Juyin mulkin da ya gwara kan manyan aminan juna biyu na Afirka

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Tun bayan hamɓarar da Shugaba Bazoum Mohamed daga mulki da sojoji suka yi a ranar Laraba 26 ga watan Yuli, dangantaka ta fara tsami tsakanin Nijar da babbar aminiyarta kuma maƙwabciyarta a yankin Afirka ta Yamma wato Najeriya.

A ranar Juma'ar nan, sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun sanya Najeriya a jerin ƙasashen da suka janye jakadansu.

Matakin ya zo ne bayan Najeriya ta katse wutar lantarki ga Nijar, da kuma rufe kan iyakarta mai tsawon fiye da kilomita 1,600 da babbar abokiyar ƙawancen tata.

Irin wannan mataki da ita ma Jamhuriyar Benin wadda Nijar ta dogara da tashoshin ruwanta wajen fiton kaya, sun haɗu sun sanya farashin kaya yin tashin gwauron zabi cikin 'yan kwanaki ƙalilan tare da tsunduma unguwannin Niamey, babban birnin Nijar da sauran biranen ƙasar cikin matsalar ƙarancin lantarki.

A ƙarshen makon da ya gabata ne kungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta Ecowas ko Cedeao - ƙarƙashin jagoranchin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu - ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulkin na Nijar wa'adin mako guda su mayar da shugaban Bazoum kan karagar mulki, ko su fuskanci matakin soji.

Haka kuma cikin makon da ya gabatan manyan hafsoshin tsaron kasashen ƙungiyar suka yi wani taro a Abuja babban birnin Najeriya da nufin tattauana matakan da ya kamata su ɗauka kan Nijar ɗin muddin ta kasa cika umarnin ƙungiyar ta Ecowas.

To sai dai a nasu ɓangare sojojin da suka gudanar da juyin mulkin sun yi gargadin cewa a shirye suke su mayar da martani matuƙar kungiyar Ecowas - wadda shugaban Najeriya ke jagoranta ta kai wa ƙasar hari ta wane fuska.

'Amincin da ke tsakanin Najeriya da Nijar'

Najeriya da Nijar sun kasance tamkar 'yan uwan juna ta fuskar dangantaka, domin kuwa tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka yankin yammacin Afirka, ƙasashen biyu ke hulda da juna ta fuskar auratayya da kasuwanci da zamantakewa da sauran abubuwa.

Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sototo ya ce Najeira da Nijar ƙasa ɗaya ce ta fuskanr al'ada da addini da tarihi da zumunci Turawa ne kawai suka raba ta.

''Alaƙar Najeriya da Nijar alaƙa ce da jini da tsoka, domin kuwa kashin 50 cikin 100 na ƙabilun da ke Nijar akwai su a Najeriya, kuma tun kafin zuwan Turawa ƙasa ɗaya ce, su ne suka raba su'', in ji Farfesa Bunza

Shehin malamin ya ce ''yadda akwai katsinawa a Najeriya, to akwai su a Nijar, akwai Gobirawa da fulani da sauran ƙabilu tsakanin kasashen biyu''.

Idan muka ɗauki batun 'Ƙasar Hausa' wadda ta ƙunshi wasu yankunan ƙasshen biyu, ta taimaka wajen ƙulla zumunta na 'yan uwantaka tsakanin Najeriya da Nijar, kasancewar al'umomin ƙasashen biyu na magana da Harshen na Hausa.

Sannan batun addini ya yi matukar tasiri wajen habbaƙa amincin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Addinin musulunci shi ne addinin da ya haɗa ƙasashen biyu musamman yankin arewacin Najeriya.

Haka kuma Farfesa Bunza ya ce yanzu haka kawai mutanen Nijar da ke da gonaki a Najeriya kuma mutanen Najeriya da ke da gonakin noma a Jamhuriyar Nijar.

''Ta fuskar sarautar gargajiya sarkin Katsinan maradi asalinsa daga garin Katsina ta Najeriya yake'', in ji shehin malamin

A yanzu ƙasashen biyu sun haɗa kan iyaka ta ɓangaren jihohin Najeriya har guda shida da suka haɗar da Sokoto da Kebbi da Katsina da Jigawa da Yobe da Borno.

A don haka ne har yanzu huldar dangantaka ke ci gaba da wanzuwa takanin ƙasashen biyu da wani mawaƙi ya kira da ''Hassan da Hussani''.

Farfesa Bunza ya kuma ce akwai manyan tituna da gwamnatin Najeriya ƙarƙashin mulkin Yakubu Gawon ta gudanar a jamhuriyar Nijar.

Ko ya dace Najeriya ta kai wa Nijar hari?

Tun bayan sanarwar da Ecowas ta fitar ƙarƙashin jagorancin shugaban Najeriya Bola Tinubu, wasu manyan fitatun 'yan Najeriya ciki har da Kungiyar dattawan Arewa ta 'Arewa Consultative Forum' (ACF) da kuma tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar ke kira ga kungiyar da ta kauce wa ɗaukar matakin soji kan Nijar din.

Sun ce hanyar da kawai ta fi dacewa wajen warware wannan taƙaddama ita ce hanyar diplomasiyya, in kuma hanyar ba ta ɓulle ba to a iya amfani da jerin takunkumi kan waɗanda suka shirya juyin mulkin domin tilasta musu sake tunani don mayar da mulki hannun farar hula.

Sun ce idan aka yi amfani da ƙarfin soji babu wanda zai abin zai fi shafa sai fararen hular da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Toshon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abukakar cikin wata sanaraw da ya fitar ya ce ''batun amfani da ƙarfin soji a jamhhriyar Nijar ya haifar da zaman ɗar-ɗar a Africa ta yamma, kuma abin na jan hankalin ƙasashen duniya game da halin da makwabciyar mu ke ciki''.

''Al'amarin na ƙara zama abin damuwa saboda adadin ƙasashen da suka fuskanci juyin mulkin soji a yankin na ƙara yin yawa'', in ji Atikun.

Haka ita ma ƙungiyar Dattawan Arewa ta ce ya kamata a yi kaffa-kaffa a kuma kauce wa amfani da ƙarfi wajen kawar da sojojin da suka yi juyin mulki don maido da Bazoum.

Shin amfani da ƙarfin soji zai shafi alaƙar Najeriya da Nijar?

Atiku Abubakar ya ce ''yayin da ECOWAS ke ci gaba da ƙoƙarin maido da mulkin dimokradiyya a Nijar, to amma bai kamata ƙungiyar ta bi tafarkin amfani da ƙarfin soji ba domin gudun kada abubuwa su ƙara rincabewa''.

Haka ita ma ƙungiyar dattawan Arewacin ƙasar ta 'Arewa Consultative Forum' ta ce a yi kaffa-kaffa kan amfani da ƙarfin soji, domin a cewarsu hakan ka iya lalata tsohuwar dangantakar da ke tsakanin ''tagwayen ƙasashen''.

Sakataren ƙungiyar na kasar Malam Muratala Aliyu ya shaida wa BBC cewa bai kamata a yi amfani da karfin soji, a maimakon sauran hanyoyin diplomasiyya.

''Muna da tsohuwar dangantaka mai ƙarfi tsakaninmu da Nijar tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, muna da auratayya da kasuwanci a tsakaninmu'', in ji sakataren na ACF.

A nasa ɓangare Farfesa Bunza ya ce hanyar da tafi dacewa ta warware rikicin ita ce hanyar diplomasiyya.

''Ba ma son abin da zai kawo fitina takanin ƙasashen biyu da zai ɗauki watanni ko shekaru masu yawa ana gwabzawa'', in ji Farfesa Bunza.

Ya kuma shwarci gwamnatin najeriya da kada ta yi amfani da ƙarfin soji wajen magance matsalar Nijar.

''A sani cewa babu wata ƙasa da aka ɗaukar wa matakin soji sannan aka ƙare lafiya a duniya, dan haka kar su je su janyo mana yaƙin duniya'', in ji Bunza.

Shehin malamin ya kuma yi kira ga shugabannin Najeriya da 'yan siyasar da su guji ɗaukar matakin sojin saboda yadda zai shafi alaƙa tsakanin manyan aminan juna biyu na Afirka.

Tura tawagar wakilan Ecowas

Tuni dai ƙungiyar Ecowas ta tura tawagogi gubi zuwa Nijar da makwabtanta, inda tawaga tafarko ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojin kasar Janar Abdussalami Abubakar ta gana da wakilan gwamnatin mulkin sojin Nijar ranar Alhamis da maraice.

Haka kuma Ecowas din ta sake tura wata tawagar wakilai ƙarƙashin jagorancin Ambasada Babagana Kingibe zuwa kasashen Libya da Algeriya kan batun juyin mulkin na Nijar.

A ranar Juma'a ne kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da wasiƙa zuwa ga Majalisar Dattawan ƙasar yana mai neman amincewarta domin tura sojojin ƙasar zuwa Nijar.

A yayin da wa'adin mako guda da ecowas ke bai wa sojojin Nijar din ke ciki a ranar Lahadi, abin jira a gani shi ne ko kungiyar ta yammacin Afirka za ta cika alƙawarin da ta dauka ta amfani da ƙarfin soji domin maido da gwamnatin farar hula a Nijar din.