Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Girman alaƙar Arsenal da baƙaƙen fata ta tsawon shekaru
- Marubuci, Ameer Ahmed da Khadidiatou Cisse
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa
- Lokacin karatu: Minti 5
Lokacin da Dr Clive Chijioke Nwonka ya je Manchester domin ziyartar abokansa a ranar 28 ga Satumban 2002, ashe zai ga muhimmin al'amari.
Zai kalli wasan ƙwallon ƙafa mai cike da tarihi.
A ranar ce Arsenal ta kasance ƙungiyar ƙwallon ƙafa da ta yi amfani da ƴanwasa tara baƙaƙen fata daga cikin 11 a wasan Premier League.
Uku daga cikinsu - Thierry Henry, Nwankwo Kanu da Kolo Toure - kuma suna cikin waɗanda suka jefa ƙwallo a raga a wasan da Gunners ta doke Leeds United 4-1.
"Ƙwazonsu ya nuna tasirin wannan lokacin mai tarihi da kuma muhimmancin launin fata," kamar yadda Dr Nwonka, wanda yanzu farfesa ne a University College London, ya shaida wa BBC.
"Ya nuna muhimmancin kasancewarsu kan wannan nasarar."
Dr Nwonka ya nuna rawar da ƙungiyar ta taka ga tarihin al'adun baƙaƙen fata, a matsayin ɗaya daga cikin editan littafin da aka wallafa mai taken "Black Arsenal," wanda ya ƙunshi bayanai da hotunan wasu da suke ganin suna da alaƙa da ƙungiyar da ke birnin Landan.
"Ni ɗan Birtaniya ne mai asali daga Najeriya, kuma ina ganin ƴanwasa baƙaƙen fata da ƴanwasan Afrika a ƙwallon Birtaniya yana da muhimmanci a gare ni," in ji shi.
Wani ɓangare na littafin ya yi sharhin gudunmuwar Arsenal ga kwararar ƴanwasa baƙaƙen fata a gasar Premier da kuma samun magoya baya mata a filin ƙungiyar na Emirates.
"Ina jin kullum akwai wani abu muhimmi, kan yadda baƙaƙen fata ke da alaƙa da Arsenal, in ji Dr Nwonka.
Goyon bayan da ƙungiyar ke samu zai shafi harakokin yau da kullum na dimbin magoya bayan ƙungiyar, kuma an taɓo wannan a cikin littafin.
"Idan na ce Arsenal, ina nufin irin al'adar muhimmancin Arsenal ga baƙaƙen fata," a cewar Dr Nwonka.
Wenger da Afirka
Ian Wright, shi ne ya kasance mai farin jini ga dimbin magoya bayan Arsenal baƙaƙen fata a shekarun 1990, saboda yunwarsa ta cin ƙwallaye.
Sai dai ba dukkanin magoya bayan Arsenal za su amince da hotonsa a bangon littafin Black Arsenal ba, amma Dr Nwonka da sauran ƴan Najeriya, suna ganin akwai wani muhimmin ɗanwasa.
Sun tuna tawagar Najeriya da ta lashe zinari a wasannin Olympics bayan doke Argentina a 1996, kuma ɗanwasan da ya ci ƙwallon da ta bayar da nasara a wasan kusa da ƙarshe da Brazil - shi ne Kanu.
An haife shi a jihar Imo, ɗanwasan na gaba ya koma Arsenal ne daga Inter Milan ta Italiya a 1999.
"Zuwansa Arsenal yana da muhimmanci a gare ni da kuma wasu kamar ni," in ji Dr Nwonka.
Arsene Wenger, tsohon kocin Arsenal, wanda ya yi fice wajen sayen ƴanwasan Faransa da baƙaƙen fata, tare da renon yanwasa da dama a shekara 22 da ya shafe yana horar da Arsenal tsakanin 1996 zuwa 2018.
Kocin ya samu karɓuwa da girmamawa kan tsarinsa na tafiyar aikinsa musamman lokacin da Arsenal ta lashe kofi a kakar 2003-04.
Irin wannan nasarar ce wani ɓangare na magoya baya suka koma goyon bayan Chelsea abokiyar gabar Arsenal a London, wadda ta yi fice zamanin Jose Mourinho lokacin da ya ɗauko ƴanwasa baƙaƙen fata kamar su Didier Drogba na Ivory Coast da ɗanwasan Ghana Michael Essien da kuma ɗanwasan tsakiya na Najeriya John Obi Mikel.
Yaƙi da wariyar launin fata
Sai dai duk da nasarorin ƴanwasa baƙaƙen fata, har yanzu wariyar launin fata babbar matsala ce a filin wasa.
A 2021, bayan rashin nasara a wasan ƙarshe a gasar cin kofin Turai ta Euro 2020 hannun Italiya, ƴanwasa uku na Ingila - Bukayo Saka, Jadon Sancho da Marcus Rashford - sun fuskanci wariyar launin fata saboda sun ɓarar da fanariti.
An kama mutum 11, kuma Arsenal ta fitar da sanarwa tana nuna goyon baya ga ɗanwasanta Saka da sauran abokan wasansa na Ingila.
Sai dai an daɗe Saka yana fuskantar wariya, ciki har da lokacin da Arsenal ta sha kashi a hannun Nottingham Forest a bara.
Matsalar wariya ta kasance ruwan dare a dukkanin ɓangarori na ƙwallon ƙafa da aka fi bayar da rahoto a Ingila, kamar yadda alƙalumman ƙungiyar yaki da wariyar launin fata ta Kick It Out suna nuna.
Makomar Arsenal
A kakar bana, ta yi bikin alaƙarta da Afirka ta hanyar samar da rigar ƴanwasa da ke da launi irin na tutar ƙasashen nahiyar.
Ɗan asalin Saliyo, Foday Dumbuya ne ya tsara rigar kuma a birnin Freetown aka dauƙi bidiyon tallar sabbin tufafin ƴanwasan.
A matsayinsa na wanda ya girma a Landan, Dr Nwonka ya bayyana tufafin na Arsenal a matsayin tufafin birnin.
Saka, iyayensa ƴan Najeriya ne da suka haife shi a Landan, kuma yanzu shi yake da farin jinin magoya bayan Arsenal.
Ɗanwasan mai shekara 23 ya yi wa Arsenal wasa 230 kuma ya daɗe yana adawa da nuna wariyar launin fata.
Yanzu shi ne kan gaba a bunƙasar alaƙar Arsenal da baƙaƙen fata.