Su wane ne ke mulkin China a yanzu?

Asalin hoton, EPA
Jam’iyyar Kwaminisanci ta China a karshe dai ta bayyana mutanen da za su ja ragamar kasar tsawon shekara biyar a nan gaba.
Mambobi bakwai na babban kwamitin zartarwa na jam’iyyar su ne daidai da majalisar ministoci ta shugaban kasa.
‘Yan wannan kwamiti su ne jiga-jigai a cikin jam’iyyar, kuma zuwa wannan matsayi yana bukatar mutum ya kasance ba kawai mai fitaccen tarihi na siyasa ba, sai ya kasance wanda ya iya kulle-kulle na siyasar cikin jam’iyya.
Ba wani sabon abu ba ne a ga an yi manyan sauye-sauye a cikin wnnan kwamiti bayan wa’adi ya kare, saboda haka a wannan karon ma sauyin bai zo da wani mamaki ba.
Yawancin mambobin kwamitin na yanzu da kusan a ce Shugaba Xi Jinping ne ya zabe su da kansa, sababbi ne in banda Zhao Leji da Wang Huning.
Babu ko mace daya a cikin mutum 24 mambobin babban kwamitin jam’iyyar, wanda daga cikinsu ne ake zabo jiga-jigan bakwai.
Da farkon farawa dai a iya cewa yanzu ba wata tababa, Xi Jinping shi ne har yanzu yake rike da iko kuma zai ci gaba da kasance a kan mulki tsawon iya lokacin da yake so idan dai ba wani tsautsayi ko dambarwar siyasa ba ce ta taso ta kawar da shi ba.
Daman ba wani da ya san yadda siyasar kasar ke gudana a yanzu da zai yi tsammanin za a ga sauyi a shugabancin kasar sabanin ci gaba da kankane iko da Mista Xi ya yi a jam’iyyar ta Kwaminisanci.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bugu da kari kuma mambobin sabon kwamitin jiga-jigan yana cike ne da mabiyansa.
Babu ko da mutum ɗaya da yake da wani ɗan sabanin ra’ayi da shugaban da aka sanya a ciki.
A iya cewa nadin da ya fi daukar hankali shi ne na sanya Li Qiang a matsayin Firimiya, wato mataimakin shugaban kasa kenan, wanda kuma shi ne zai ja ragamar harkokin tattalin arzikin kasar.
Naɗa mutumin da ya jagoranci mummunan tsarin kullen Shanghai , inda miliyoyin mutane suka rasa abinci, a matsayin wanda zai jagoranci harkar tattalin arziki, hakan na nuna cewa biyayya ga Shugaba Xi ita ce gaba da kwarewa wajen samun mukami.
Duk da irin laifuka da kura-kurenta jam’iyyar Kwaminisanci ta China tana bugun kirji da cewa tana la’akari ne da kwarewa wajen bayar da mukami, to amma wannan naɗin kusan a ce ya saba da wannan magana.
Bugu da kari wannan zai nuna cewa Babban Sakatare wato Shugaba Xi ba shi da wata kwarewa ko fahimta ta tattalin arziki da kuma abin da ake bukata domin bunkasa tattalin arziki.
Ko kuma idan har yana da wannan ilimi to sai a ce bai ba wa tattalin arzikin fifiko ba.
A gareshi kenan, biyayya ga jam’iyya da kuma kishin kasa su ne a gaban komai.
Haka kuma babu mace ko guda ɗaya a kwamitin jiga-jigan da ke jagorantar China, mutum bakwai.
Daman ba a taba sanya mace a wannan kwamiti ba, kuma a wannan karon ma Xi bai saɓa wannan al’ada ba.
Mace ɗaya da ta taba kasancewa ita ce Madame Mao, a can baya, to amma ko a lokacin ma ba a hukumance take ciki ba.
Rashin naɗa mace a kwamitin ba zai yi wa mutane da yawa daɗi ba, amma kuma ba a bin mamaki ba ne.
Ga jiga-jigan da ke jan ragamar China, karkashin Shugaba Xi Jinping

Asalin hoton, Reuters
Li Qiang - Shekararsa 63
Mukaminsa na siyasa a yanzu: Shi ne sakataren jam'iyya na Shanghai
Ana masa kallon wanda Shugaba Xi ya fi amincewa da shi a cikin mukarrabansa.
Li ya yi aiki a kananan yankuna a lardin Zhejiang. Lokacin da Xi yake shugaban jam'iyya a Zhejiang, Li ne shugaban ma'aikatansa.
Yadda ya jagoranci harkoki a yayin annobar korona a Shanghai a farkon shekaran nan abu ne da mutane ba su ji dadinsa ba, wanda ake takaddama a kansa.
Har sai da aka yi ta yada jita-jita ma cewa kila abin ya shafi siyasarsa.
To amma sababin haka, wannan nadin da Shugaba Xi ya yi masa ya nuna cewa biyayya ga shugaban ita ce gaba da komai.
A shekara mai zuwa ne za a tabbatarwa da kowa daga cikin mambobin kwamitin mukaminsa, kuma da yawa na ganin Li zai zama Firimiya na gaba, wato mataimakin Shugaba Xi ke nan.

Asalin hoton, Reuters
Zhao Leji - Shekararsa 65
Mukaminsa na siyasa na yanzu : Shugaban Babbar Hukumar Tabbatar da Da’a
Ana daukar Zhao a matsayin wani tauraro mai tasowa a jagorancin China, kuma yana da kusanci da lardin Shaanxi, kamar dai Xi.
Bayan da ya samu shiga gwamnatin lardin Qinghai, nan da nan likkafarsa ta yi gaba, inda ya zama gwamna yana da shekara 42 - mutum mafi karancin shekaru da ya zama gwamnan lardi a kasar.
A matsayinsa na shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Zhao ne ke da alhakin tabbatar da da’a a jam’iyyar, kuma ya kai rahoton manyan jam’iyya da dama da suka karbi cin hanci a tsawon shekaru.

Asalin hoton, Reuters
Wang Huning - Shekararsa 67
Mukaminsa na siyasa na yanzu: Shi ne Sakatare na farko na jam'iyyar Kwaminisanci.
Tsohon malami kuma farfesa, Wanga ya samu daukaka bayan da ya dauki hankalin manyan 'yan siyasa.
An gabatar da shi ga tsohon shugaban kasar Jiang Zemin, inda ya samu karin girma zuwa mai bayar da shawara ga Jiang.
A matsayinsa na fasihin jam'iyyar, ana daukar Wang a matsayin wanda ya ke kirkiro da dama daga cikin manufofi da tsare-tsare na jam'iyyar, ciki har da akidun shugabanni uku:
Wato hadakar tunani da manufofin shugabannin kasar biyu na baya da kuma na yanzu, wato Jiang Zemin da Hu Jintao da kuma Xi Jinping.
An ce shi ne ya kirkiro gagarumin shirin nan mai cike da buri na 2013 na China na zuba jari wajen bunkasa abubuwan jin dadin jama'a a hukumomi da kasashen duniya kusan 150.
Kuma an ce yana dasawa da dukkanin bangarori a jam'iyyar.

Asalin hoton, Reuters
Cai Qi - Shekararsa 66
Matsayinsa na siyasa a yanzu: Shi ne Magajin Garin Beijing
Amini ne na kusa sosai ga Shugaba Xi, inda ya yi aiki da shugaban na China a lardunan Fujian da Zhejiang, kuma yana masa biyayya sosai
A cikin jam'iyyar ana danganta nasarar da birnin Beijing ya samu ta karbar bakuncin wasannin Olympics na bazara a farkon shekarar nan a tsakar annobar korona, da shi.
To amma kuma ya janyo ce-ce-ku-ce a lokacin da ya kaddamar da wani shiri a 2017 na rage yawan al'ummar babban birnin.
Abin da a karshe ya tilasta wa talakawa da dama ficewa daga birnin.

Asalin hoton, Reuters
Ding Xuexiang - Shekararsa 60
Matsayinsa na siyasa a yanzu: Darekta ne a Ofishin Babban Sakatare, kuma Ofishin Shugaban Kasa.
Kwararren injiniya, Ding ya fara harkokin siyasa a wata cibiyar bincike ta gwamnati da ke Shanghai.
Duk da cewa ba shi da wata kwarewa a matsayin sakataren jam'iyya na lardi ko gwamna, kwarewar da ake bukata wajen taka matsayi a siyasar, ya zama sakataren Xi a 2007.
Tun 2014 ya kasance babban jami'i a ofishin shugaban kasa, abin da a takaice yake nufin shi ne shugaban ma'aikata na ofishin shugaban kasa.
Babban mai fafutukar bin akidar Xi Jinping, yana ɗaya daga cikin wadanda shugaban ya fi amincewa da su.
Ya raka shugaban na China a ziyarce-ziyarce da dama a ciki da wajen China - masu lura da al'amura sun ce kusan shi ne shugaban da ya fi zama da shi fiye da duk wani jami'i a shekarun nan.

Asalin hoton, Reuters
Li Xi - Shekararsa 66
Matsayinsa na siyasa a yanzu : Sakataren jam'iyya a lardin Guangdong.
Ya kasance makusancin Xi wanda yake da alaƙa ta kut da kut da iyalin shugaban na China.
Ana masa kallo a matsayin mai magance matsala idan ta taso, saboda yadda ya tafiyar da wata badakala da ta taso a 2017 a lardin Liaoning kan wasu alkaluma na karya da aka fitar kan tattalin arziki.
Ya riƙe shugaban jam'iyya a birnin Yanan mai muhimmanci, inda nan ne Mao Zedong ya yi amfani da shi a matsayin hedikwatar jam'iyyar a lokacin yakin duniya na biyu, inda Xi ya yi shekara bakwai yana aikin gwale-gwale.
Li ne ya matsa aka samu bunkasar masana'antun kere-kere da sauye-sauyen tattalin arziki a Guangdong.











