Shin tallafin Amurka zai iya magance matsalar tsaro a Najeriya?

A Najeriya, gwamnatin kasar tana duba batun tayin da aka yi mata na taimako daga kasashen waje don yaki da matsalar sace-sacen jama'a da sauran manyan miyagun laifuka.

Ministan watsa labarai na kasar, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a fadar shugaban Najeriyar, inda ya ce Amurka da sauran wasu kasashe da bai bayyana sunayensu ba, su ne suka yi wa Najeriyar tayin taimakon na tsaro.

To, sai dai kuma masana harkar tsaro suna ganin akwai bukatar Najeriyar ta yi taka-tsantsan game da irin wannan taimako.

Galibi dai ana kallon tayin taimakon na tsaro da Amurka da sauran wasu kasashen waje suka yi wa Najeriya, a matsayin wani zancen ji mai karfafa gwiwa da zaburar da kyakkyawan fata.

Domin kuwa ya zo a dai-dai lokacin da ake matukar bukatarsa, kuma ana hangen hakan zai taimaka, wajen yaki da matsalar sace-sacen mutane don neman kudin fansa, da sauran miyagun laifuka da 'yan bindiga ke aikatawa a Najeriyar.

Amma kuma masana harkar tsaro, irin su Dakta Kabiru Adamu, shugaban kamfanin harkar tsaro da tattara bayanan sirri na Beacon, suna ganin akwai bukatar a tantance irin tsarin da za a yi aiki da shi wajen karbar taimakon na tsaron daga waje.

"An yi lokuta da yawa da muke buƙatar makamai don magance wannan matsalolin na tsaro amman wadannan ƙasashe basu bamu ba," cewar Dakta Kabiru.

Masanin tsaron ya kuma yi tsokaci, cewa ba dole ba ne irin wannan taimako na kasar waje ya kai Najeriya ga gaci, "dole ne sai mun zauna mun yi namu tsarin na cikin gida, akwai inda ake makamai."

Wasu na ganin cewa Amurka da sauran kasashen Yamma ba sa kai irin wannan taimako na tsaro, sai inda su ma za su amfana. " Akwai alamar cewa irin wannan taimakon ba ana yi ba ne na fisabilillahi, yawanci da muradin da suke son cimmawa," a cewar masanin.

Masana harkar tsaro da dama sun yi ittifaki a kan akwai bukatar mahukuntan Najeriya su guji bin duk wata hanya da za ta buge ga tsallen-badake, dangane da karbar taimakon tsaro daga waje.