Faransa ta ƙalubalanci Trump kan barazanar ƙwace tsibirin Greenland

Trump ya ce tsibirin ya taka muhimmiyar rawa wajen bin sahun jiragen yakin China da na Rasha waɗanda ya ce "sun warwatsu a yankin".

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Faransa ta ce Tarayyar Turai ba za ta bari ƙasashe su kai wa "ƙasashe masu ƴanci" da ke maƙwabtaka da ita hari ba, bayan da zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya ce bai cire ran yin amfani da ƙarfin soji wajen ƙwace iko da yankin Greenland.

A ranar Talata ne dai Trump ya nanata sha'awarsa ta mamayar yankin na Denmark inda ya ce "na da muhimmanci" ga tsaro da tattalin arziƙin ƙasa.

Ministan harkokin ƙasar waje na Faransa, Jean-Noel Barrot ya shaida wa gidan rediyon Faransa cewa "babu tamtama cewa tarayyar turai ba za ta bar wasu ƙasashe ba su kai hari kan ƙasashe masu ƴanci da ke iyaka da ita, koma su wane ne."

Barrot ya ce bai yi amanna da cewa Amurka za ta kutsa tsibirin da ke yankin Arctic ba to amma ya fayyace cewa bai kamata Tarayyar Turai ta bari a firgita ta ba.

Trump ya sha bayyana sha'awarsa wajen sayen Greenland, kasancewar ya ɓunta maganar a zangon mulkinsa na farko a matsayinsa na shugaban Amurka.

Denmark, wadda daɗaɗɗiyar ƙawar Amurka ce ta fayyace cewa Greenland ba ta siyarwa ba ce kuma mallakar mazauna wurin ne.

Firaiministan Greenland, Mute Egede na ta ƙoƙarin neman wa yankin ƴancin cin gashin kai inda ya sha bayyana cewa yankin ba na siyarwa ba ne. Zai kai ziyara Copenhagen ranar Laraba.

Trump dai ya yi waɗannan kalaman ne a yayin wani taron manema labarai a rukunin gidajensa da ke Mar-a-Lago a Florida, ƙasa da makonni biyu kafin rantsar da shi a matsayinsa na shugaban Amurka karo na biyu.

An tambaye shi ko akwai yiwuwar amfani da ƙarfin soji ko kuma matakan tattalin arziƙi wajen mamaye Greenland ko mashigar ruwa ta Panama Canal, sai Trump ya ce "A A, ba zan ba ku tabbacin kowa ɗaya daga cikin abubuwan nan guda biyu ba.

"Sai dai zan iya cewa, muna buƙatar tsaro a fannin tattalin arziƙi."

Amurka dai na da na'ura a Greenland tun lokacin yakin cacar baka kuma tun lokacin yankin ya zama mai muhimmanci ga Amurkar.

Trump ya ce tsibirin ya taka muhimmiyar rawa wajen bin sahun jiragen yakin China da na Rasha waɗanda ya ce "sun warwatsu a yankin".

Ya shaida wa manema labarai cewa "Ina magana ne a kan kare duniyar walwala,"

Trump ya ce tsibirin Greenland ya taka rawa wajen daƙile shawagin jiragen yaƙin China da Rasha a lokacin yaƙin cacar-baka.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Donald Trump Junior wanda ɗa ne ga zaɓaɓɓen shugaban na Amurka ya kai wata ziyarar ƙashin kai yankin na Greenland
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tsibirin na Greenland dai shi ne tsibirin da ya fi kowanne girma a duniya kuma yankin na da yawan jama'ar da suka kai 57,000, kuma yana da ɗan ƙwarƙwaryar ƴanci duk da cewa tattalin arziƙinsa ya dogara ne kan tallafin da Denmark ke ba su sannan yankin wani ɓangare ne na ƙasar ta Denmark.

Greenland na da albarkatun ƙarƙashin ƙasa fiye da kowane yanki a duniya, waɗanda ke da muhimmanci wajen yin batiri da na'urori.

Danjaridar kafar watsa labarai ta ƙasar Denmark, da ke rahoto daga Greenland, Nuuk Kretz ya ce mutanen da ya tattauna da su a Grenland dangane da kalaman Trump sun bayyana kaɗuwa da ƙoƙarin mamaye yankin nasu.

Yayin da mafi yawan al'ummar yankin ke fatan samun ƴancin kai a gaba, ya ce tsibirin na buƙatar ƙasar da za ta sanya ta a gaba wajen samun fa'aidar tattalin arziƙi da tsaro, kamar dai yadda Denmark ke yi mata a yanzu.

Kretz ya shaida wa BBC cewa a daidai lokacin da gwamnatin Denmark ke ƙaƙarin danne yiwuwar fito-na-fito da Trump, "a bayan fage, na fuskanci cewa wannan rikicin ka iya zama babban rikici na duniya ga Denmark a tarihinta".

Ɗan gidan Donald Trump, Donald Trump Junior ya kai wata ƴar ƙwarƙwaryar ziyar ga Greenland ranar Talata, abin da ya bayyana da "ziyarar kashin kai" domin tattaunawa da jama'a.

Ya kuma wallafa hotunansa tare da wasu mutanen tsibirin na Greenaland sanye da hular da ke nuna goyon bayan Trump, a wata mashaya.