Wane tasiri takunkuman Amurka ke yi ga man Rasha da Iran?

    • Marubuci, Jeremy Howell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 5

Amurka na ƙara yawan takunkumai kan Rasha da Iran, da suka shafi ɓangaren mai, abin da ya fi kawo musu arziki.

Sun shafi wasu tankokin mansu da suke da wuyar ganowa da ƙasashen biyu suke amfani da su domin dakon mai ba bisa ka'ida ba.

Takunkuman sun haɗa da rage shigar da mai zuwa China - babbar mai amfani da man Rasha da China.

Hakan ya janyo ƙarancin mai a sassan duniya a makonnin baya-bayan nan lamarin da ya sa farashin mai ya yi tashin gwauron zabo.

Gwamnatin Trump tana iya ƙaƙaba takunkumai masu tsauri kan man Rasha da Iran kuma hakan zai iya sa farashin man ya ɗaga.

Yawan man da Rasha da Iran ke fitarwa, da masu sayen shi

Rasha tana sirrinta bayanan man da take fitarwa amma hukumar kula da nukiliya ta duniya IEA - ta ƙiyasta cewa a yanzu akwai ganga miliyan 7.33 duk rana a ƙasar waje.

A cewar cibiyar da ke nazari kan makamashi, Rasha ce babbar ƙasar da ke samar da mai ga China. Tana kuma shigar da kashi ɗaya bisa uku na kayayyakinta zuwa Indiya.

Amurka da Birtaniya duka sun haramta shigar da man Rasha ƙasashensu a Maris ɗin 2022.

Rasha na samun dala biliyan 190 duk shekara daga man da take fitarwa - arzikin da ake amfani da shi wajen tafiyar da harkokin yaƙi.

Ƙungiyar ƙasashe mafiya karfin tattalin arziki ta G7 ta ƙayyade kowace gangar man Rasha ɗaya kan dala 60.

Sai dai Neil Fleming daga Argus Media, wani kamfanin tattara bayanan makamashi da kayayyaki, ya ce "Ƙayyade farashin bai yi wani tasiri ba.

A shekarar da ta gabata, ana sayar da man Rasha kamar ɗanyen man Urals kan sama da dala 60 kowace ganga, a wasu wuraren kan sama da dala 75 kowace ganga."

Ana kuma tunanin Iran tana fitar da kusan gangar mai miliyan 1.7 inda kusan ganga miliyan 1.2 ko miliyan 1.3 ke tafiya ga China (duk da cewa ita ma tana sirranta bayanan fitar da man da take yi).

A cewar wasu rahotanni, tana fitar da ganga dubu 400 zuwa Indiya.

Tun 2012, gwamnatin Amurka ta haramta shigar da man Iran ƙasarta, sannan ta haramta kamfanonin ƙasashen waje da ke amfani da man Iran yin hulɗa da Amurka.

Tana son daƙile samun Iran wajen ƙera makaman nukiliya da makamai masu linzami ko kuma tallafa wa Hamas da Hezbollah da mayaƙan Houthi.

Donald Trump ya tsaurara takunkuman a 2019 da 2020 a wa'adin shugabancinsa na farko a matsayin shugaban Amurka.

Sai dai Iran har yanzu tana kokarin fitar da mai zuwa China, a wani ɓangaren saboda galibin sa kananun matatu ke siya.

Waɗanne takunkumai aka ƙaƙaba wa man Rasha da Iran a baya-bayan nan?

Rasha da Iran sun yi ƙoƙarin kauce wa takunkuman ta hanyar jigilar jiragen dakon ɗanyen mai a wasu jiragen ɓoye.

A Janairun 2025, a ƙarshen mulkin Biden, Amurka ta ƙaƙaba takunkumi kan wasu tankoki 183 da ke jigilar man Rasha da Iran, da wasu kamfanonin man Rasha biyu - Gazprom Neft da Surgutneftegas.

Amurka ta kuma ƙaƙaba takunkumai kan tankokin da ke ɗauke da man Iran a Oktoban 2024, a matsayin martani ga harin makami mai linzami da aka kai kan Isra'ila sannan kuma aka ci tarar tankokin da ke dakon man Rasha da Iran a Disambar wannan shekarar.

Homayoun Falakshahi of Kpler, wani kamfanin tattara bayanai, ya ce Amurka ta ci tarar kashi 23 cikin 100 na jiragen da suka yi dakon man Iran da kashi 90 cikin 100 na waɗanda suka yi dakon man Rasha.

"Muna ganin raguwar kusan kashi 20 zuwa 25 a yawan man Rasha da Iran da ake shigar wa China," in ji shi, "sannan akwai tankoki da ke ɗauke da ganga miliyan 20 na mai suna maƙale a teku domin kai wa China.

"Hakan ta faru ne saboda tashar jirgin ruwa ta Shandong, babbar tasha ga man Iran, ba ta karɓar duk wata tankar mai da ke jerin waɗanda aka ƙaƙaba wa takunkumi.

Matatun man Indiya sun ce za su daina karɓar man Rasha da Amurka ta ƙaƙaba wa takunkumi.

Ƙaƙaba takunkumi na ɗaya daga cikin matakan da ke janyo tashin farashin mai cikin 'yan watannin baya-bayan nan, in ji Falakshahi.

Labarin ƙaƙaba wa Rasha takunkumo a Janairu ya janyo man kamfanin brent ya tashi zuwa sama da dala 80 kan kowace ganga - tashi mafi girma cikin watanni biyar - kafin ya koma ƙasa da dala 80 kowace gangar mai ɗaya.

Akwai yiwuwar ƙaƙaba ƙarin takunkumai a gaba?

Dr Burcu Ozcelik, daga kamfanin Royal United ta ce akwai yiwuwar shi ma Trump ya saka takunkumai a ɓangaren man Iran, kasancewar ya yi wa ɓangaren matsin lamba a zagayen mulkinsa na farko.

Fitar da mai ba bisa ƙa'ida ba yana amfanar dakarun juyin juya hali na Iran sannan yana ba su damar tallafa wa ƙungiyoyin yan tawaye", in ji ta.

Gwamnatin Biden ta ƙaƙaba wa Bankin Kasuwanci da hannun jari na Yemen Kuwait takunkumi saboda zargin samar wa Hezbollah da wasu ƙungiyoyi kuɗaɗe.

Ozcelik ya ce Fadar White House na iya duba yiwuwar ƙaƙaba takunkumi kan bankuna a Iraki da ke aiki mai kamanceceniya ga Iran.

A 2019 da 2020, Trump ya ƙaƙaba takunkumai kan Iran abin da ya janyo raguwar man da take fitarwa zuwa ganga dubu 500 duk rana.

Ana sa rai Trump zai ƙara yawan takunkumai kan Rasha don ƙoƙarin rage yawan kuɗin da take samu daga ɓangaren mai.

"Za mu iya tsammanin matakan da za su ba da mamaki," in ji Tom Keatinge, shi ma daga kamfanin Rusi.

"Muna sa ran Trump zai faɗa wa ƙasashe: Idan kuka ci gaba da sayen man Rasha, to za mu sa haraji kan kasuwancinku. Zai kuma iya ƙarfafar su, su sayi mansu daga wasu ƙasashen - har da Amurka."

Raguwar fitar da mai daga Rasha da Iran na iya janyo raguwarsa a kasuwar duniya tare kuma da sake daga farashinsa a 2025.