'Kudin fito ne dalilin tsadar motoci a Najeriya'

Motoci

Asalin hoton, Photoshot

Bayanan hoto, Farashin motocin ya tashi ne sakamakon kudin fiton da ake biya

Kungiyar masu sayar da motoci a Najeriya ta koka kan wani tsari da hukumar kwastam ta yi, na yi wa wasu motocin da ake shigarwa kasar kudin-goro, dangane da kudin-fiton da hukumar ke karba a kan su.

 Kungiyar ta ce gwamnati ta kayyade kudin fiton ne a kan motocin da ba su wuce shekara goma da kerawa ba, kenan haka za a biya ko da mota ta fi haka tsufa.

Hukumar kwastan din tana karbar kudin fiton ne ta hanyar intanet da aka fi sani da e-valuation.

Shugaban kungiyar masu sayar da motocin, Injiniya Prince Ajibola Adedoyin, ya shaida wa BBC cewa tsarin kudin fiton na cikin dalilan da suka sa motoci ke tsada, kuma sana`arsu na fuskantar barazana.

“Mun san cewa idan aka yi wannan to za a samu matsala sosai, saboda sun ce shekara 10 da kera mota watau motoci da aka yi daga daga 2012 zuwa sama, su ne kadai zaa iya shigowa da su cikin kasar” in ji shi.

Ya ce da farko hukumar kwastam ta sa kudi a kan sabbin motoci amma kungiyar ta ki amincewa da haka, amma a tattaunawar da suka yi da jami'an kwastam daga bisani sun fada musu cewa za su yi la'akari da shekarar mota.

Sai dai kungiyar ta ce tun a wannan lokaci sun fada musu cewa za a samu matsala idan suka yi haka, a cewar Prince Ajibola.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu kungiyar masu sayar da motocin ta ce hukumar Kwastan ta fada musu cewa za ta yarda su shigo da motocin da suka fi wadannan tsufa, amma za su biya kudi iri daya da na wadanda aka yi daga 2012 zuwa sama.

“Ka ga yanzu za ka sayi mota misali miliyan daya amma za su sa ka biya duti na miliyan biyu, to ka gani ta ya mutane za su iya sayen wannan mota? shi yasa kudin motoci ya hau sosai”, in ji Prince Ajibola

Kungiyar ta ce matsalar za ta sa masu sayar da motoci su rika zuwa wasu kasashe domin su sayar da motocinsu, kuma wannan na nufin cewa gwamnatin tarayya za ta samu raguwa a yawan kudaden shiga, tare da haifar da matsalar shigo da motoci ta haramtacciyar hanya.

Shugaban kungiyar ya ce duk da cewa tashin farashin dala na tasiri a kan matsalar, amma kudin dutin da zasu biya shi ne ya fi tasiri.

Kazalika kungiyar ta nuna fargabar cewa tsarin kan iya sa wasu mamboninta su rasa ayukkan yi, idan ba a dauki mataki ba

Ta ce ta na da mambobi sama da miliyan uku masu sayar da motoci a cikin Najeriya.