Matsayin Najeriya da Ivory Coast ya ƙaru a kwallon ƙafa bayan Afcon

Asalin hoton, Getty Images
Matsayin Ivory Coast ya yi sama da mataki 10 a jerin ƙasashen da suka fi iya taka leda a duniya, bayan lashe kofin Nahiyar Afrika na 2023 da ta yi.
Najeriya da ta buga wasan ƙarshe a gasar ta Afcon matsayinta ya yi gaba da mataki 14.
Super Eagles yanzu tana matsayi na 28 duk da cewa ta yi rashin nasara a ranar Lahadi da ci 2-1, ta kuma koma matsayi na uku a nahiyar Afrika.
Angola ta koma matsayi na 93 daga 24 bayan rashin nasarar da ta yi a wasan kusa da dab da na ƙarshe.
Matsayin Tunisia da Algeria ya yi ƙasa da matsayi 13, sun koma 41 da 43, bayan cire su da aka yi tun a matsayin rukuni a gasar.
Moroko ce ke jan ragamar ƙasashen Afrika inda take matsayi na ɗaya, a duniya kuma ta koma matsayi na 12 bayan fitar da ita daga Afcon a matakin 'yan 16.
Senegal tana matsayi na 17 bayan cireta da mai masaukin baƙi ta yi a matakin 'yan 16.
Matsayi 10 na farko da Fifa ta fitar bai sauya ba, yana nan kamar yadda yake bayan kammala kofin duniya na 2022, Argentina na sama yayin da Faransa ke biye mata sai kuma Ingila.
Ga dai jerin ƙasashe 10 na Afrika da Fifa ta fitar:
1. Morocco: ce ta ɗaya a Afrika, ta 12 a duniya.
2. Senegal: ta biyu a Afrika, ta 17 a duniya.
3. Nigeria: ta uku a Afrika , ta 28 a duniya..
4. Egypt: Hudu a Afrika, ta 36 a duniya.
5. Cote d’Ivoire: ta biyar a Afrika, ta 39 a duniya.
6. Tunisia: Sixth in Africa, ta 41 a duniya.
7. Algeria: ta bakwai a Afrika, ta 43 a duniya.
8. Mali: ta takwas a Afrika, ta 47 a duniya.
9. Cameroon: ta tara a Afrika, ta 51 a duniya.
10. South Africa: ta 10 a Afrika, ta 58 a duniya.











