Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Coppa Italia ne kofin farko da Juventus ta ci a shekara uku
Juventus ta lashe babban kofi karo na farko cikin shekara uku bayan nasarar doke Atalanta 1-0 ranar Laraba da dare a wasan ƙarshe na Coppa Italia.
Dusan Vlahovic ne ya ci ƙwallon ɗaya tilo a filin wasa na Stadio Olimpico minti huɗu kacal da take wasan lokacin da Andrea Cambiaso ya ba shi ƙwallon kuma ya jefa ta raga daga yadi na 12.
Ɗan wasan gaban na Serbia ya sake cin wata amma aka soke ta saboda satar gida.
Ɗan wasan Atalanta da Najeriya Ademola Lookman, da kuma Fabio Miretti sun buga ƙwallayen da suka bugo turke.
An bai wa kocin Juventus Massimiliano Allegri jan kati a ƙarshe-ƙarshen wasan saboda nuna rashin amincewa da wani hukunci. Shi ne kocin da ya lashe Coppa Italia biyar kuma mafiya yawa a tarihi.
Yunƙurin Atalanta na lashe wani babban kofi ya ci tura bayan nasarar cin kofin Coppa Italiya tun shekarar 1963.
Sai dai suna da damar cin babban kofi a mako mai zuwa yayin da za su gwabza wasan ƙarshe na gasar Europa League da Bayer Leverkusen a birnin Dublin.