AC Milan ta ɗauki Morata daga Atletico Madrid

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

AC Milan ta kammala ɗaukar ɗan wasan gaban Spain Alvaro Morata daga Atletico Madrid kan kwantaragin shekara huɗu da kuma zaɓin tsawaita ta na watanni 12.

Kungiyar ta nemi jin kuɗin sakin Morata wanda aka ce ya kai fan miliyan 11 kafin daga baya ta biya kudin sayan shi.

Dan wasan mai shekara 31 shi ne ya sanya wa Spain kambu a gasar Euro 2024 da suka lashe a farkon wannan watan.

Morata ya fara kwallonsa ne a Real Madrid daga baya kuma ya buga wa Juventus da Chelsea wasa.

Ya lashe Champions Lig sau biyu a Real Madrid ya kuma ci kofin Italiya sau biyu da Juventus.

Morata ya ci FA da Chelsea, ya kuma ci kwallo 36 cikin wasa 80 ga Spain.