Nijar ta yi zargin ana shiryo mata maƙarƙashiya daga Najeriya

Zaman doya da manja tsakanin Nijar da Najeriya ya sake rincaɓewa, bayan da ministan harkokin wajen Nijar ya gayyaci jami'a mai kula da harkokin diflomasiyya a ofishin jakadancin Najeriya da ke ƙasar, don ta je ta yi bayani kan zargin da suke yi wa Najeriyar na hada kai da wasu kasashen Turai wajen shirya mata manaƙisa.
Ministan ya yi zargi cewa, duk da irin na-mijin ƙoƙarin da Nijar ke ta yi na ganin ta kyautata dangantaka da daɗaɗɗiyar aminiya ko ma abokiyar tagwaitakar ta ta, watau Najeriya, amma ƙasar bata hakura ba, inda take ci gaba da haɗa kai da wasu manyan ƙasashen duniya da jami'an tsohuwar gwamnatin Bazoum da ke zaman mafaka a Najeryar ake ci gaba da kitsa yadda za a jefa ƙasar cikin hargitsi.
Wannan zargi na zuwa ne duk da wani taro da aka yi watannin baya tsakanin hafsoshin sojan Nijar da na Najeriya, inda Najeriya ta bayar da tabbacin ba za yarda a ci dunduniyar ƴar uwar ta ta ba.
Yayin wata hira da sashen Hausa na BBC a watannin baya, Firaministan Nijar din Lamine Zain, ya yi zargin cewa mahukuntan Najeriya da jami'an tsohuwar gwamnatin na tsara yadda za a cutar da kasar daga Abuja, zargin da Najeriyar ta musanta.
Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ta ɓalɓalce ne tun bayan da sojoji suka karɓe ragamar mulki a Nijar. Suka kuma fitar da ƙasar tasu daga ƙungiyar raya tattalin Afirka ta yamma, wato ECOWAS.
Ko da yake a baya-bayan nan ƙungiyar ta ECOWAS, ta ce jamhuriyyar ta Nijar da sauran ƙasashen da suka fice daga cikin ƙungiyar tare da ita, za su iya sauya shawara cikin watanni shida.
'Ya kamata a yi hattara'

Asalin hoton, SULAIMAN DAHIRU
Masana harkokin diflomasiyya dai na ganin wannan ƙorafi abu ne da ɓangarorin biyu ya kamata su yi hattara a kai, kuma su zauna su tattauna game da shi.
Ambasada Sulaiman Dahiru, tsohon jakadan Najeriya da ya shafe shekaru 35 a matsayin jami'in diflomasiyya, ya ce ya kamata sojojin da ke rike da mulki a Nijar, su kai zuciya nesa, domin yana da tabbacin Najeriya ba za ta yi abun da suke zargi ba.
''Na tabbata Najeriya ba za ta taɓa so a cutar da Nijar ba, babu wani mutum daga arewacin Najeriya da zai yadda a cuce su, idan da an yi abubuwan da suke ganin bai dace ba, yanzu an zo an janye, don haka dukka wadannan bangarori su yi takatsantsan, Najeriya da Nijar yan uwan juna ne'' inji shi.
Sai dai ya ce babban abun da ke tayar wa Nijar hankali shine ganin yadda a baya bayan nan Najeriyar ke jan Faransa a jiki, don haka ya kamata shima shugaba Tinubu ya yi hattara da wannan.
Ya ce ''Ban ga dalilin da zai sa Tinubu ya yi ta jan Najeriya kusa da Faransa ba, ni a ganina a aikin da na yi babu wani dalili da zai sai Najeriya ta rika jan Faransa a jiki, me suka mana ? lokacin da muke bukatar taimako ai ba su taimake mu ba''











