An yanke wa Aung San Suu Kyi ƙarin ɗauri na shekara bakwai

Asalin hoton, Reuters
Wata kotun soji a Myanmar ta yanke wa tsohuwar jagorar ƙasar Aung San Suu Kyi ƙarin hukuncin ɗauri na shekara bakwai.
Hakan ya sanya tsawon hukuncin ɗaurin da aka yanke mata a baya ya ƙaru zuwa shekara 33.
Dama dai Suu Kyi na fuskantar ɗaurin talala a gidanta tun bayan da sojoji suka tuntsurar da gwamnatinta a watan Fabrairun 2021.
Tun daga wancan lokaci ake mata shari’a kan tuhume-tuhume 19, waɗanda ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama suka ce ba su da tushe.
A makon da ya gabata ne kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya buƙaci da a sake ta.
A ranar Juma’ar nan ne kotu ta yanke hukunci kan sauran tuhume-tuhume biyar da suka rage a kanta.
Kotun ta same ta da laifin rashawa saboda ba ta bi ƙa’ida ba wajen bayar da hayar wani jirgi mai saukar ungulu ga wani minista.
Kafin wannan an same ta da laifuka 14, ciki har da na wancakali da matakan kariya na cutar korona, da shigar da wayoyin jami’an tsaro na oba-oba daga ƙasar waje, da kuma saɓa wa dokokin asirta bayanan gwamnati.
A cikin wannan shekara an rinƙa gudanar da shari’o’inta a ɓoye, inda al’umma da ƴan jarida ba su da damar shiga kotu, sannan an haramta wa lauyoyi magana da kafafen yaɗa labaru.
Suu Kyi dai ta musanta duk tuhume-tuhumen da aka yi mata.
Matar mai shekara 77 ta kwashe tsawon lokaci tana ƙarƙashin ɗaurin talala a babban birnin ƙasar Nay Pyi Taw.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ms Suu Kyi da wasu da dama daga cikin ƴayan jam’iyyarta na daga cikin mutane sama da 16,600 waɗanda sojojin suka kama tun bayan karɓe mulki.
Wata ƙungiya a ƙasar ta ce har yanzu akwai irin waɗannan ƴan siyasa 13,000 da ake tsare da su a gidajen yarin ƙasar.
A makon jiya kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira da a kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasar tare da sakin ƴan siyasa da aka tsare.
China da Rasha sun ƙi kaɗa ƙuri’a a kan batun.
Anmensty International ta ce shari’ar da ake ta yi wa Suu Kyi ya nuna yadda sojojin ƙasar suke amfani da kotu a matsayin makamin faɗa da masu hamayya.
Juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar ya haifar da zanga-zanga da bore, abin da ya sanya sojoji suka yi ta ƙoƙarin murƙushe masu hanƙoron tabbatar da demokuraɗiyya.
Haka nan ya ƙara iza wutar faɗace-faɗace tsakanin ƴan tawaye na ƙabilu, da kuma fararen hula mayaƙa masu adawa da gwamnatin soji.
Ana zargin gwamnatin sojin da kashe mutane ba bisa ƙa’ida ba, da yin ruwan wuta a ƙauyuka.
An yi ƙiyasin cewa ya zuwa yanzu sama da mutum 2,600 ne aka kashe a ƙoƙarin sojoji na murƙushe masu adawa da su.











