Matar da ke sarrafa garken ɗaruruwan raƙuma a Nijar

    • Marubuci, Ousmane Badiane
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Digital Journalist BBC Afrique
    • Aiko rahoto daga, Dakar
  • Lokacin karatu: Minti 5

A Jamhuriyar Nijar, kusan kashi 87 na ƴan ƙasar na kiwon dabbobi ko dai a matsayin asalin sana'arsu ko kuma sana'ar gefe.

Kiwo na cikin abubuwan da suke taimakon tattalin arzikin Nijar, duk da cewa ba a cika bayyana gudunmuwar da suke bayarwa a ɓangaren ba, duk da ƙoƙarin da suke yi.

Wouro Habsatou Aboubacar, ta ƙware wajen kiwon raƙuma da sarrafa nononsu, inda take samar da madarar da ake nema sosai.

A garkenta mai sama da raƙuma 200, ta kutsa ne cikin harkar da ake ganin ta maza ce, inda Wouro take nuna bajinta tare da shigewa gaba wajen nuna yadda mata suke bayar da gudunmuwa a fannin kiwo domin inganta tattalin arziki da ci gaban Nijar.

Kamfaninta na "Habsatou Lait de Chamelle" wanda ta ƙirƙira a 2011, tana samar da litar madara 160 zuwa 180 a kullum.

Yadda ta gaji kiwon raƙuma

Wouro wadda ta fara tatsar nono ne a shekarar 2011 da dabbobin gidansu kusan 30, ba ta taɓa tunanin za ta mallaki garken raƙuma 200 ba.

Wouro matar aure ce mai ƴaƴa huɗu, wadda take zaune a yankin Niamey. Ta taso ne cikin gidan kiwo, kuma tun tana ƙarama ta fara koyon kiwo.

Tun tana ƙaramar ce take da wani buri: Ta assasa wurin kiwo na zamani babba.

"Tun ina ƙarama nake sha'awar raƙuma, tun a lokacin nake tunanin yadda zan zamanantar da kiwon domin riƙe kaina da ɗaukar wasu aiki," in ji ta a tattaunawarta da BBC Africa.

Ta fara tatsar nono ne tana zuwa talla gida-gida tun a lokacin da take ƙarama.

Wahalar farawa

Da raƙumi ɗaya Wouro ta fara kiwo, kuma a haka ta fara tsara yadda za ta cika burinta na tara garke babba.

"A shekarar 2011 na fara. Da farko na yi tunanin in tatsa nonon ne, in haɗa madara in sayar a Niamey, sai na yi mamakin yadda ake neman nonon raƙumi a sauran sassan ƙasar saboda yadda yake magani. Haka ya sa na ɗauki wasu aiki domin isar da shi zuwa yankunan da ake buƙata."

Yanzu tana samun kuɗin shiga ne daga sayar da nono da kayan maƙulashe da ake haɗawa da madara, kamar yogurt da wani abu da ake kira "wagashi"

Sai dai duk da haka ta sha wahala a lokacin da ta fara.

Burin haɓaka sarrafa nono a cikin ƙasa

A yankuna da dama da ake kiwo, mata ne suke tatsar nono, da sarrafa shi ya zama madara da yoghurt da sauran kayan maƙulashe.

"Madara na cikin abubuwan da kusan kowa ke amfani da shi, shi ya sa ake nemansa sosai domin amfanisa ga lafiya da gina jiki."

Idan ta tuna baya, ta tuna wahalar da ta sha, ganin irin nasarar da ta samu, sai take godiya ga Allah wahalar ba ta tafi a banza ba.

"Abin da ya ƙarfafa min gwiwa shi ne na kawo sabon tsari; shi ya sa ake matuƙar buƙatar madarar domin duk lokacin da na fita, za ka ji mutane na cewa in kawo musu madara, wanda shi ya sa na ce ai kamata in mayar da shi kasuwanci," in ji Wouro.

Ƙalubalen da take fuskanta a ɓangaren

Duk da amfanin da kiwonn ke tattare da shi, mata masu kiwo a Nijar suna fama da matsaloli: ƙarancin fili da ƙarancin dabbobin da rashin kuɗi da rashin kayan aiki da ma rashin tsaro da sauransu.

"Ƙalubalen suna da yawa saboda sarrafa nonon raƙuma ba abu ba ne da aka saba, kuma babu tsari mai kyau. Kayayyakinmu ba sa cikin jerin waɗanda gwamnati ke bayyanawa a cikin tsare-tsarenta wanda kuma yana cikin abun da muke buƙata domin zai haɓaka harkar. Na san ka san yankinmu na fama da rashin tsaro, wanda hakan ya sa muke asarar dabbobinmu, kuma yake rage yawan nonon da nake fitarwa."

"A matsayin mace, babban ƙalubalen da nake fuskanta shi ne zuwa gonaki. Ba na iya zuwa kamar yadda nake so, kuma ga shi ina son bibiyar al'amuran. Gonakina biyu ne: da mai nisan kilomita 35 da mai nisan kilomita 60 daga Niamey."

Abar koyi a cikin al'umarta

Bayan aikin nata, Wouro Habsatou ta zama abar koyi ga matan yankinsu.

Tana shirya tarukan wayar da kan mata horar da su hanyoyin tatsar nono cikin tsafta, da kuma yadda za su mayar da harkar ta zama sana'a domin su riƙe kansu.

"Ba wai alfahari ba, amma ina tunanin za a iya cewa na zama abar koyi. Ina ƙarfafa wa mata gwiwar cewa babu wata sana'ar da za a ce dole ta maza ce. Ina koya musu yadda za su yi sana'a domin su zama masu riƙe kansu."

Duk da cewa kasafai ake samun mata a kiwon raƙuma ba, Wouro Habsatou ta samu nasarar assasa ɗaya daga cikin manyan garken raƙuma a Nijar.

Burinta na gaba shi ne assasa wani kamfani babba da zai tsallaka zuwa ƙasashen waje, wanda zai taimaka wajen samar da aikin yi da rage talauci a Nijar.

"Burina kamfanina ya shiga cikin manyan kamfanonin sarrafa nono a Afirka. Sannan ina so in ga mata sun zama masu ƙarfin tattalin arziki, domin rage rashin aikin yi da rage talauci."