China ta soma haramta wasu kayayyakin Taiwan a ƙasarta

..

Asalin hoton, Reuters

Zuwan da shugabar Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosy ta yi Taiwan na neman barin baya da ƙura domin kuwa tun kafin ta bar ƙasar, mai iƙirarin iko da ƙasar wato China ta soma maka wa Taiwan din takunkumi.

Yayin da ake kallon ziyarar da Nancy Pelosi ke yi a Taiwan a halin yanzu a matsayin wani ci gaba, ita kuwa China a wurinta Amurka ta kira ruwa ba laima, domin kuwa tun kafin Pelosi ta sauka ƙasar a ranar Talata,

sai da China ta yi gargaɗin cewa ziyarar tata za ta kawo cikas ga Taiwan ɗin da kuma yin mummunan tasiri kan dangantakar da ke tsakanin China da Amurka.

A halin yanzu dai China ta saka takunkumi kan wasu jerin kayayyakin da Taiwan ke samarwa inda China din ta haramta sayar da su a ƙasarta.

A Laraba neministan kasuwanci na China ya sanar da haramta sayar da wani nau'in lemo na Taiwan da wasu nau'ukan kifi da ƙasar ke shigarwa China da kuma toshe shigar da yashi zuwa tsibirin.

Bugu da ƙari har biskit-biskit da sauran kayan ƙwalama da Taiwan ɗin ke samarwa ba su tsira ba domin sai da China ɗin ta maka musu takunkumi tun a Talata.

Ziyarar Nancy Pelosi Taiwan ta kasance babban labari a duniya baki ɗaya domin kuwa ita ce jami'ar gwamnatin Amurka ta farko da ta kai ziyara tsibirin a shekaru 25 da suka gabata kuma ana ganin China za ta iya saka ƙafar wando ɗaya da duk wata ƙasa da za ta iya sa hannu ko kuma tallafa wa Taiwan ɗin domin ganin ta zama ƙasa mai cikakken ƴanci.

China dai na kallon Taiwan a matsayin wani lardi da ya ɓalle daga cikinta kuma tuni ta lashi takobin dawo da Taiwan ɗin cikinta inda ta ce za ta yi amfani da ƙarfin tuwo idan ta kama.

Sai dai masu jagorantar Taiwan ɗin tuni suka ce bakin alƙalami ya bushe inda suka ce Taiwan ta wuce a kira ta da lardi domin kuwa a cewarsu, ƙasa ce mai faɗa a ji kuma mai cikakken iko.