Me zai faru idan ba a warware rikicin APC da PDP nan kusa ba?

APC da PDP

Asalin hoton, TWITTER/FACEBOOK

A yayin da yaƙin neman zaɓukan 2023 na Najeriya ke ƙaratowa, rikici yana ci gaba da dabaibaye manyan jam'iyyun ƙasar na APC da PDP.

Tsohon sakataren gwamnatin tarayyar ƙasar Babachir Lawal ya sha alwashin APC ba ta kai labari ba saboda batun ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa duk Musulmai ne, a ganinsa mummunan shiri ne na raba kan arewacin ƙasar.

"Ga dukkan masu son haɗin kan ƙasar nan, musamman ma na arewa inda su abin zai fi shafa, wannan tafiyar ba za ta yi nasara.

Kuma za mu tabbatar sai mun kayar da su ta yadda babu bwani mai cikakken hankalin da zai sake tunanin hakan," in ji Lawal.

Ya ce ba shi da tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara ba ne kawai suke adawa da wannan tikiti na Musulmi da Musulmi na APC.

Lawal wanda ya faɗi waɗanan maganganun a wata hira da gidan talabijin na Arise ranar Laraba 21 ga watan Satumba, ya ce tuni sun fara gangain nuna wa mutane cewa wannan tafiya ba mai kyau ba ce.

A nasa ɓangaren, Yakubu Dogara ya ce batun tikitin Musulmi da Musulmi abu ne da ba zai haifar wa APC alheri ba.

Dogara ya bayyana ra'ayinsa ne a Abuja ranar Larabar shi ma a yayin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taron da gamayyar Kiristocin Najeriya ta shirya.

Nyesom Wike da rikicin PDP

Wike

Asalin hoton, GOVWIKE/TWITTER

A ranar Laraba ne Gwamna Nyesom Wike da tawagarsa suka janye daga kwamitin yaƙin neman zaɓe na PDP saboda ƙin murabus ɗin da shugaban jam'iyyar ya yi.

Gwamnan da tawagarsa sun ce dole ne jam'iyyar ta miƙa shugabancinta ga ɗan yankin kuduncin ƙasar tun da ɗan arewa ne ya samu takarar shugaban ƙasa a PDP ɗin.

Mambobin tawagar sun haɗa da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da tsofaffin gwamnonin jihohin River da Ekiti, Donald Duke da Ayo Fayose, da wasu ƴan jam'iyyar da dama.

Me masu sharhi kan siyasa ke ganin zai faru?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa kuma ɗan jarida a birnin Fatakwal na jihar Rivers, Lekan Ige, ya shaida wa sashen BBC Pidgin cewa masu adawa da tikitin Musulmi da Musulmi din nan a ganinsa ba don sun ƙi jinin jam'iyyar suke yi ba, suna yi ne don kare muradun mutane masu mabambantan ra'ayoyi.

Ya ce ya rage wa jam'iyyar APC ta warware matsalolinta kuma yana da tabbacin za ta yi hakan gabanin zaɓen da ke tafe.

Ya ce a zaɓen 1993 Najeriya ba ta damu da bambancin addini ba a lokacin da aka zaɓi ɗan takarar jam'iyyar SDP Moshood Abiola da mataimakinsa Babagana Kingibe, duk da cewa dukkansu Musulmai ne.

"Jam'iyyar ta koyi wani abu ne daga wancan yanayi kuma tana duba yadda za ta iya ɗinke ɓarakar da take da ita a yanzu," in ji Ige.

Ige ya ce an ɗan tayar da jijiyoyin wuya a lokacin da Abiola ya zaɓi Kingibe a matsayin mataimakinsa amma ƴan jam'iyyar ne suka yi aiki tare don samar da ƴan takarar.

Ya ce ita kuwa PDP, ya rage nata ta tsara dabarun warware matsalolin da take fama da su. Ige ya ce wannan duk siyasa ce, kuma jam'iyyar za ta yi ƙoƙarin warware rikicin idan dai har suna son yin nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Kan batun ko akwai yiwuwar sauya sheƙa kuwa, Ige ya ceba ya jin Wike zai bar PDP saboda su ƴan siyasa a ko yaushe suna duba wane alkawari sabuwar jam'iyyar za ta yi musu ne.

"Don haka idan har ya sauya sheƙa zuwa wata jam'iyyar, wane alkawari za a yi masa? Ba za su iya ba shi gwamna ko shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa ba.

"Sai dai idan minista zai nema a ba shi, wanda ko a PDP ma zai samu wannan cikin sauƙi idan har jam'iyyar ta kai labari," a cewar mai sharhi.

Ige ya ce wani dalilin da zai hana Wike barin PDP kafin zaɓen shi ne ganin shi ke mara wa ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Rivers baya, kuma zai so ya yi nasara."

Duk wani yunƙuri na ficewa daga PDP zuwa wata jam'iyyar na barazana ga damar nasa ɗan takarar ta cin zaɓe.

Don ba zai iya yi wa ɗan takarar gwamnan Ribas na PDP kamfe ba kuma a lokaci guda a gan ka kana yi wa ɗan takarar shugaban ƙsa na APC ko Labour kamfe, abin bai yi ma'ana ba," in ji Ige.

Ya ce daga yanzu zuwa watan Fabrairu lokaci mai dan tsawo kuma komai na iya faruwa, wanda a ƙarshe za su iya fitowa su ce matsalar cikin gida ce kuma an sasanta.

"Idan ba su warware matsalar ba kuma, za su kawo tarnaƙi ga damarmakin jam'iyyun wajen cin zaɓukan 2023," kamar yadda ya ƙara da cewa.

‘Wike ba irin mutumin da PDP za ta yi wasa da shi ba ne’

Wani mai sharhi kan siyasa kuma masanin tattalin arziki Sani Bala, ya ce idan ana so a ga yadda za ta kaya a zaɓen 2023, dole mutane su yi duba da ƙarfin jam'iyyun siyasa da mutanen da suka tsayar takara.

Bala ya ce sanya batun addini da ƙabilanci a harkokin siyasa na daga cikin abin da ke kashe Najeriya inda ya ƙara da cewa kuma duk ana buƙatar juna.

"Arewacin Najeriya na buƙatar kudanci, kudu ma na buƙatar arewa a siyasance, in ji Bala.

Ya ce abu ne marar kyau ga ƴan siyasa su dinga amfani da addini da ƙabilanci don samun karɓuwa wajen masu zaɓe.

Kan rikicin da ya baibaye PDP kuwa, Bala ya ce Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar ya gaza wajen nemo mafita da sasanta rikicin.

Ya ce Wike yana da ƙarfi a siyasance kuma yana da kuɗin da zai iya juya akalar PDP a yankin kudu maso kudancin ƙasar.

Ya ƙara da cewa yankin kudu maso kudu zai taka rawa sosai wajen samun nasarar APC ko PDP a zaɓen shugaban ƙasa.

"Wike ba irin mutanen da PDP za ta yi wasa da su ba ne. Ya kamata a ce sun yi ƙoƙari sun duba buƙatunsa.

"Ka san cewa ita siyasa duk batun muradu ne, shi ya sa ma ake cewa a yi ta ba da gaba ba," in ji Bala.

Bala ya jaddada cewa idan dai har PDP na so ta ci zaɓe a 2023 to dole ta warware rikicin da ke tsakanin Wike da Atiku.

Sannan yana ganin kowace jam'iyyar siyasa na duba matsalolin da abokiyar hamayyarta ke da su ne don yin amfani da damar hakan ta inganta kanta.

A ganin Bala, idan har waɗannan mutanen suka sauya sheƙa suka kuma taimaka wa jam'iyyar wajen cin zaɓe, to sai an yi yarjejeniya sun ga me jam'iyyar za ta ba su kafin aikata hakan.

Bala ya ce akwai guguwar sauya sheƙa kuma za a ci gaba da ganin hakan daga nan har lokacin zaɓukan 2023.