Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haaland ya ci ƙwallo na 100 a Man City
Erling Haaland ya zura ƙwallo na 100 a raga a Manchester City ranar Lahadi a wasan da suka yi 2-2 da Arsenal a Premier League.
Shi ne ya fara cin Arsenal a karawar ta hamayya a Etihad, kuma na 10 a kakar nan, sh ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a bana da fara babbar gasar tamaula ta Ingila.
Ɗan wasan tawagar Norway ya ci na 100 a City a karawa ta 105 a kaka biyu tun bayan da ya koma Etihad daga Borussia Dortmund.
Haaland na taka rawar gani a bana a Premier League da 10 a raga da fara kakar nan, ƙwazo mai girma tun bayan bajintar ɗan wasan Aston Villa, Pongo Waring a 1930.
Haaland ya ci ƙwallo 235 a tarihi tun daga Molde da Red Bull Salzburg da Borussia Dortmund da kuma City - ya kuma ci wa Norway 32 yana da shekara 24.
Ya kuma yi kan-kan-kan da Cristiano Ronaldo a tarihin da ya kafa a Real Madrid, wanda ya zura 100 a mafi karancin wasanni daga manyan gasar Turai biyar.
Ƙwallo 10 da Haaland ya ci a wasa bakwai da fara kakar bana:
Ya fara da Chelsea a karawar da City ta ci 2-0 a Stamford Bridge ranar 18 ga watan Agusta, wato wasan farko da fara kakar nan ta Premier League.
Ya zura uku rigis a ragar Ipswich a wasan da City ta ci 4-1 ranar Asabar 24 ga watan Agusta, sai ya kara cin uku rigis a ragar West Ham da City ta yi nasara 3-1 a Premier League ranar Asabar 31 ga watan Agusta.
Haka kuma shi ne ya ci Brentford biyu a wasan da City ta yi nasara 2-1 a Premier League ranar 14 ga watan Satumba.
Sai dai bai zura ƙwallo ba a ragar Inter Milan a wasan da City ta tashi 0-0 a Champions League a Etihad ranar 18 ga watan Satumba.
Sai kuma wadda ya fara cin Arsenal a Etihad da City ta tashi 2-2 a Premier League ranar Lahadi 22 ga watan Satumba.