Wadanne irin makamai kasashen duniya suka bai wa Ukraine?

Sojojin Ukraine

Asalin hoton, Getty Images

Ukraine ta sake yin kira ga kasashen duniya da su samar mata da karin kayan yaki domin tunkarar mamayar Rasha.

Shugaba Volodomyr Zelensky ya shaida wa taron Nato na makon da ya gabata cewa: "Muna bukatar mu karya lagwon makaman Rasha. Muna bukatar karin makamai na zamani."

Ya ce idan har Ukraine ba ta samu makaman da take bukata ba don kayar da Rasha, to shugabannin NATO za su fuskanci yaki a nan gaba da Moscow da kansu.

Kasashe sama da 30 ne suka bai wa kasar Ukraine dinbin kayayakin yaki, sai dai ana tafiyar hawainiya game da manyan makamai, kuma a wasu yankunan sojojin Ukraine ba su da makamai.

Wadanne kasashe ne suka fi ba Ukraine makamai?

Birtaniya ita ce ta biyu yayin da Poland ita ce ta uku a jerin kasashen da ke kashewa Ukraine makudan kudade.

Dangane da kudaden da aka kashe, maimakon alkawuran bayar da kudi da kasashe suka yi, Fadar White House ta ce Amurka ta bayar da tallafin dala biliyan 6.3 a matsayin taimakon tsaro ga Ukraine tun lokacin da Shugaba Joe Biden ya hau karagar mulki a watan Janairun 2021.

Birtaniya ta ce ta samar da dala biliyan 1.6 , kuma ta yi alkawarin bayar da karin dala biliyan 1.2 tun farkon yakin.

Shugaba Zelensky ya nemi karin kudade, kuma ya ce kudaden da kasar ke kashewa kan tsaro a kowanne wata ya kusan dala biliyan 5.

Wadanne irin makamai ne Ukraine ta ke bukata?

Kwararun sojoji sun ce samun nasara a fagen daga na bukatar manyan makamai, da horo da kayayyakin gyara da sauran tallafi.

"Babu tsarin makami da ya zama harsashi na azurfa," a cewar Janar Mark Milley, Shugaban Hafsan Hafsoshin Sojojin Amurka.

Duk da haka, ana kyautata zaton na'urorin makamai da dama sun taka muhimmiyar rawa a rikicin ya zuwa yanzu.

Rokoki masu cin dogon zango

Yayin da sojojin Rasha ke ci gaba da luguden wuta a yankunan Ukraine da ke gabashin kasar, manazarta sun ce Ukraine tana matukar bukatar samar da ingantattun makamai da harsasai don rike manyan yankunanta.

Ya zuwa yanzu, ana tunanin cewa an tura wa kasar makaman roka guda 10 masu cin dogon zango ko kuma suna kan hanya, daga Amurka da Birtaniya da Jamus.

Ukraine ta ce ana bukatar wasu da dama don dakile danawar sojojin Rasha.

Makaman yakin na Amurka sun hada da naurar roka ta M142 ko Himars Kayayyakin da aka ba wa Ukraine a halin yanzu makaman da aka ba Ukraine za su iya cin dogon zango na mil 43.5 wato kilomita 70.

Motar harba rokoki ta Himars

Howitzers

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Australia da Canada da kuma Amurka sun tura da karin makamai da ake kira howitzers sama da 100 da kuma arburusai dubu dari 300 zuwa Ukraine.

Kasashen Yamma sun yi tafiyar hawainiya wajen amsa bukatar Ukraine na neman manyan makamai.

A farkon yakin akwai damuwa game da tsokanar Rasha.

'Yan siyasa kuma sun dauka sojojin Ukraine ba za su kai labari ba.

Bayan dan lokaci wannan tunani ya canza, ko da yake har yanzu akwai tambayoyi game da ƙudirin yamma na ci gaba da bai wa Ukraine makamai.

Da farko an mayar da hankali ne kan samar wa Ukraine makamai masu jituwa - wadanda aka horar da su don amfani da su.

Wannan ya haɗa da tankunan yaƙi na zamanin tarayyar Soviet, na'urorin tare makamai ta sama da harsasai.

Amurka da sauran kawayenta sun taimaka wa Turai don neman makaman makamancin haka, amma wadannan tarin makaman sun ragu matuka.

Don haka a yanzu ana som a turawa kasar da karin makamai na zamani na kasashen yamma tare da fatan za su dore a cikin dogon lokaci.

Amma hakan ya kawo ƙarin ƙalubale.

Tsarin makaman zamani galibi ya fi rikitarwa kuma yana buƙatar horo, ba kawai yadda ake sarrafa su ba, amma don kula da su da gyara su.

Makaman lalata tankokin yaki

An turawa Ukraine da makaman lalata tankokin yaki akalla 5,000 da ake kira Nlaw.

Ukraine ta karbi tankokin yaki sama da 230 daga Poland da Jamhuriyar Czech.

Tankokin yaki

Asalin hoton, Getty Images

Sojojin Ukraine sun shafe shekaru suna amfani da tankokin yaki kirar T-72 kuma suna da kayayyakin gyra da kuma sojoji da suka kware a wannan fani.

Jiragen yaƙi marasa matuƙa

An yi amfani da jiragen sama marasa matuka a yakin Ukraine inda an yi amfani da dama wajan sintirin tsaro da kai hari da kuma jigilar kayayyaki masu nauyi.

Turkiyya ta sayarwa Ukraine da jirgin sama marasa matuka na Bayraktar TB2 a watannin baya-baya nan.

Jirgin sama mara matuki

Masu sharhi sun ce jirgin sama mara matuki na Bayraktar TB2 ya yi tasiri sosai wajan kai wa sojojin Rasha hari.

An yi ammanar cewa an yi amfani da su wajen lalata jiragen sama masu saukar ungulu da jiragem ruwan yaki da makamai masu linzami

Na'urar tare makami ta sama

Ukraine ta yi nasarar hana Rasha cikakken ikon mallakar sararin samaniyarta a lokacin rikicin, amma ta yi kira akai-akai da samar mata naurar tare makami ta sama mai inganci.

A cikin kwanaki masu zuwa, ana sa ran Washington za ta sanar da cewa za ta aika NASAMS, na'urar harba makami mai linzami daga sama

Naurar harba makami daga sama