Shugaban ƙasa 'mai gaskiya' da ke fuskantar zargin cin hanci

Shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yana cikin matsala.

Wani jawabi da ya yi cikin ciccijewa a yayin wani taron tsare-tsare na ƙasa ranar Juma'a ya nuna cewa da yana fuskantar gagarumar matsala.

Ya amince cewa jam'iyyarsa mai mulki ta African National Congress (ANC), "ta yi rauni sosai," amma shugaban ƙasar kansa yana fuskantar suka.

Shekara huɗu da suka gabata, ya maye gurbin Jacob Zuma, shugaban ƙasar da ya "shahara kan batun cin hanci" inda ya yi alkawarin cewa zai yi mulki cikin gaskiya.

Amma a yanzu shi ma yana fuskantar tasa dambarwar mai alaƙa da cin hanci.

Ana yi masa laƙabi da "mai abin kunyar da ya faru a gona", saboda wani rikici kan wani zargin rufa asirin wata sata da aka yi a gonarsa, Phala Phala, a watan Fabrairun 2020.

Wannan abu yana faruwa ne a shekarar da ANC take shirin zaɓar ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2024 kuma Mr Ramaphosa yake ci gaba da fuskantar matsi da sa ido.

Bayan jan ƙafar da ya dinga yi, a ƙarshe ya amsa tambayoyin da aka yi masa a kan lamarin daga babban jami'in hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasar.

Kholeka Gcaleka ya yi barazanar gurfanar da shugaban ƙasar a gaban ƙuliya bayan da ya gaza cimma wa'adin da aka ɗibar masa na amsa tambayoyi.

Labarin fashin da kuma zargin abin da ya biyo bayan sun fara bayyana ne a watan Yuni daga bakin Arthur Fraser, tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya ta ƙasar.

Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin, wanda aboki ne na ƙut da ƙut ga Zuma, ya zargi shugaban ƙasar da sace mutane don kudin fansa da rashawa da kuma karya doka kan zargin cin dunduniyar waɗanda ake zargi da sace dala miliyan huɗu daga gonarsa.

Mr Fraser ya yi zargin cewa wadannan makudan kuɗaɗen da aka ce an cuccusa su a cikin kushin, za su iya kasancewa kudi ne da aka samu sakamakon cin hanci.

Wasu ƴan ƙasar Namibiya ne ake zargin sun saci kuɗaɗen, bayan haɗa kai da wani ma'aikacin gidan gonar.

‘Ba a aikata mummunan laifi ba’

Saboda kudin da aka sata na kasar waje ne, hakan yana nufin an karya dokokin canjin kudi.

A martanin farko, shugaban kasar ya ce "babu tushen zargin aikata mummunan laifi.”

Ofishin Mr Ramaphosa ya tabbatar cewa an yi fashi a gonarshi da ke lardin Limpopo “wajen da aka sace kudaden shiga daga cinikin namun daji”, sai dai ya musanta lissafin da Mr Fraser ya gabatar.

Shugaban ya yi watsi da zargin Mr Fraser a matsayin na bata masa suna da ke da asalin wadanda ke kalubalantar yakin da yake yi a kan cin hanci da rashawa.

Ya kuma yi imanin cewa masu adawa da shi a siyasance da ke cikin ANC ba su so ya sake yin takara na wa’adi na biyu.

A wani jawabi da yayi makonni biyu da suka wuce, Mr Ramaphosa ya ce yayi ”alkawarin ba da duka hadin kai a binciken” kuma zai dauki alhaki idan aka same shi da laifi.

Dokokin Jam’iyyar ANC sun tanadi cewa duk wanda ake zargi da cin hanci da wasu munanan laifuka dole su sauka yayin da ake gabatar da bincike.

Duk da cewa har yanzu ba’a zargi shugaban da aikata laifi ba, masu goyon bayan Zuma na so ya sauka daga kan aikin sa.

A watan da ya gabata ne daruruwan su suka yi gangami a babban ofishin ANC suna nema a tsare shi kuma ya ajje aiki.

Zubar da kimar kasa

Masu adawa su ma suna hura wa shugaban wuta.

Bantu Holomisa, shugaban jam’iyyar United Democratic Movement ya rubuta wasika zuwa ga kakakin majalisar dokokin kasar inda ya bukaci a dakatar da shugaban kasar har sai sakamakon binciken da ake yi a kan shi ya fito.

"Wannan zargin ya zubar da kimar kasarnan sosai, kuma zai iya shafar karfin gwiwar masu zuba jari ta yadda ba a so, saboda Shugaba Ramaphosa ya bayyana kan sa a matsayin shugaba na gari,” a cewar Mr Holomisa.

Duk da cewa Shugaba Ramaphosa na da tambaoyin da zai amsa dangane da dalolin da aka sace a gonarsa, lokacin da Mr Fraser ya fito ya yi magana ya sa zargin wani abu duba da takarar shugabancin ANC.

Mutanen Afirka ta Kudu sun saba da gani ana zargin shugabannin su da manyan laifuka, da jita-jita da kazafce-kazafce gabannin takara mai zafi na babbar kujerar ANC.

Babu bambancin wannan shekara da shekarun baya.

A watan Disamba mai zuwa, ANC za ta gudanar da karamin zabe domin zaben wanda zai kasance dan takarar shugaban kasa, kuma dole a samu zaman doya da manja.