Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kotu ta samu Amazon da laifin keta hakkin sirrin yara
Kamfanin Amazon zai biya dala miliyan 25 don sasanta zare-zargen da ake yi masa a kan cewa ya keta hakkin sirrin yara ta hanyar amfani da manjaharsa ta Alexa
Kamfanin ya amince ya biya Hukumar cinikayya ta Amurka (FTC) kudin bayan an zarge shi da kin goge muryoyin da manhajarsa ta Alexis ta naɗa bisa bukatar iyaye.
An gano cewa kamfanin ya na riƙe muhimman bayanai na tsawon shekara.
Wani reshe na kamfanin da ake kira Ring shi ma zai biya diyya bayan da aka gano cewa ya bai wa ma'aikata damar shiga bayanan abokan ciniki.
Kamfanin Ring zai biya mahukunta dala 5.8 a cikin hukuncin da wata kotu tarraya da ke Columbia ta yanke.
Hukumar ta FTC ta yi korafi a kan manhajar Alexa inda ta yi ikirarin cewa Amazon ya sha ba masu amfani da manhajar ciki harda iyaye tabbacin cewa za su goge muryoyin da naurar ta naɗa.
Sai dai kamfanin bai yi haka ba, inda ya shafe tsawon shekaru yana adana bayanai tare da amfani da su ba kan kaida ba don taimakawa wajan inganta naurar ta Alexa
End of Karin labaran da za ku so karantawa
A cikin wata sanarwa, Samuel Levine, Darakta a ofishin kare hakkin masu Siyaya na hukumar ta FTC, ya zargi Amazon da "yaudarar iyaye ta hanyar adana muryoyin yaran da aka naɗa tare da yin watsi da bukatun iyaye na goge bayanan".
Kamfanin "ya sadaukar da sirri don riba", in ji shi.
Hakazalika hukumar ta FTC ta ce kamfaninsa na Ring wanda Amazon ya saya a 2008 ya ba dubban ma'aikatasa da 'yan kwangila damar kallo ko sauraren abubuwan da kwastamominsu suka naɗa.
Hukumar ta ce sun samu damar dubawa da saukar da bayanan hotunan bidiyo na sirri domin su yi amfani da su.
Amazon ya shaida wa BBC a cikin wata sanarwa cewa "kamfaninsa na Ring ya yi gaggawar daukar matakan shawo kan matsalolin shekaru biyu da suka gabata, tun kafin hukumar ta FTC ta soma bincike.
Hukumar ta yi korafin cewa ɗaya daga cikin ma'aikatan ya kalli dubban hotunan bidiyo mata masu amfani da kyamarar Ring da ya dauki hotonan wasu wuraren da ke cikin gidajensu kamar banɗakunan ko dakunan kwanansu
An taka ma sa birki ne lokacin da wani abokin akinsa ya bankaɗo shi, a cewar hukumar.
"Rashin mutunta sirri da tsaro da Ring ya yi ya sa an rika leken asirin masu amfani da naurar tare da cin zarafi", a cewar Mista Levine.
"Umurnin na FTC ya bayyana a sarari cewa sanya riba akan sirri baya biya."
A cikin wata sanarwa da ya aikewa BBC, Amazon ya ce: "Yayin da ba mu yarda da ikirarin FTC ba game da Alexa da Ring, kuma mun musanta karya doka, amma kuɗin da muka biya ya sa mun manta da abubuwan da suka faru a baya".
Kamfanin ya kuma kara da cewa zai ci gaba da kirkiro karin manhajoji da za su adana sirrin abokan cinikayya.