Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Samia Suluhu ta lashe zaɓen shugaban ƙasar Tanzaniya
Hukumar zaɓen ƙasar Tanzaniya ta bayyana shugabar ƙasa mai ci Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaɓen shugaban ƙasar.
Tun bayan kammala kaɗa ƙuri’a a ranar Laraba ne rikici da zanga-zanga suka ɓarke a ƙasar, inda ƴan jami’iyyar adawa ke nuna rashin jin daɗi kan yadda aka gudanar da zaɓen.
"Na ayyana Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaben shugaban kasa a karkashin jam'iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM)," in ji Jacobs Mwambegele, shugaban hukumar zaben Tanzaniya a lokacin da yake sanar da sakamakon a safiyar ranar Asabar.
Samia ta samu kimanin kuri'a miliyan 31.9, wato kashi 97.66% na jimillar kuri’un da aka kada.
Kimanin kashi 87% ne na jimillar wadanda suka yi rajistar zabe miliyan 37.6 suka fita domin kada kuri'a, in ji hukumar zaben.
A yankin Zanzibar mai kwarya-kwaryar iko - inda al'ummar yankin kan zabi nasu shugaban - shugaba mai ci Hussein Mwinyi na jam'iyyar CCM ne ya lashe zaben.
Ya lashe kusan kashi 80% na jimillar kuri'un da aka kada.
Jam'iyyar adawa ta kasar ta ce daruruwan mutane ne suka mutu sanadiyyar zanga-zangar da aka kwashe kwanaki ana yi tun bayan zaben na ranar Laraba.
Alkaluman da ke fitowa game da yawan mutanen da suka rasa rayukan nasu sun sha bamban, kuma toshe hanyar sadarwar intanet ta sanya kokarin tantance gaskiyar alkaluman na da matukar wahala.
Yayin da mai magana da yawun jam'iyyar adawa ta Chadema ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "kimanin mutum 700" aka kashe a zanga-zangar ta bayan zabe, wata majiyar diflomasiyya a cikin Tanzaniya ta shaida wa BBC cewa akwai kwararan hujjoji da ke tabbatar da cewa an kashe akalla mutum 50.
Gwamnati ta yi kokarin nuna cewa zanga-zangar ba ta kazance ba - sannan hukumomi sun tsawaita dokar hana fita a yunkurin shawo kan matsalar.
Akasarin masu zanga-zangar matasa ne wadanda suka hau kan titunan biranen kasar domin yin Allah wadai da zaben.
Sun zargi gwamnati da yi wa dimokuradiyya zagon kasa ta hanyar danne manyan 'yan adawa - daya daga cikinsu na kulle a gidan yari yayin da dayan aka hana shi takara - wanda hakan ya kara share wa Samia Suluhu da jam'iyyarta ta Chama Cha Mapinduzi (CCM) hanyar lashe zaben.