Newcastle na son James Trafford, Man United na son Branthwaite

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle ta yi wa Burnley tayin fam miliyan 16, kan mai tsaron ragar Ingila James Trafford mai shekara 21, sai dai su na bukatar fam miliyan 20. (Mail)
Ana sa ran Manchester United za ta kammala tattaunawa da mai tsaron gida na Everton Jarrad Branthwaite, kafin ranar 30 ga watan Yuni, bayan an cire shi daga tawagar Ingila a gasar Euro 2024. (Liverpool Echo)
A karo na biyu Red Devils sun shirya taya dan wasan tsakiya na Benfica Joao Neves, mai shekara 19, bayan gaza daidaitawa kan fam miliyan 51. (A Bola - in Portuguese)
Manchester City na son dan wasan gaba na Argentina Julian Alvarez, ya ci gaba da zama a kungiyar, ba kuma za su amince da duk wani tayi kan dan wasan mai shekara 21 ba. (Fabrizio Romano)
Atletico Madrid na son Alvarez, sai dai shugaban kungiyar Enrique Cerezo, ya ce har yanzu bai amince dan wasan gaban zai bar Etihad ba. (Standard)
Leicester City na tuntuba kan tsohon shugaban Brighton da Chelsea, Graham Potter, kan yiwuwar aiki tare. (Telegraph - subscription required)
Juventus ka iya yiwa dan wasan tsakiya na Amurka Weston McKennie, mai shekara 25, tayin musaya da dan wasan tsakiya na Brazil mai taka leda a Aston Villa Douglas Luiz, mai shekara 26. (Calciomercato - in Italian)
Ita ma kungiyar Arsenal na son dan wasan Luiz. (Rudy Galetti)
Bayern Munich na sake tuntubar dan wasan tsakiya na Portugal Fulham Joao Palhinha, mai shekara 28. (Talksport)











