Yadda sakin ruwa daga madatsar Lagdo ta Kamaru zai ta'azzara ambaliya a Najeriya

Ambaliya a Maiduguri

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ambaliyar da birnin Maiduguri na jihar Borno ya fuskanta a baya-bayan nan ta shafi sama da mutum miliyan biyu
    • Marubuci, Aminu Adau
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 3

Duk shekara idan za a sako ruwa daga madatsar ruwa ta Lagdo da ke Kamaru, miliyoyin mazauna jihohin Najeriya aƙalla 10 kan shiga cikin zullumi.

An samu asarar ɗaruruwan rayuka a 'yan shekarun da suka wuce sakamakon sakin ruwan madatsar, yayin da dubbai suka rasa muhallansu tare da jawo lahani kan harkokin kasuwanci har sai ruwan ya kwaranye.

A ranar Talata, hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya Nigerian Hydrological Services Agency (NIHSA) ta fitar da gargaɗi cewa Kamaru za ta sako ruwan na Lagdo kuma jihohi 11 da ke kusa da Kogin Binuwai ne ke cikin haɗarin ambaliya.

Idan hakan ta faru, lamarin zai iya ta'azzara ambaliyar da ake ciki a faɗin ƙasar, inda tuni gomman mutane suka mutu dubbai suka rabu da muhallinsu.

Jihohin da ambaliyar za ta iya shafa su ne- Adamawa, Anambra, Bayelsa, Benue, Cross River, Delta, Edo, Kogi, Nasarawa, Rivers, da kuma Taraba.

Jihohin sun yi fama da matsalar ambaliya a shekara goma da ta gabata a duk lokacin da aka sako ruwa daga madatsar ta Lagdo da ke Kamaru.

Kuma duk shekara, mutanen da ambaliyar ke tagayyarawa na ƙaruwa abin da masana suka ce ana iya magancewa.

“Za a iya taƙaita yawan ruwan da za a saki ta yadda ba zai fi ƙarfin Kogin Binuwai ba, wanda hakan zai iya hana ambaliya a sassan Najeriya,” in ji Umar Mohammed, shugaban hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya ( NIHSA) a wata sanarwa.

Me ya sa madatsar ruwan Lagdo ta Kamaru ke damun Najeriya?

Madatsar ruwan ta Lagdo wadda aka kammala a 1982, an yi ta ne domin samar da wutar lantarki ga arewacin kamaru da kuma samar da hanyar noman rani a filin hekta 15,000. To amma kamar sauran wasu madatsun ruwan , ita ma takan cika ta batse a wani lokaci na shekara ta yadda har sai an bude ruwan domin gudun kada ta fashe.

An ce ita ma Najeriya ya kamata a ce ta gina madatsar ruwa a bangarenta - Madatsar ruwan Dasin - wadda ya kamata a yi a jihar Adamawa- wannan madatsara ce ya kamata a ce ta ta karbi ruwan da za a saki daga madatsar Lagdo a duk lokacin da aka saki ruwan a can domin rage illar da sakin ruwan zai iya yi a Najeriya.

To amma ita wannan madatsar ruwa da ya kamata a yi a Najeriya, ba a kammala ta ba, wannan ne kuma ya sa ruwan da ake saki daga madatsar Lagdoke yin illa ga al'ummomi da dama a Najeriya, musamman ma wadanda suke kusa da gabar kogin Binuwai, inda yawancin ruwan ke bi.

Yaya tasirin hakan yake?

A bara lokacin da gwamnatin Najeriya ta ce ambaliya ta kashe mutum 28 tare da raba 48,168 da muhallinsu a kasar, an danganta matsalar ga sakin ruwan na madatsar Lagdo.

A 2022 lokacin da hukumomi suka ce mutum 612 sun mutu, wasu sama da miliyan 3.2 sun gamu da illar ambaliya da ta shafi jihohi da dama, a nan ma sakin ruwan madatsar Lagdo aka danganta da haddasa hakan.

A wannan shekara an bayar da rahoton cewa gidaje 181,600 suka lalace, yayin da wasu gidajen 123,807 suka lalace gaba daya sannan gonaki hekta 176,852 suka gamu da illa wasu kuma hekta 392,399 ruwan ya lalata gaba daya in ji hukumomi.

Illar ambaliyar ta shekara-shekara a Najeriya, wadda aka fara tattara bayananta a 2012 lokacin da ta kashe mutum sama da 10 tana karuwa a kowace shekara tun daga sannan.

Ko za a ga bambanci a bana?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Naija, Ibrahim Audu Usaini, daya daga cikin jihohin da ambaliya ta fi yi wa barna, ya gaya wa BBC cewa ana ta fadakar da al'ummomin garuruwan da ke kusa da inda ambaliayr ke bi sannan kuma ana kwashe mutane daga kwari inda ake mayar da su wuraren da suke kan tudu..

“Sannan kuma muna samar da abinci da sauran kayan tallafi ga jama'ar, kasancewar ba sa son barin wadannan garuruwa nasu gaba daya,” in ji shi.

Ya yi bayanin cewa yayin da tuni kasar take fuskantar matsalar ambaliya sakamakon mamakon ruwan sama, haka kuma tana kara shirin tunkarar wata ambaliyar ta sanadin sakin ruwan madatsar ruwan ta Lagdo da sauran madatsun ruwa.

Yayin da hukumomin Najeriya ke cewa za a takaita kwararar ruwan madatsar ruwan ta Lagdo ta yadda ba za a bari ruwan ya yi illa ba sosai, abin jira a gani shi ne yadda hukumomin na Najeriya za su iya yin hakan, da kuma yawan illar da ambaliyar ke haifarwa nawa za a iya ragewa.