Abin da ya kamata ku sani kan Champions League ranar Talata

Asalin hoton, Getty Images
Yau ne za a fara wasannin farko a cikin rukuni a Champions League kakar 2022/23, inda za a yi fafatawa takwas.
Wannan ce gasa ta 68 da za a gudanar karo na 31 tun bayan da aka sauya fasalin wasannin.
Real Madrid ce mai rike da kofin da ta lashe a kakar da ta wuce, bayan doke Liverpool a Faransa, ta dauki na 14 jumulla ita ce kan gaba a bajinta.
Cikin wasannin da za a yi rukuni na biyar zai fara fafatawa, wanda ya kunshin AC Milan, Chelsea, Dinamo Zagreb da kuma Red Bull Salzburg

Asalin hoton, Getty Images
Rukuni na biyar:
- AC Milan
- Chelsea
- Red Bull Salzburg
- Dinamo Zagreb
Za a kara tsakanin Red Bull Salzburg da AC Milan da wanda Chelsea za ta ziyarci Dinamo Zagreb a rukuni na biyar.
Wannan shi ne wasa na uku da Red Bull da AC Milan za su fafata a Champions League tun 1994/95 da Milan ta yi nasara gida da waje.
Champions League Laraba 7 ga watan Disambar 1994
- RB Salzburg 0 - 1 Milan
Champions League Laraba 28 ga watan Satumbar 1994
- AC Milan 3 - 0 RB Salzburg
Daya wasan rukuni na biyar za a yi ne tsakanin Dinamo Zagreb da Chelsea - Watakila Pierre-Emerick Aubameyang ya fara buga wa kungiyar ta Stamford Bridge tamaula ranar Talata.
Dan kwallon Gabon, wanda aka dauka a bana daga Barcelona zai saka fuskar roba domin kariya, bayan raunin da ya ji a lokacin da 'yan fashi suka shiga gidan da yake a makon jiya a Sifaniya.
Wannan shi ne karon farko da Dinamo Zagareb da Chelsea za su fafata a babbar gasar tamuala ta Zakarun Turai.
AC Milan tana da Champions League bakwai sai Chelsea mai biyu a rukuni na biyar.
Rukuni na shida ma zai fara wasa ranar Talata da ya kunshi mai rike da kofin Real Madrid da RB Leipzig da Shakhtar Donetsk da kuma Celtic.

Asalin hoton, Getty Images
Rukuni na shida:
- Real Madrid
- RB Leipzig
- Celtic
- Shakhtar Donetsk
Idan anjima Celtic za ta yi wa Real Madrid masauki da fafatawa tsakanin RB Leipzig da Shakhtar Donetsk.
Real Madrid mai kofi 14 jumulla za ta fuskaci Celta mai kofi daya a wasa na uku tsakaninsu, bayan karawa biyu a Europen Cup a 1979/70, inda kowacce ta ci wasanta na gida a lokacin.
European Cup Laraba 19 ga watan Maris 1980
- Real Madrid 3 - 0 Celtic
European Cup Laraba 5 ga watan Maris 1980
- Celtic 2 - 0 Real Madrid
Sai dai RB Leipzig da Shakhtar za su kara a karon farko a gasar Zakarun Turai a tsakaninsu.
Rukuni na shida Real Madrid tana da Champions League 14 da Celtic mai daya.
Ita kuwa Manchester City da Sevilla da Borussia Dortmund da kuma FC Kobenhavn suna rukuni na bakwai.

Asalin hoton, Getty Images
Rukuni na bakwai
- Manchester City
- Sevilla
- Borussia Dortmund
- FC Kobenhavn
Za a buga wasa tsakanin Sevilla da Manchester City da na Borussia Dortmund da FC Kobenhavn a Jamus.
Wannan shi ne karo na uku da za a fafafa tsakaninsu Sevilla da Manchester City tun bayan 2015/2016.
Champions League Talata 3 ga watan Nuwambar 2015
- Sevilla 1 - 3 Man City
Champions League Laraba 21 ga watan Oktoban 2015
- Man City 2 - 1 Sevilla
Borussia Dortmund da FC Kobenhavn za su fafata a karo na uku a Champions League tun bayan 2001/2002.
UEFA CUP Talata 4 ga watan Disambar 2001
- Borussia Dortmund 1 - 0 FC Copenhagen
UEFA Cup Alhamis 22 ga watan Nuwambar 2001
- FC Copenhagen 0 - 1 Borussia Dortmund
Borussia Dortmund ce kadai a wannan rukunin na bakwai mai Champions League daya.
Rukuni na takwas kuwa ya hada da Paris Saint-Germain da Juventus da Benfica da kuma Maccabi Haifa.

Asalin hoton, Reuters
Rukuni na takwas:
- Paris Saint-Germain
- Juventus
- Benfica
- Maccabi Haifa
Ranar Talata za a kece raini tsakanin Paris Saint-Germain da Juventus, sai gumurzu tsakanin Benfica da Maccabi Haifa.
Wannan shi ne karon farko da za a kece raini tsakanin Paris St Germain da Juventus.
Haka kuma Benfica ba ta taba fuskantar Maccabi Haifa ba.
Juventus da Benfica kowacce tana da Champions League biyu a tarihi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Wasannin da za a buga ranar Talata:
- Borussia Dortmund da FC Kobenhavn
- Dinamo Zagreb da Chelsea
- Sevilla da Manchester City
- Paris Saint-Germain da Juventus
- Celtic Glasgow da Real Madrid
- Benfica da Maccabi Haifa
- Red Bull Salzburg da AC Milan
- RB Leipzig da Shakhtar Donetsk










