Antony ne na hudu mafi tsada da aka saya a Premier League

Most EPL expensive players

Asalin hoton, Getty Images

Manchester United ta sanar da cimma yarjejeniyar daukar dan kwallon Ajax dan kasar Brazil, Antony.

Ana cewar United za ta sayi dan wasan kan sama da fam miliyan 80.75 da karin tsarabe-tsaraben fam miliyan 4.25.

Antony zai zama na biyu da United ta dauka kan dan karen kudi - Paul Pogba ne mafi tsada da kungiyar Old Trafford ta saya daga Juventus kan fam miliyan 89.

Mai buga tamaula daga gaba zai zama na biyar da United ta dauka a bana, bayan Lisandro Martinez da Casemiro da Tyrell Malacia da kuma Christian Eriksen wanda kwantiraginsa ya kare a Brentford.

Antony

Asalin hoton, Getty Images

Antony ya taka rawar gani a Ajax da cin kwallo 47 a dukkan fafatawar da ya yi mata kaka biyu.

Dan wasan ya nuna kwarewarsa karkashin Erik ten Hag a Ajax, shi ne kocin ya dauke shi zuwa Manchester United.

Antony, mai shekara 22 zai zama na hudu da aka saya a Premier League da tsada, bayan Paul Pogba da ya koma Manchester United, sai Chelsea da ta kara daukar Romelu Lukaku da kuma Jack Grealish da Manchester City' ta dauka.

Jerin 'yan wasa ukun da aka dauka da tsada a Premier League

Paul Pogba

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ranar 8 ga watan Agustan 2016, Manchester United ta kammala daukar Paul Pogba kan fam miliyan 89.

Dan kwallon tawagar Faransa ya sanar cewar ''lokaci ne ya yi da na sake komawa kungiyar da ta dace da ni da salon wasannina''.

Ya koma Old Traford yana da shekara 23 a lokacin, bayan shekara hudu da ya bar kungiyar zuwa Juventus kan fam miliyan 1.2 a 2012.

Kudin da aka sayi Pogba ya haura fam miliyan 85 da Real Madrid ta dauki Gareth Bale a 2013 a matakin mafi tsada a duniya.

Pogba shi ne dan wasa na hudu da Jose Mourinho ya dauka a lokacin, bayan dan wasan tawagar Ivory Coast, Eric Bailly da dan kwallon Sweden, Zlatan Ibrahimovic da dan wasan Armenia, Henrikh Mkhitaryan.

Karon farko bayan shekara 20 da wata kungiya a Ingila ta sayi dan wasa a matakin mafi tsada a duniya tun bayan da Newcastle United ta biya fam miliyan 15 kudin Alan Shearer daga Blackburn Rovers.

Pogba ya fara zuwa United daga Le Havre a 2009 a matakin mai shekara 16, sai dai wasa bakwai kadai ya yi wa kungiyar, sannan ya bar Old Trafford zuwa Juventus a 2012, bayan da kwantiraginsa ya kare.

Dan wasan ya yi karawa 178 a Juventus da cin kwallo 34 da lashe Champions League a kungiyar ta Italiya a 2015.

Romelu Lukaku

Romelu Lukaku

Asalin hoton, EPA

Ranar 12 ga watan Agustan 2021, Romelu Lukaku ya sake komawa Chelsea daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5.

Mai shekara 28 a lokacin da dan kwallon tawagar Belgium ya sake komawa Stamford Bridge kan yarjejeniyar kaka biyar, bayan da ya koma Everton daga kungiyar kan fam miliyan 28 a 2014.

Kadan ya rage kudin da aka sayo Lukaku ya kai iri daya da wanda Manchester City ta dauki Jack Grealish daga Aston Villa kan fam miliyan 100.

Dan kwallon Belgium shi ne mafi tsada da wata kungiya a Italiya ta sayar, tun farko ya zama na uku mafi tsada da aka dauka a Italiya a 2019 da Inter Milan ta saya daga Manchester United kan fam miliyan 74.

Tun farko Chelsea ta bai wa Everton aron Lukaku a 2013 daga baya ta sayar mata da shi a Yulin 2014 kan fam miliyan 24 a matakin dan wasan da ta saya da tsada a tarihin Everton.

Jack Grealish

Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images

Ranar 5 ga watan Agustan 2021, Manchester City ta sanar da daukar Jack Grealish kan yarjejeniyar kaka shida da za ta kare zuwa 2027.

Ta kuma sayi dan kwallon tawagar Ingila daga Aston Villa kan fam miliyan 100.

Mai shekara 25 ya karbi riga mai lamba 10, wadda Sergio Aguero ya yi amfani da ita a kungiyar.

Kudin da City ta sayi dan kwallon ya haura fam miliyan 89 da Manchester United ta dauki Paul Pogba daga Juventus a 2016.

Kwana bakwai tsakani da City ta sayi Grealish, Chelsea ta sake daukar Lukaku daga Inter Milan kan fam miliyan 97.5.

Hakan ne ya sa Grealish shi kan gaba a matakin wanda aka dauka mafi tsada a tarihin gasar Premier Legue.

Lukaku ne na biyu sai Pogba na uku sannan Antony na hudu.

Jack Grealish

Asalin hoton, Getty Images