasu gwamnonin APC sun gana da Wike.

Jaridun Najeriya sun ce gwamnonin sun haɗa da gwamnan jihar Ekiti, shugaban ƙungiyar gwamnoni Dr. Kayode Fayemi tare da gwamnan Legas da kuma na Ondo.

Sai dai babu wani abu da ya fito na dalili da kuma sakamakon tattaunawar tsakanin Wike da gwamnonin na APC, amma ba ya rasa nasaba da zaɓen 2023.

Gwamna Wike yana da ƙarfin faɗa a ji a PDP, inda ya nemi takarar shugaban ƙasa a tutar jam'iyyar amma bai samu nasara ba.

Abin tambaya shi ne, ko Mista Wike zai iya fita daga jam'iyyar PDP?

Kuma me ya sa sauran manyan jam'iyyun ke zawarcinsa?

Me ya sa ake zawarcin Wike?

Gwamna Wike da Sanata Kwankwaso

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto, Gwamna Wike da Sanata Kwankwaso
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun shan kayen Gwamna Wike a zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, wasu jam'iyyun siyasa ke kai komo jiharsa har ta kai ga an fara raɗe-raɗin cewa wataƙila zawarcinsa suke yi.

Masana siyasa kamar Dakta Faruk BB Faruk na Jami'ar Abuja na ganin cewa za a iya zawarcin Mista Wike, saboda ba ƙyallen yadawa ba ne.

Ya ce Wike na da kuɗi kuma ya zamo gwarzo saboda yadda ya riƙe PDP lokacin da ba ta da gata bayan ta faɗi zaɓe.

Kuma a cewar masanin, jam'iyyun na neman samun goyon bayan kudu maso kudu saboda tasirin jihar Rivers a siyasar a yankin.

Kazalika wasu masu sharhin na ganin Wike na da kuɗi a hannunsa kuma yana da faɗa a ji a yankin kudu maso kudancin Najeriyar.

Zuwa yanzu Gwamna Wike bai ce zai sauya sheƙa daga PDP zuwa wata jam'iyya ba. Amma yadda ake zawarcinsa, masana na ganin komi na iya faruwa.

Kuma fitarsa daga PDP, a cewa Mallam Kabiru Sa'id Sufi malami a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta jihar Kano, za ta yi wa jam'iyyar PDP illa.

"Wike yana da ƙarfi a yankinsa, don haka ba ƙaramin giɓi ba ne ga PDP idan har ya fice," in ji Malam Sufi.

Duk da cewa wasu ƴan PDP na fargabar ficewar Mista Wike daga jam'iyyar, wasu kuma na da ra'ayin ko-gezau, kamar Mallam Shehu Yusuf Kura wanda ya ce PDP gidan gandu ce.

"Ko da Wike ko ba Wike ba zai hana Atiku cin zaɓe ba," in ji Kura.

Amfanin Wike ga sauran jam'iyyu

PDP tana ganin Wike jigo ne da zai iya kawo mata yankin kudu maso kudu, wanda hakan zai ƙara wa jam'iyyar tagomashi a ƙuri'un 2023.

Duk da cewa wanda Atiku ya ɗauka a matsayin mataimaki ɗan yankin ne, amma ana ganin bai kai Wike iko da faɗa a ji ba.

A ɓangaren Peter Obi kuwa, wataƙila yana ganin a yanzu da yake da tabbacin ƙuri'un kudu maso gabas a hannunsa, samun na kudu maso kudun na iya sanyawa ya yi zarra a zaɓen 2023.

Yayin da shi ma Sanato Kwankwaso yake hasoshen cewa idan har ya yi sa'ar samo kan Wike, to ƙuri'un kudu maso kudun za su taimaka wa fafutukarsa sosai.

APC ma a nata lissafin, yankin kudu maso kudun ne take ganin a yanzu ya rage mata da idan ta same shi sai ta yi hamdala.

Hakan dai na nuna cewa a yanzu Wike ya zama tamkar zinaren da kowa ke nema ruwa a jallo.

PDP na da yaƙinin Wike ba zai bar ta ba

Mafi yawan ƴan jam'iyyar PDP dai na da yakinin Gwamna Wike ba zai sauya-sheƙa daga jam'iyyar zuwa wata ba.

Amma ana ganin yana jan zarensa ne don ya tantance a wace jam'iyya ce zai samu makoma mai kyau bayan ya sauka daga gwamna a 2023.

Ana tunanin WIke na fargabar idan har ya sauka daga gwamna a 2023 ba tare da samun tudun dafawa ba, to za ta iya ƙare masa a siyasance.

A makwannin da suka gabata mai magana da yawunsa ya jaddada cewa tsakanin Wike da PDP irin soyayyar nan ce ta saɓar ƙafar kaza, wadda ƴan magana kan ce mutu ka-raba.

Amma masana sun ce siyasa ƴar lissafi ce tana iya sauyawa a kowane mataki.